Zamani TV News

Zamani TV News Zamani TV kamfani ne dake kawo sahihan labaran da suke faruwa a Najeriya harma da ƙasashen ƙetare

ASUU ta fara yajin aiki a fadin ƙasar sak**akon rashin biyan albashi.Ƙungiyar Malamai ta Jami'o'in Najeriya (ASUU) ta um...
08/07/2025

ASUU ta fara yajin aiki a fadin ƙasar sak**akon rashin biyan albashi.

Ƙungiyar Malamai ta Jami'o'in Najeriya (ASUU) ta umurci mambobinta a jami’o’in tarayya da na jihohi da su dakatar da ayyukansu a fadin ƙasar, bayan da gwamnati ta ƙi biya albashin watan Yuni 2025, wanda ya wuce kwanaki 3 ba tare da an biyan ba wanda hakan ya sanya ƙungiya ta ayyana ƙa'idar yajin aikin “ba a biya ba, ba a aiki ba” .

Prof. Chris Piwuna, shugaban ƙasa na ASUU, ya bayyana cewa wannan jinkiri ba saboda matsalar fasaha ba ne, sai dai saboda rashin mayar da kuɗaɗen ga jami'o'i, wanda hakan ya sanya malaman suke bin gwamnatin kimanin Naira biliyan 10 na ƙarin hakkokin da ba'a biya ba .

A Jami’ar Jos (UNIJOS), Shugaban reshen ASUU, Prof. Jurbe Molwus, ya sanar da shiga yajin aiki tun daga 4 ga Yuli 2025, saboda ba a biya albashin Yuni ba haka ma Jami’o'in Abuja (UniAbuja) da ATBU Bauchi sun bi sahun wajen dakatar da ayyukansu bisa wannan sharadi.

-Zamani TV

Ci Gaba da Aikin Gina Sabuwar Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa (International Conference Center) a BauchiAiki na ci gaba da ...
08/07/2025

Ci Gaba da Aikin Gina Sabuwar Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa (International Conference Center) a Bauchi

Aiki na ci gaba da gudana na sabuwar Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa da Gwamnatin Jihar Bauchi ke ginawa, wacce ke daga cikin manyan ayyukan ci gaba da gwamnati Sanata Bala Mohammed Abdulkadir ke aiwatarwa don bunƙasa harkokin tattalin arziki, yawon buɗe ido, da kuma karɓar bakuncin tarukan ƙasa da ƙasa a cikin jihar.

Cibiyar wacce ake ginawa a babban birnin jihar Bauchi na ɗaya daga cikin ginshiƙan shirin Gwamna Bala Mohammed na tabbatar da ingantaccen ci gaban gine-gine da samar da muhimman ababen more rayuwa da za su amfani al’umma da ma baki daga waje.

-Zamani TV

An Koma Gasar Bayyana G-WagonAhmad XM, shahararren matashi dan forex kuma mamallakin XM Academy ya bayyana na shi G-wago...
08/07/2025

An Koma Gasar Bayyana G-Wagon

Ahmad XM, shahararren matashi dan forex kuma mamallakin XM Academy ya bayyana na shi G-wagon G63 AMG da ya siya a matsayin murnar ranar zagayowar haihuwarsa.

Tsohon kaftin din tawagar Super Eagles na Najeriya Ahmed Musa MON, OON ya k**a aiki gadan-gadan a matsayin babban Janar ...
08/07/2025

Tsohon kaftin din tawagar Super Eagles na Najeriya Ahmed Musa MON, OON ya k**a aiki gadan-gadan a matsayin babban Janar Manaja na Kano Pillars a ranar Litinin inda ya gana da shugaban ƙungiyar ta Kano Pillar Alhaji Ali Muhammad Umar tare da sauran membobi.

