28/06/2025
ZAMANI RIGA...: MANUFAR MUJALLAR AJAMI-BOOKO A WANNAN ZAMANI ABIN A YABA NE DA SHIGA CIKIN LAMARIN MUJALLAR DOMIN FIDDA 'DAN DUMA DAGA CIKIN KABEWA !!!
زَامَنِي رِيغَ...: مَنُفَر مُجَلَّر عَجَمِي-بُوكُو أَ وَنَّن زَامَنِي أَبِن أَ يَبَ نٖي دَ شِغَ ثِكِن لَمَرِن مُجَلَّر دُومِن فِدَّ طَن دُمَ دَاغَ ثِكِن كَبٖيوَ!!!
Shi dai rubutun ajami, wani nau'in salon rubutu ne da Bahaushe ya samar daga harrufan Larabci. Wannan salon rubutu yana ɗaya daga cikin daɗaɗɗun hanyoyin rubutu da aka yi amfani da ita a Ƙasar Hausa. Zarruƙ, Kafin Hausa, da Al-Hassan (1987), sun ce an haura sama da shekaru ɗari da hamsin ana amfani da wannan hanya ta rubutun ajami a Ƙasar Hausa kafin zuwan rubutun boko. Mashahuran malaman Musulunci na ƙarni na goma sha tara kamar irin su Mujadaddi Shehu Ɗanfodiyo da almajiransa, sun yi amfani da wannan salon rubutu wajen rubuta littattafai da waƙoƙi da isar da sakonni.
شِي دَي رُبُوتُن عَجَمِي٬ وَنِ نَوعِن سَلُون رُبُوتُ نٖي دَ بَهَوشٖي يَا سَمَر دَاغَ هَرُفَّن لَارَبثِي. وَنَّن سَلُون رُبُو نٖي دَ بَهَوشٖي يَا سَمَر دَاغَ هَرُفَّن لَارَبثِي. وَنَّن سَلُون رُبُوتُ يَنَ طَيَ دَاغَ ثِكِن دَطَطُّن هَنيُويِين رُبُوتُ دَ أَكَ يِي أَمفَانِ دَ إِتَ أَ قَسَر هَوسَ. زَرُّق٬ كَفِن هَوسَ٬ دَ أَلحَسَن (١٩٨٧)٬ سُن ثٖي أَن هَورَ سَمَ دَ شٖيكَرُو طَرِي دَ هَمسِن أَنَا أَمفَانِي دَ وَنَّن هَنيَ تَا رُبُوتُن عَجَمِي أَ قَسَر هَوسَ كَافِن زُووَن رُبُوتُن بُوكُو. مَشَهُورَن مَالَمَن مُسُلُنثِي نَا قَرنَي نَا غُومَ شَا تَارَ كَمَر إِرِن سُو مُجَدَّدِي شٖيحُ طَنفُودِيُو دَ أَلمَاجِرَنسَ٬ سُن يِي أَمفَانِي دَ وَنَّن سَلُون رُبُوتُ وَجَن رُبُوتَ لِتَّتَّافَي دَ وَاقُوقِي دَ إِسَر دَ سَقُنِّي.
Farfesa Bunza (2002), ya fassara shi da cewa, “ajami na nufin rubutun harshen Hausa cikin harufan Larabci”.
فَرفٖيسَ عَلِيُّ ﷴُ بُنزَا(٢٠٠٢)٬ يَا فَسَّارَ شِي دَ ثِيوَ٬ عَجَمِي نَا نُوفِن رُبُوتُن هَرشٖين هَوسَ ثِكِن هَرُفَّن لَارَبثِي".
Dangane da yaushe ne kuma a ina aka fara yin rubutun ajami kuwa, masana fannin Hausa sun yi rubuce-rubuce masu yawa kowa da nasa ra’ayin. Farfesa Bunza (2002), yana ganin cewa rubutun ajami ya wanzu a Ƙasar Hausa tun kafin zuwan Musulunci, ta in da ya kafa hujjoji da zuwan Bayajidda, da kuma dangantakar cinikayya da ta sarauta da ta wanzu tsakanin Ƙasar Hausa da kuma Ƙasashen Larabawa.
