Bakandamiya TV

Bakandamiya TV Informations de contact, plan et itinéraire, formulaire de contact, heures d'ouverture, services, évaluations, photos, vidéos et annonces de Bakandamiya TV, Chaîne de télévision, Douala.
(2)

Bakandamiya TV tasha daya tilo dake watsa shirye-shiryen ta cikin harshen hausa zalla sannan tana maïda hankali akan al'adu zamantakewar malam bahaushe tare da kawo muku labaru masu inganci domin sanin me duniya take ciki.

31/08/2026

LABARU DA DUMI DUMI NA 31 AGUSTA 2026

31/08/2026

AFRIKAN MU A YAU NA 24 AGUSTA 2026

31/08/2026

LABARAN DUNIYA NA 31 AGUSTA 2026

31/08/2026

WANI MAI TAIMAKON AL'UMMA KUMA DAN TAKARAR KUJERAR SENATAN GOMBE TA KUDU DR. JERRY JOSEPH DAMARA YA BAYAR DA GUDUNMAWAR NAIRA MILIYAN BIYAR DOMIN TALLAFA WA GASAR KARATUN ALƘUR’ANI TA SHEKARA-SHEKARA DA ƘUNGIYAR IZALA TA SHIRYA A BAMBAM, ƘARAMAR HUKUMAR BALANGA TA JIHAR GOMBE.

31/08/2026

LABARUN CIKIN GIDA NA 29 AGUSTA 2026

- YAWAITAR KASHE MATA
- KAZANTA A BIRNIN YAOUNDÉ
- KOMAWAR DALIBAI MAKARANTA

Al’umma a Kano na ci gaba da jimamin rasuwar fitaccen mai sharhi kan harkokin jama’a, ɗan jarida kuma marubuci, Bello Mu...
30/08/2026

Al’umma a Kano na ci gaba da jimamin rasuwar fitaccen mai sharhi kan harkokin jama’a, ɗan jarida kuma marubuci, Bello Muhammad Sharada, wanda ya rasu yana da shekaru 56.

Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Bello Sharada ya shahara wajen yin sharhi da nazari kan al’amuran siyasa da sauran batutuwan da s**a shafi Najeriya, musamman ta kafafen sada zumunta, ciki har da Facebook.

Ya kasance mai goyon bayan siyasar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, kuma ya shafe shekaru yana bayar da gudunmawa wajen bunkasa muhawarar jama’a ta hanyar rubuce-rubuce da sharhinsa kan siyasa da sauran al’amuran ƙasa.

Bayan rasuwarsa, abokai, abokan aiki da sauran al’umma sun bayyana alhininsu, inda s**a bayyana marigayin a matsayin mutum mai kishin rubutu da bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen wayar da kan jama’a.

Anyi jana’izarsa da misalin ƙarfe 8:00 na safe ranar Lahadi a Sharada Fegi, cikin ƙaramar hukumar Kano Municipal, bisa tsarin addinin Musulunci.
Marigayin ya rasu ya bar iyalansa da ’yan uwa da abokan arziki.

Allah Ya jikansa da rahama, Ya bai wa iyalansa da ’yan uwansa haƙurin jure wannan rashi. Amin.

A cewar sanarwar da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar...
30/08/2026

A cewar sanarwar da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce shugaban ƙasar zai fara dira ne a birnin Landan na ƙasar Birtaniya a zangon farko na tafiyar.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya bayan kammala hutun nasa domin shiga cikin shirye-shiryen yaƙin neman zaɓe gabanin zaɓen da aka shirya gudanarwa a watan Janairun 2027,

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya gana da Shugaban Kamfanin Hummels Water Engineering na Hungary...
30/08/2026

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya gana da Shugaban Kamfanin Hummels Water Engineering na Hungary, Injiniya Peter Hummel, a Abuja, domin nemo mafita kan matsalar matatar ruwan Alkaleri.

Ganawar ta biyo bayan bukatar Gwamnan ga injiniyoyin Hungary da s**a girka matatar, da su dawo Jihar Bauchi domin gudanar da gyare-gyare da aikin fasaha da zai dawo da tashar cikin cikakken aiki.

Matatar ruwan, wadda gwamnatin Hungary ta gina tare da bai wa Najeriya a matsayin tallafin jin kai a shekarar 2023, tana da karfin samar da kusan lita dubu 40 na ruwa mai tsafta a kullum, wanda ke amfanar da kimanin mutane dubu 4.

Gwamna Bala Mohammed ya ce matatar ta daina aiki ne sakamakon matsalolin kula da ita da gudanar da aikinta, yana mai cewa gwamnati ta dauki matakin dawo da injiniyoyin da s**a girka ta domin magance matsalar.

Gwamnan ya gode wa gwamnatin Hungary da kamfanin Hummels Water Engineering bisa hadin gwiwa, yana mai tabbatar da aniyar gwamnatinsa ta samar da ingantattun hanyoyin ruwan sha da za su taimaka wa al’ummomin da ke fama da karancin tsaftataccen ruwa a fadin jihar.

Bola Oyebamiji, ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Osun, ya amince da saka...
30/08/2026

Bola Oyebamiji, ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Osun, ya amince da sakamakon zaɓen gwamnan jihar tare da taya Ademola Adeleke murna, makonni biyu bayan gudanar da zaɓen.

​A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Oyebamiji ya mika godiyarsa ga mambobi da magoya bayan jam’iyyar APC bisa tsayawa tsayuwar daka da s**a yi a lokacin yaƙin neman zaɓe, inda ya yaba da sadaukarwarsu, juriyarsu, da kuma addu’o’in da s**a gudanar.

​Bugu da ƙari, ɗan takarar ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da su ajiye bambance-bambancensu domin haɗa kai da sake gina jam’iyyar gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

​Hukumar zaɓe dai ta sanar da Adeleke ne a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 15 ga watan Agusta.

29/08/2026

Hawan Maulidi Sarkin Kano Mohamadu Sunusi 2 na 29 /8/2026

Adresse

Douala

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque Bakandamiya TV publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Raccourcis

Partager