26/09/2025
Gwamnatin Kano ta mika ƙorafe-ƙorafe da kuma na masu ƙin amincewa da ƙorafe-ƙorafen kan Ustaz Lawan Abubakar Shuʼaibu da aka fi sani da Triumph ga Majalisar Shura ta jihar domin nazari da bayar da shawara.
Nigerian spy TV ta rawaito cewa, mai magana da yawun sakataren gwamnatin jihar, Musa Tanko, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 25 ga Satumba, 2025.
Sanarwar ta ce ƙungiyoyin da s**a shigar da ƙorafe-ƙorafen sun haɗa da Safiyatul Islam of Nigeria, Tijjaniya Youth Enlightenment Forum, Interfaith Parties for Peace and Development, Sairul Qalbi Foundation, Habbullah Mateen Foundation, Imamai na masallatan Juma’a ƙarƙashin Qadiriyya, Committee of Sunnah Preachers da kuma Multaqa Ahbab Alsufiyya.
Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki don tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da mutunta addinai a jihar, tare da kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da gudanar da harkokinsu yadda ya kamata.
Kungiyoyin dai sun gabatarwa da gwamnatin ƙorafe-ƙorafe ne bisa zargin malamin da sakin baki a fagen Shugaba (s.a.w), zargin da magoya bayansa da malaman ɓangarensa s**a musanta, inda su ma s**a shigar da na su ƙorafin.