HOTUNA: Kano Pillars FC

Luka Modric zai koma kungiyar kwallon kafa ta AC Milan bayan kammala gasar Club world cupDan wasan tsakiya na Real Madri...
07/07/2025

Luka Modric zai koma kungiyar kwallon kafa ta AC Milan bayan kammala gasar Club world cup

Dan wasan tsakiya na Real Madrid, Luka Modric, wanda zai cika shekaru 40 a watan Satumba, na iya barin kulob din bayan dogon lokaci.

Modric ya koma Real Madrid daga Tottenham a shekarar 2012, kuma tun farkon watan Yuni ake danganta shi da yiwuwar komawa gasar Serie A ta Italiya k**ar yadda rahoton gidan talabijin na Channels ya tabbatar.

DANDALIN WASANNI DA ƊUMI ƊUMI!Ɗan wasan Bayern Munchen  Jamal Musiala ba zai dawo fata wa ƙungiyar wasa ba kafin watan N...
07/07/2025

DANDALIN WASANNI

DA ƊUMI ƊUMI!
Ɗan wasan Bayern Munchen Jamal Musiala ba zai dawo fata wa ƙungiyar wasa ba kafin watan Nuwamba ko Disamban shekarar 2025, sak**akon karye wa da ya yi a wasan su da PSG a gasar club World Cup.

DA DUMI-DUMI: Atiku Abubakar, Ya karbi bakuncin wasu fitattun masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ADC daga jihar Adamawa a g...
07/07/2025

DA DUMI-DUMI: Atiku Abubakar, Ya karbi bakuncin wasu fitattun masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ADC daga jihar Adamawa a gidansa da ke Abuja a safiyar yau.

Tawagar ta hada da shugaban jihar Hon. Adamu Shehu Yuhanna; Dan takarar gwamna na jam'iyyar a 2023, Alh. Usman Muhd Shuwa; da kuma mai baiwa reshen jihar shawara kan harkokin shari’a Hassan Ahmadu Har.

Tattaunawar tasu ta ta'allaka ne kan yanayin siyasar da ke ci gaba da bunkasa, dabarun inganta mulkin dimokuradiyya.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya jaddada kudirin Najeriya na ci gaba da mara wa ƙoƙarin hana gwajin ...
07/07/2025

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya jaddada kudirin Najeriya na ci gaba da mara wa ƙoƙarin hana gwajin mak**an nukiliya baya ta hanyar haɗin gwiwa da Ƙungiyar Hana Gwajin Mak**an Nukiliya ta Ɗuniya, wato Comprehensive Nuclear-Test-Ban Treaty Organization (CTBTO).

Shettima ya bayyana hakan ne a yau yayin da ya karɓi baƙuncin Babban Sakataren CTBTO, Dr. Robert Floyd, a wata ziyarar ban girma da ya kai masa a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

A cewar Shettima:
“Najeriya na da cikakken goyon baya ga yarjejeniyar hana gwajin mak**an nukiliya gaba ɗaya, tare da ƙudurin haɗin gwiwa da CTBTO wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a duniya."

Ya kara da cewa babu wata nasara da ake samu daga rikicin nukiliya, domin irin wannan rikici ba ya barin kowa da riba. Shettima ya jaddada cewa a halin yanzu nahiyar Afrika na cikin yakin neman yanci daga talauci da matsin rayuwa da sauyin yanayi.

“Muna cikin yaƙi da talauci. Muna fafutukar daidaita alakar tattalin arziki da muhalli a ƙasashen nahiyar Afirka, musamman yankin ƙasashe da ke ƙasa da hamadar Sahara. Babu dalilin da zai sa mu shiga harkar da ke da alaƙa da mak**an nukiliya. Abinda ke gabanmu yanzu shi ne yaki da kalubalen rayuwa na yau da kullum.”

A nasa bangaren, Dr. Robert Floyd ya yaba da matsayin Najeriya a cikin ƙasashen da ke ɗaukar batun hana gwajin mak**an nukiliya da muhimmanci, yana mai bayyana Najeriya a matsayin abokiyar aiki mai muhimmanci ga CTBTO a nahiyar Afrika.

