Muhammad S Tomo

Muhammad S Tomo Public Awareness

23/05/2026

Me ka sani kan Makabarta Mafi Girma a Duniya !? 👇🏽

Muna Rayuwa ne iri biyu ta zahiri da ta badini , kuma kamar yadda mutum ke da bukatar ci ,sha da tsaftace gabban sa na z...
22/05/2026

Muna Rayuwa ne iri biyu ta zahiri da ta badini , kuma kamar yadda mutum ke da bukatar ci ,sha da tsaftace gabban sa na zahiri haka badinin sa ke bukatar wannan .

Akwai mamaki ka ga ubangiji Allah ya kira mutanen da ke ji da gani da kurame makafi a wurare da dama cikin Kur’ani mai tsarki .

Idan kaga wani ya kamu da wata cuta kila ya samu rashin daidaito ne wurin amfani da wadansu ababe wanda wannan ya zamo silar kamuwar sa da wannan cuta ko kuma wasu sinadarai ko muce kwayoyin halitta ne s**a samu matsala .

Idan akwai yiwuwar ka kamu da wannan cuta 😳…Hausawa s**a ce Rigakafi yafi magani .

Domin haka ne Dan uwa Sheikh Mahdy Fadlullah ya yi Kokarin sanar da haske da kuma Rigakafi na Gani (Ganin badini) Inda ya tattara Abinda Allah ya hire masa Cikin Wannan Littafi da ke kasa mai suna البصيرة تقود الحياة : Insight guide life .

Littafi ne da aka Rubuta da harshen Arabi na Hausa kuma yana nan tafe . Ga masu Bukatar Littafin Musamman Wadanda ke Iraki zasu iya Tuntubar mu haka nan masu Bukatar Soft Copy (Pdf) ma .

Muhammad S Tomo ✍🏽

Wacece Wannan Baiwar Allahr ?Ita ce Sayyida Fatima wacce ake kiran ta kuma da Ummu Abdullah (a.s) Jikar Imam Ali ,Yar Im...
22/05/2026

Wacece Wannan Baiwar Allahr ?

Ita ce Sayyida Fatima wacce ake kiran ta kuma da Ummu Abdullah (a.s)

Jikar Imam Ali ,Yar Imam Hasan ,Matar Imam Zainul Abidin ,Mahifiyar Imam Bakir (a.s) .

Imam Bakir (a.s) na cewa akan ta :wata rana ta kasance zaune jikin katanga sai ya tsage da nufin zai fadi , mun ji wannan karar sosai ,sai tayi nuni da hannun tace , A'a ina gama ka da darajar Musdafa ban maka izinin ka fadi ba , sai garun ya tsaya cak a sama har sai da ta masa Izini (bayan ta kauce).

Jikan ta Imam Sadik (a.s) na cewa Mahaifiyar sa (Imam Bakir) ta kasance mai gaskiya ba'a samu kamarta ba a cikin Yayan Hasan (a.s)

Allah ya azurta mu ziyayar ta a duniya da ceton ta a Lahira

Hoton da ke kasa zaku gan mu yayin da muka kai mata ziyara a markadin ta da yake Shari-e banat -el Hasan Najaf Ashraf ne

Muhammad S Tomo ✍🏽

Kada ka cika idanunka da kallonsu (iyaye) face da rahama da tausayi. Kada ka ɗaga muryarka sama da muryoyinsu, kada kuma...
22/05/2026

Kada ka cika idanunka da kallonsu (iyaye) face da rahama da tausayi. Kada ka ɗaga muryarka sama da muryoyinsu, kada kuma ka ɗaga hannuwanka sama da nasu, kuma kada ka taba shiga gabansu ( a ra’ayoyi da yanke hukunci).

Inji Imam Sadik
Bihar J 71 Shafi 79

وَقَضَىٰ رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا ۚ إِمَّا يَبْلُغَنَّ عِندَكَ الْكِبَرَ أَحَدُهُمَا أَوْ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُل لَّهُمَا أُفٍّ وَلَا تَنْهَرْهُمَا وَقُل لَّهُمَا قَوْلًا كَرِيمًا ۝ وَاخْفِضْ لَهُمَا جَنَاحَ الذُّلِّ مِنَ الرَّحْمَةِ وَقُل رَّبِّ ارْحَمْهُمَا كَمَا رَبَّيَانِي صَغِيرًا

Barkan mu da Safiyar Juma’a 🕋🌹

Muhammad S Tomo ✍🏽

Muhammad ðin ku 😇
21/05/2026

Muhammad ðin ku 😇

21/05/2026

Yakini da Imani

KWANA - 30 RANA TA - 7

Ku ji tsoron saɓon Allah a wuraren da kuke keɓe (boye)ku kaɗai; domin Wanda yake gani (Allah)Shi ne kuma Mai hukunci.Inj...
21/05/2026

Ku ji tsoron saɓon Allah a wuraren da kuke keɓe (boye)ku kaɗai; domin Wanda yake gani (Allah)Shi ne kuma Mai hukunci.

Inji Amirul-Mu’uminin (a.s)
Nahjul Balagha Hadisi na 324

Muhammad S Tomo ✍🏽

Idan (wutar) fushi ya taso muku, to ku kashe shi da yafiya ,domin a ranar Alƙiyama mai kira zai yi kira cewa: Duk wanda ...
20/05/2026

Idan (wutar) fushi ya taso muku, to ku kashe shi da yafiya ,domin a ranar Alƙiyama mai kira zai yi kira cewa: Duk wanda yake da lada a wurin Allah, to ya tashi.Wadanda s**a kasance masu yafiya ne kaɗai za su tashi. Shin ba ku ji faɗin Allah Maɗaukaki ba:
فَمَنْ عَفا وَ أَصْلَحَ فَأَجْرُهُ عَلَى اللَّهِ
(Duk wanda ya yafe kuma ya gyara, to ladansa yana wurin Allah).

Inji Manzon Allah (S)
Bihar J 74 Shafi na 182

Muhammad S Tomo ✍🏽

19/05/2026

A Wani Yanayi ake Taimakon Imam (a.s)

KWANA - 30. RANA TA - 6

Ku riƙa fada wa mutane magana mafi  kyawo irin wadda kuke so a fada muku; domin Allah yana ƙin mai yawan tsinuwa, mai za...
19/05/2026

Ku riƙa fada wa mutane magana mafi kyawo irin wadda kuke so a fada muku; domin Allah yana ƙin mai yawan tsinuwa, mai zagi, mai cin mutuncin Muminai, mai maganganun batsa da rashin kunya, da kuma mai roƙo cikin nacewa da takura.

Inji Baban Ja’afar Muhammad Bakir (a.s)
Bihar J 65 Shafi na 153

Daga kasa Hoton za’imul Hauza Ayatullah Shaikh Husain Wahid -Al khurasani (Allah ya Kara masa Lafiya )mai Shekaru 104 ne 👇🏽

Muhammad S Tomo ✍🏽

18/05/2026

MAHDI MAI DOGON - 4

Muhammad S Tomo

Address

No 1
Najaf
3131451

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muhammad S Tomo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share