دَنغَنٖي دَ يَوشٖي نٖي كُمَا أَ إِنَا أَكَ فَارَ يِن رُبُوتُن عَجَمِي كُوَا٬ مَسَنَا فَنِّن هَوسَ سُن يِي رُبُوثٖي-رُبُوثٖي مَاسُ يَوَ كُووَ دَ نَاسَ رَعَيِن. فَرفٖيسَ عَلِيُّ ﷴُ بُنزَا(٢٠٠٢)٬ يَا نَ غَنِنثٖيوَ رُبُوتُن عَجَمِي يَا وَنزُو أَ قَسَر هَوسَ تُن كَافِن زُووَن مُسُلُنثِي٬ تَ إِندَ يَا كَفَ هُجُّوجِي دَ زُووَن بَايَجِدَّ٬ دَ كُمَا دَنغَرتَكَر ثِنِكَيَّ دَاتَا سَرَوتَ دَاتَ وَنزُو ثَكَانِن قَسَر هَوسَ دَ كُمَا قَسَشٖين لَارَبَاوَ.
Shi kuwa Ɗanmasanin Kano, Alhaji (Dr.) Yusuf Maitama Sule, ya bayyana cewa malam Ɗanmasani na Katsina shi ne ya ƙirƙiro rubutun ajami na Hausa. A wannan ra'ayi nasa yau kenan ana lissafa shekarun ajami kusan shekaru ɗari bakwai kenan.
شِي كُوَا طَنمَسَنِن كَانُو٬ أَلهَجِ (دَكتَ) يُوسُف مَيتَامَ سُلٖي٬ يَا بَيَّنَ ثٖيوَ مَالَم طَنمَسَنِي نَا كَشِنَه شِي يَا قِرقِرُو رُبُوتُن عَجَمِي نَا هَوسَ. أَ وَنَّن رَعَيِي نَاسَ يَو كٖينَن أَنَ لِسَّافَ شٖيكَرُون عَجَمِي كُسَن شٖيكَرُو طَرِي بَكُوي كٖينَن.
Sai dai, wani abu da ya fito fili shi ne cewa yaɗuwar addinin Musulunci a Ƙasar Hausa ta taimaka gaya wajen shaharar wannan salo na rubutu. Sannan kuma ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban rubutu a cikin harshen Hausa.
سَيدَي٬ وَنِ أَبُو دَ يَا فِتُو فِيلِي شِي نٖي ثٖيوَ يَطُوَر أَدِّينِن مُسُلُنثِي أَ قَسَر هَوسَ يَا تَيمَكَ غَايَ وَجَن شَهَرَر وَنَّن سَلُون رُبُوتُ.
سَنَّن كُمَا يَا بَايَر دَ غَغَرُمَر غُدُمُّوَا وَجَن ثِي غَبَن رُبُوتُ أَ ثِكِن هَرشٖي هَوسَ.
Nazarin wadannan zantuka na masana ya zaburarar da mawallafin 'Mujallar Ajami-Booko', malam Rabi'u Ibrahim wanda aka fi sani da suna 'Go slow' , kuma haifaffen garin Katsina domin kafa wannan kafar labarai don kusanto da cike gibin da ke tsakanin masu ilimin boko da malamanmu na Tsangaya, masana Littafin Allah, ( Hadisai da Littafan Ilimi)da Almajiransu wadanda tun tali-tali suke amfani da haruffan Larabci (Ajami) wajen isar da sakunansu.
نَزَرِين وَطَنَّن زَنتُتُّكَ نَا مَسَنَا يَا زَابُرَر دَ مَوَلّافِن "مُجَلَّر عَجَمِي-بُوكُو" , مَالَم رَابِعُ إِبرَاهِيم وَندَ أَكَ فِ سَنِي دَ سُونَ 'غُوسِلُو' كُمَا هَيفَفّٖين غَرِن كَشِنَه دُومِن كَفَ وَنَّن كَفَر لَابَرَي دُون كُسَنتُو دَ ثِكٖي غِيبٖين دَ كٖي ثَكَانِن مَسُ إِلِمِين بُوكُو دَ مَلَمَمُّو نَا ثَنغَيَ٬ مَسَنَا لِتَّافِن أَللَّه٬(هَدِيسِي دَ لِتَتَّفَن إِلِمِي) دَ أَلمَاجِرَنسُ وَطَندَ تُن تَلِ-تَلِ سُكٖي أَمفَانِي دَ هَرُفَّن لَارَبثِي(عَجَمِي) وَجَن إِسَر دَ سَاقُنَنسُ.
