03/10/2025
BAD TA BAI WA NIJAR TALLAFIN BILIYAN 89 NA CFA DOMIN INGANTA WUTAR LANTARKI DA TALLAFIN MASU ZAMAN KANSU
A wani mataki na kara tallafa wa ci gaban tattalin arzikin Jamhuriyar Nijar, Bankin Raya Afirka (BAD) ya amince da bai wa ƙasar tallafin kuɗi na kimanin biliyan 89 na CFA (kwatankwacin dala miliyan 144.7), domin inganta samun wutar lantarki mai inganci a fadin ƙasar, taimakawa ci gaban bangaren masu zaman kansu, gina ingantattun cibiyoyin da za su tallafa wa kasuwanci da fasaha.
An rattaba hannu kan wannan yarjejeniya ce a ranar Laraba, 1 ga Oktoba 2025, a birnin Abidjan, babban birnin kasuwanci na Côte d’Ivoire, tsakanin Firayim Ministan Nijar, Ali Mahamane Lamine Zeine, da Shugaban Bankin BAD, Sidi Ould Tah.
Muhimman abubuwan da tallafin zai taimaka wajen cimmawa sun hada da, kafa sabbin layukan wutar lantarki da gyara tsofaffi, sauƙaƙa wa kamfanoni da ‘yan kasuwa samun lantarki, tallafa wa ƙananan masana’antu da masu fasaha, kara gasa da inganci a fannin masana’antu da kasuwanci, samar da guraben ayyuka ga matasa.
Firayim Minista Zeine ya bayyana godiyar gwamnati ga Bankin BAD bisa wannan tallafi mai muhimmanci, yana mai cewa wannan mataki zai taimaka wajen cimma burin gwamnatin Nijar na cin gashin kai a fannin makamashi, da kuma gina tattalin arziki mai dorewa.
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban BAD, Sidi Ould Tah, ya ce Bankin na da kwarin gwiwa kan alkiblar da Nijar ke bi, musamman yadda take mai da hankali wajen karfafa gasa da rage dogaro da waje.
Wannan tallafi na zuwa ne a daidai lokacin da Nijar ke fuskantar kalubale a fannin makamashi, sakamakon takunkuman da ake fama da su daga ƙasashen waje, inda gwamnati ke kokarin bunkasa hanyoyin cikin gida domin wadata jama'a da wutar lantarki.