Ziyarar ta kara tabbatar da matsayin Najeriya na zaman lafiya da sadaukarwa wajen tabbatar da duniyar da ba ta da barazanar mak**an nukiliya.

-Zamani TV

Gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP, Sen. Bala Mohammed Abdulkadir ya ce ba zai yi gaban...
07/07/2025

Gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP, Sen. Bala Mohammed Abdulkadir ya ce ba zai yi gaban kansa ba wajen zaɓar wanda zai gaje shi a zaɓen 2027.

Mafi yawa dai ya zamo k**ar wata al'ada ga gwamnonin jihohi da ke wa'adin mulki na biyu, su shige gaba wajen ganin naɗin ƴan takara da kuma shigewa gaba domin ganin dole sai shi ne zai gaje su bayan sun kammala mulkinsu.

Gwamnonin s**an kafa hujjar yin hakan ne da buƙatar ganin an ci gaba da aiwatar da ayyukan da s**a faro ko kuma kwaɗayin ci gaba da samar da ribar dimokuradiyya a karkashin tutar jam'iyyarsu.

To sai dai a hirar sa da BBC, gwamna Bala Mohammed ya ce baya da ra'ayin irin waccan al'ada ta gwamnonin Najeria.

Gwamnan ya ce jama'ar jihar Bauchi ne, musamman masu ruwa da tsaki a siyasance za su tantance wanda ya dace ya gaje shi a ƙarshen wa'adin mulkin nasa, k**ar yadda shi ma aka yi masa a baya.

A cikin wani hira da aka gudanar da mawakin siyasa na jam'iyyar APC Dauda Kahuta Rarara a DCL Hausa, mawakin ya bayyana ...
07/07/2025

A cikin wani hira da aka gudanar da mawakin siyasa na jam'iyyar APC Dauda Kahuta Rarara a DCL Hausa, mawakin ya bayyana jarumtar sa kan siyasa. Ya ce idan har ya tsaya takarar shugaban kasa, zai iya kayar da Atiku Abubakar da sauran 'yan hamayya, tare da duk wasu yan hadaka dake jam'iyyar ADC.

Wannan jawabi ya tayar da cece-kuce a kafofin sada zumunta, domin an ji wasu suna ganin yana nuna girman kai da wulakanci ga 'yan takara masu karfi irin su Atiku.

Menene ra'ayoyin ku?

Zan yaƙi duk wanda ya yi sata idan na zama shugaban ƙasa - AtikuTsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya y...
06/07/2025

Zan yaƙi duk wanda ya yi sata idan na zama shugaban ƙasa - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi alwashin fada da duk wanda ya ce zai yi sata muddin ya zama shugaban ƙasa.

Atiku ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin tawagar masu ruwa da tsaki daga jihar Gombe da s**a kai masa ziyara, karkashin jagorancin tsohon Sanata Idris Abdullahi.

Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen cin hanci a Najeriya.

"Ya isa haka, kowace ƙasa na cigaba amma ban da mu sak**akon wasu mutane kalilan da kuma rashin gwamnati na gari," in ji Atiku.

Ya ce shugabannin haɗaka karkashin inuwar jam'iyyar ADC, za su yi aiki tukuru domin kawo canji mai nagarta wanda zai inganta rayuwar ƴan Najeriya.

Yanzu da Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta kaddamar da sabbin shugabannin ta a wani mataki na tunkarar zabe...
02/07/2025

Yanzu da Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta kaddamar da sabbin shugabannin ta a wani mataki na tunkarar zaben 2027, wani tasiri kuke ganin jam'iyyar zata yi wajen nasara a kan gwamnatin Bola Tinubu?

Ina kuma makomar babban jami'yyar adawa na PDP?

Adresse

Democratic Republic Of The

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque Zamani TV News publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Partager