20/07/2025
Copied
UWA UWACE
Jiya naje Gonar Shinkafa da Barayi s**a addabemu , se karfe 8pm na dare nafito daga Gona , ana mamakon ruwan sama , dakyar nakawo Bakin Kwalta saboda Karfin ruwan da akeyi , nazo Bakin t**i na tsaya nawanke jikina saboda na dauko Tarba dayawa .
Can ina Kokarin nabuga Babur dina se ga Yaro yazo Inda nake , kallo Daya nayiwa Yaron duk da aduhune nafahinci yana Cikin damuwa . Nace kai daga ina kake haka , ina zakaje acikin ruwan nan haka , ga duhu ?
Yace Baba Dan Allah katemakamini karagemini hanya , nace ina zakaje , Yace Kwanar Liman na Kwatalo zeje , nadaukoshi mukataho duk da ana Ruwa sosai haka mukai Karfin Hali mukataho , mina tafiya Yaron Yace Baba nagode , nace Masa daga ina kake haka , yacemin Baba tun Jiya nabaro Azare akafa nazo Zaki .
Ni almajirine yau Shekara 3 Banga Mahaifiyata ba , Kullum na kwanta barci se ina mafarkin babata tana Kuka , nafadawa malamin mu Yace bakomai zan Dena . Har abin Yafara damuna, akarshe na yankee Shawarar se nakoma Gida naga Mahaifiyata , nafadawa malamin Yace bazanjeba , Jiya aka kaimu aikin barema na Noma , Kawai nagudo.
Can nacemasa to yanzu Idan nasaukeka a inda Kace kana da kudin motar zuwa Garin naku , Yace a a , amma daga inda zan saukeshi zuwa garinsu banisa , akarshe yafadamin sunan Garinsu , lokacin da mukazo inda zan saukeshi se tausayinsa yakamani saboda yarone karami, haka nayi Karfin Hali nawuce dashi Garinsu , Allah yatemaka Ruwa yayi sauki daf da Garinsu.
Kaitsaye muka Isa Gidansu wajen karfe 9:30 na dare , har an kwanta saboda yanayi na Damina , mina Isa Kofar Gidan Yaro ya cillawa Babarsa Kira , Kai Kace tasan da zuwansa , ta amsa , segata aguje, tana ganinsa tafashe da Kuka , tana cewa , Allah nagodemaka ashe zan kara Ganin me sunan Baba , can sega uban Yaron yafito , yana zuwa yakama Fada , ta Inda Yashiga bata nan yake fita ba .
Can nace yanzu kai Malam ko sallama bakayimin ba , Kawai kakama fada, Mahaifiyar Yaron tacemin Malam nagode Allah yabiyaka da Gidan Aljanna . Yau Shekaru 3 ina Kuka har nagaji ,Uban Yaron nan yadaukeminshi yakaishi makarantar Allo ,kuma yaki fadamana inda yakaishi . Yau zamana Yakare a gidan sa , dama dan nasamu Labarin inda yakaimun Dana shiyasa nake zaune dashi , amma yau Allah ya amsa Addua ta.
Can nace to bewar Allah Yakiyaye Gaba ,ni ma akwai sauran tafiya agabana Gida zanje , ban iso Gida se can tsakiyar dare . But Alhamdulillah Naji Dadi sosai yadda naga uwar Yaron can tashiga farin Ciki saboda ni.
Daga Shafin: Engr Ibrahim Said Uba
Follow Adam Adam