Ganin yadda ake ta samun sabani tsakanin Malamammu na Tsangaya a gefen abin da aka rubuta a matsayin Jarida ko kuma abin da aka watsa a cikin kafar watsa labarai na zamani "social media"ko wadanda aka saba da su na al'ada "conventional" media, shi ne ya sa "Mujallar Ajami-Booko" ta fito don ta yi sulhu tsakani.
غَنِن يَدَّ أَكٖي تَا سَامُن سَبٰنِي ثَكَانِن مَلَمَمُّو نَا ثَنغَيَ أَ غٖيفٖين أَبِن دَ أَكَ رُبُوتَ أَ مَثَيِن جَرِيدَ كُو كُمَا أَبِن دَ أَكَ وَاثَ أَ ثِكِن كَفَر سَادَروَر زَامَنِي "سُوشِيَل مِيدِيَ" كُو وَطَندَ أَكَ سَابَ دَ سُ نَا أَلعَادَ "كُونبٖينشِنَل مِدِيَ", شِي نٖي يَسَ "مُجَلَّر عَجَمِي-بُوكُو" تَا فِتُو دُون تَ يِي سُلهُ ثَكَنِي.
Gano dalilan wannan sabani da Mujallar Ajami-Boko ta yi ta sa ta yunkuro don wallafa labarai da makaloli makamantan irin wadanda ake bugawa a jaridun harshen Turanci da Larabci da Hausar Boko tsantsa, domin wayar da kai da ilimantarwa da fadakarwa da ma nishadantarwa ga al'ummar da ke zaune a kasar Hausa da ma masu sha'awar karatun ajami musamman wadanda ba su iya karanta wani rubutun da ba ajami ba.
غَانُو دَلِيلَن وَنَّن سَافٰانِي دَ مُجَلَّر عَجَمِي-بُوكُُو تَايِي تَاسَ تَا يُنقُرُو دُون وَلَّافَ لَابَرَي دَ مَقَالُولِي مَكَمَنتَن إِرِن وَطَندَ أَكٖي بُغَاوَ أَ جَرِيدُن هَرشٖين تُورَنثِي دَ لَارَبثِي دَ هَوسَر بُوكُو ثَنثَ٬ دُومِن وَايَر دَ كَي دَ إِلِمَنتَروَ دَ فَطَكَروَ دَ مَا نِشَاطَنتَروَ غَ أَلعُمَّر دَ كٖي زَونٖي أَ قَسَر هَوسَ دَ مَا مَاسُ شَعَوَر كَرَاتُن عَجَمِي مُسَمَّن وَطَندَ بَاسُ إِيَ كَرَنتَ وَنِي رُبُوتُن دَ بَا عَجَمِي بَا.
Kuma Mujallar Ajami-Boko ta fahimci cewa, salon labarai da rubutun dan shekara tisi'in ya bambanta da na dan shekara arba'in haka na dan shekara talatin abin da yawo kasa na shi salon daban yake.
Wannan abu ba kome ya kawo shi ba face, kowa na da irin rayuwar da ya tashi cikinta.
كُمَ مُجَلَّر عَجَمِي-بُوكُو تَا فَهِمثِي ثِيوَ٬ سَلُون لَابَرَي دَ رُبُوتُن طَن شٖيكَرَ تِسِعِن يَا بَمبَنتَ دَ نَا طَن شٖيكَرَ أَربَعِن هَكَ نَا طَن شٖيكَرَ تَلَاتِن أَ بِن دَ يَاوُو قَسَ نَاشِ سَلُون دَبَن يَكٖي. وَنّن أَبُو بَا كُومِي يَا كَوُوشِ بَا فَاثٖي٬ كُووَ نَادَ إِرِن رَايُوَر دَ يَا تَاشِ ثِكِنتَ.
Fahimtar wannan danbarwa ta sa Mujallar Ajami da Boko cewa idan ana son daidaito a cikin wannan lamari, to salon rubutun yanzu da zai hade malamanmu na tsangaya da 'yan bokonmu ya kasance gamin gambiza, ya kunshi abin da kowane bangare ya sani. Sannan masana lamuran da ke zuwa suna dawowa sun ce suna da tabbacin cewa, ta hanyar farfado da tsarin karatu da rubutun Ajamin Hausa wanda ake amfani da shi a makarantun addinin Musulunci, wadanda s**a hada da makarantar Tsangaya da Islamiyya da kuma na Allo ; sannan a gauraya shi da da rubutun boko zai daidaita bisa kashin bayan zamani.
