
20/10/2024
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da kujerun zaman dalibai da gadajen kwantar da marasa lafiya wanda Sanatan Kano ta Kudu Alhaji Abdurrahman Kawu Sumaila ya samar a yankinsa.
Da yake jawabi yayin kaddamar da kayan, gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa Sanatan Kano ta Kudu bisa kishinsa na inganta ilimi da kiwon lafiya a jihar Kano musamman a yankin da yake wakilta.
Ya yami Kira ga sauran sanatocin jihar Kano da suyi koyi da Sanata Kawu Sumaila wajen samar da ayyukan cigaba da kyautata rayuwar al'uma.
A nasa jawabin, Sanatan Kano ta Kudu Alhaji Abdurrahman Kawu Sumaila yace ya samar da kayan ne domin tallafawa yunkurin gwamnatin jiha na Inga ilimi da kiwon lafiya a jihar Kano wanda ya Kai ga saka dokar ta baci a kan ilimi.
Daga nan ya yi alwashin samar da karin kayan koyo da koyarwa a makarantun Kimiyyar dake yankin da samar musu da karin malamai domin magance matsala karancin Malamai da makarantun yankin ke fuskanta.
Kayan da Sanata Kawu Sumaila ya samar sun hada bençinan zaman dalibai dubu uku da gadajen kwantar da marasa lafiya guda daya da sauran kayan kiwon lafiya da na koyo da koyarwa.