06/05/2025
Daga Abubakar Ado
BARI NA FADA MUKU SU WANENE HAUSAWA.
"Idan kai bahaushe ne da baka cika yin karatun litattafai ba, to yana da kyau ka sadaukar da minti biyar na rayuwarka kasan wanene kai"
Yaren hausa ya fito daga cikin dangin yarukan nan da ake kira "Afro Asiatic" ko kuma "Hemito-Semito" su hudu ne akwai Hausa, Arabic, Hebrew (Yahudanci), Coptic. Idan baka sani ba yaren hausa ya fito daga dangin yaruka mafi girman tarihi da alfarma a duniya.
Sune mazauna yankin Arewacin Nigeria, da kuma kudancin Niger anan s**a fi yawa amma ana samu su a yankunan Africa da yawa, kamar Chad, Ghana, Sudan, Benin, Togo, Cameroon, Senegal, Eritrea, Mauritania, Libya, Gabon, Ivory coast, Burkina Faso dss.
Kai ana samun hausawa har a yankunan da bana africa ba, misali akwai hausawa sama da mutum 1million a kasar Saudi Arabia. A yanzu haka harshen hausa official language ne da yana cikin yarukan da masarautar saudiya take fassara abubuwan addini dashi.
Kabilar hausa sune sune yaren da s**a fi kowa yawan "Native Speakers" a Africa, wato asalin jinin yare da mutum 65million, sannan sune s**a fi kowane yare yawan Speakers a Africa da mutum 154million.
Yare biyu ne kadai a africa recognize languages a duniya. Na farko Hausa ne, sai kuman Swahili. Shiyasa zakaga kusan komai na duniya indai ana fasaara shi, to akwai na hausar shi da kuma Swahili wani lokacin, banda wadannan yarukan babu wasu kuma.
Hakan yasa kabilar hausa ta shiga cikin yare 10 da s**a fi kowane yare karfin fada aji a duniya, akwai yaruka a duniya sama da dubu bakwai da dari daya 7,100. Amma kabilar ta samu matsayin shiga cikin 10 mafiya karfi. Nasan ba kowa yasan wannan ba.
Shine kadai yaren da ake koyarwa a jami'oin wasu kasashen da ba Nigeria ba, akeyi degree har professor ake zama. Shiyasa zakaje kasar waje turai kaga ance maka wannan professor ne a hausa, kuma bai ma taba zuwa arewacin Nigeria ba. Kamar dai yadda ake iya zama professor a English kuma baka taba zuwa England ba.