فَهِمتَر وَنَّن دَمبَروَ تَاسَ مُجَلَّر عَجَمِي دَ بُوكُو ثِيوَ إِدَن أَنَ سَن دَيدَيتُو أَ ثِكِن وَنَّن لَمَرِي٬ تُو سَلُون رُبُوتُن يَنزُو دَ يَكَمَاتَ دَ زَي هَطٖي نَا مَلَمَمُّو نَا ثَنغَيَ دَ نَا يَن بُوكُومُّومُّ يَا كَسَنثٖي غَمِن-غَمبِيزَ٬ يَا قُنشِ أَ بِندَ كُووَنٖي بٰنغَارٖي يَا سَنِي. سَنَّن مَسَنَا لَمُرَّن دَ كٖي زُووَ سُنَ دَاوُووَ سُن ثٖي٬ سُنَ دَ تَبَّ ثِن ثِيوَ٬ تَا هَنيَر فَرفَاطُو دَ ثَرِن كَرَاتُو دَ رُوبُوتُن عَجَمِين هَوسَ وَندَ أَكٖي أَمفَنِي دَ شِي أَ مَكَرَنتُن أَدِّينِن مُسُلُنثِ٬ وَطَندَ سُكَ هَطَ دَ مَكَرَنتَر ثَنغَيَ دَ إِسلَمِيَّ دَ كُمَا نَا أَلاُّو ; سَنَّن أَ غَورَيَا شِي دَ رُبُوتُن بُوكُن زَي دَيدَيتَ بِسَ قَشِن بَايَن زَامَنِي.
Daga Karshe, cikin murna da farin ciki Mujallar Ajami-Boko wadda ta hada da sashen Rediyo da Talabijin a kafar Sadarwar Zamani (Social Media) kuma take gabatar da wannan aiki nata, saboda ta sani kuma tana alfahari da tunkaho da Musulunci a kasar Hausa kuma dalilin samuwar Musuluncin rubutun ajami ya inganta har ya samu tagomashi a wancan zamani har ya dara wa tsara ; to don haka, ko ba a yaba wa wannan kafa ba a kan wannan aikin, to za a ya ba mata a kan kyakkyawar niyyarta a kan manufar.
دَاغَ قَرشٖي٬ ثِكِن مُرنَ دَ فَرِن ثِكِ مُجَلَّر عَجَمِي-بُوكُو وَدَّ تَا هَطَ دَ سَشٖين رٖيدِيُو دَ تَلَبِجِن أَ كَفَر سَدَروَ تَا زَامَنِي (سُوشِيَل مِيدِيَ) كُمَ تَكٖي غَبَاتَر دَ وَنَّن أَيكِ نَاتَ٬ سَبُودَ تَا سَنِي كُمَ تَنَ أَلفَهَرِي دَ تِنقَاهُو دَ مُسُلُنثِ أَ قَسَر هَوسَ كُمَ دَلِيلِن سَمُوَر مُسُلُنثِن رُبُوتُن عَجَمِي يَا إِنغَنتَ هَر يَا سَمُ تَغُومَشِي أَ وَنثَن زَامَنِي يَا طَرَ وَ ثَارَ ; تُو دُون هَكَ٬ كُو بَعَ يَبَ وَ وَنَّن كَفَ بَ أَ كَن وَنَّن أَيكِن٬ تُو زَاعَ يَبَ مَتَ أَ كَن كٖيككٰاوَر نِيَّرتَ أَ كَن مَنُفَر.
Wannan kafa ta Mujallar Ajami-Boko na taya dukkan musulmin duniya (musamman wadanda ke zaune a kasar Hausa), murnar shigowa sabuwar shekarar Musulunci.
وَنَّن كَفَ تَا مُجَلَّر عَجَمِي-بُوكُو نَا تَيَ دُكَّن مُسُلمِن دُونِيَ (مُسَمَّن وَطَندَ كٖي زَونٖي أَ قَسَر هَوسَ)٬ مُرنَر شِغُووَ سَبُوَر شٖيكَرَر مُسُلُنثِ.