01/12/2025
Iyalai da almajiran marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun ayyana cewar daga yanzu dukkani lamaran jagoranci za su ke amsar izinin ne daga wajen Shariff Ibrahim Saleh Al’husainiy wanda ya kasance Khalifan Ɗarikar Tijjaniyya a faɗin ƙasar nan.
Sun ayyana cewar a yanzu haka dukkanin biyayyarsu ya koma ga Sharif Saleh. A bisa wannan, yanzu almajiran Sheikh Dahiru sun miƙa dukkanin biyayyarsu ga Sharif Saleh.
Babban ɗan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi shi ne ya sanar da wannan matakin da muba'iyarsu a lokacin da tawagar Sharif Saleh s**a kawo ziyarar ta'aziyyar rasuwar Shaikh Dahiru a ranar Lahadi, daga cikin tawagar har da babban limamin babban masallacin ƙasa, Farfesa Ibrahim Ahmad Makari.
Babban ɗan Shehin ya ci gaba da cewa tun kafin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bar musu wasiyya da cewa in ya rasu Sharif Saleh ne zai jagoranci sallarsa kuma ya musu nuni da yi masa biyayya a ɓangaren lamuran addini.
Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya ce lamarin jagoranci ba lamari ne na wasa ba, don haka sun maida dukkanin biyayyarsu ga Sharif Saleh Ibrahim Saleh Al’husain wanda ya ke fitaccen malamin Ɗarikar Tijjaniyya ne a ƙasar nan.
Dan Shehin ya sake roƙon Sharif Saleh da cewa daga yanzu dukkanin lamuran da za su gudanar a rayuwa su na neman ya ke ba su izni kafin su yi. Ya ce yanzu komai za su koma saurara daga gareshi ne a matsayinsa na Khalifan Tijaniyya a Nijeriya.
Ya tabbatar da cewa yanayin dangatar kusanci da ta abota da ke tsakanin Sheikh Dahiru Usman da Sheikh Sharif Saleh babu mai isa misaltawa, ya ce sun kasance aminai na ƙut waɗanda suke tafiyar da lamuransu a tare-tare a kowani lokaci.
Babban ɗan Shehin ya tunatar da al'umma kan muhimmancin haɗin kai da biyayya wa Khalifanci domin samun tsira duniya da lahira.
Tun da farko da ya ke magana Farfesa Ibrahim Ahmad Makari, ya ce duk duniya ba wanda zai ji zafin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi kamar Khalifa Sharif Saleh saboda kusancin da ke tsakaninsu ta addini da ta abota.
I