
23/02/2025
A Yau Ake Bikin Yaye Wasu 'Yan Agaji 87 Ta Kungiyar Jama'atu Nasril Islam, Karamar Hukumar Rafi Da Sukayi Atisaye Akan Muhimmancin Agaji Na Farko Da Tarbiya A Addinin Islama Na Tsawon Kwana Bakwai(7). a Farfajiyan Fadan Mai Martaba Sarkin Kagara.
Bikin Ya Samu Wakilcin Mai Martaba Uban Kasan Kagara, Mal Ahmad Garba Gunna(Attahiru ||), Wanda Sakataren Majalisan Masarautan Kagara Ya Wakilce Shi, Na'ibin Imam Na Daya(1), Mal Aminu Yahaya Abdullahi Balarabe, JNI Asst Hajj Operation Kaduna State, JNI Chairman Birnin Gwari, JNI Niger State Intelligent Officer,Shugabanni Na Karamar Hukumar Rafi Da Sauran Iyaye,Malamai Da Musulmai Gaba Daya.
Na'ibin Imam Yayi Takaitacciyan Nasiha Akan Muhimmancin Biyayya Ga Iyaye,Kyautata Masu Da Kuma Tarbiyya Da Biyayya A Tsakanin Musulmai. Ya Qara Da Addu'an Neman Zaman Lfya, Arziki Mai Albarka Da Ikon Aiwatar Da Ibadan Watan Ramadan Mai Zuwa,Yayi Addu'a Ga Mai Martaba Sarkin Kagara, Akan Allah Ya Qara Mashi Lfya Da Nisan Kwana Mai Albarka 🤲 🤲 🤲, Allah Ya Bashi Ikon Cigaba Da Adalci A Mulkin Shi🙏
Allah Ya Qara Daukaka Masarautan Kagara,Jahar Neja Da Najeriya Gaba Daya.
Sign: JNI Media Rafi Division.