Kamfanin Dillancin Labaran Hauza

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza Wannan shafin mallakar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ne, kuma an ƙirƙire shi ne domin yaɗa labarai

Zuwa ga Al’umma Mai Manufa:Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (27) | Raj’ar Annabawa, Imamai da Muminai Hauza/ Annabawa,...
27/08/2026

Zuwa ga Al’umma Mai Manufa:

Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (27) | Raj’ar Annabawa, Imamai da Muminai

Hauza/ Annabawa, Imamai ma’asumai (AS) da kuma muminai masu tsarki — bisa ga riwayoyi— za su dawo duniya a lokacin raj’a.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, ana gabatar da jerin tattaunawa kan Mahdawiyya mai taken “Zuwa ga Al’umma Mai Manufa”, da nufin yada koyarwa da ma’arifa da s**a shafi Imamuz Zaman (AJ) ga ku masu daraja.

Bisa ga ruwayoyi, Annabawa, Imamai ma’asumai (AS) da muminai suna daga cikin waɗanda za su dawo wannan duniya a lokacin raj’a.

Ana iya rarraba waɗannan ruwayoyi zuwa rukuni huɗu:

A) Ruwayoyin da s**a yi magana gaba ɗaya game da dawowar Annabawa da Imamai (AS):

Imam Ja'afar Sadiƙ (AS) a cikin tafsirin ayar nan:

«إِنَّا لَنَنصُرُ رُسُلَنَا وَالَّذِینَ آمَنُوا فِی الْحَیاةِ الدُّنْیا وَیَوْمَ یَقُومُ الْأَشْهَادُ؛

"Lalle ne za Mu taimaki manzanninMu da waɗanda s**a yi imani a rayuwar duniya da kuma ranar da masu shaida za su tashi.» (Suratul Ghafir: 51)

ya ce:

«ذلک والله فی الرجعة، أما علمت أن أنبیاء کثیرة لم ینصروا فی الدنیا وقتلوا والائمة بعدهم قتلوا ولم ینصروا، ذلک فی الرجعة.»

"Na rantse da Allah cewa wannan ayar za ta tabbata ne a lokacin raj’a. Shin ba ku sani ba cewa Annabawa da yawa ba a taimaka musu a duniya ba kuma an kashe su, haka ma Imamai bayan su an kashe su kuma ba a taimaka musu ba? Wannan taimako da nasara za su tabbata ne a lokacin raj’a." (Mu‘ujamu Ahadith al‑Imam al‑Mahdi, j. 5, sh. 384)

B) Ruwayoyin da s**a ambaci 'adadi' game da raj’ar Annabawa:

Imam Ja’afar Sadiƙ (AS) ya ce:

«ویقبل الحسین فی أصحابه الذین قتلوا معه ومعه، سبعون نبیا، کما بعثوا مع موسی بن عمران.»

"Lokacin da Imam Hussain (AS) zai dawo tare da sahabbansa waɗanda aka kashe tare da shi, Annabawa saba’inbma za su dawo tare da shi, kamar yadda aka aiko saba’in tare da Musa ɗan Imran (AS)." (Mu‘ujamu Ahadith al‑Imam al‑Mahdi, j. 4, sh. 89)

C) Ruwayoyin da s**a ambaci raj’ar wasu Annabawa da Imamai da sunayensu:

Imam Muhammad Baƙir (AS) ya ce:

«وَ إِنَّ دَانِیَالَ وَ یُوشَعَ یَخْرُجَانِ إِلَی أَمِیرِ اَلْمُؤْمِنِینَ یَقُولاَنِ صَدَقَ اَللَّهُ وَ رَسُولُهُ.»

"Hakika Daniyal da Yusha’u (AS) za su dawo duniya a lokacin raj’ar Amirul Muminin (Ali (AS), kuma za su ce: "Allah da Manzonsa sun yi gaskiya." (Bihar al‑Anwar, j. 53, sh. 62)

Haka kuma Imam Zainul Abidin (AS) ya ce:

«یرجع إلیکم نبیکم صلی الله علیه وآله وأمیرالمؤمنین علیه‌السلام والائمة علیهم‌السلام.»

"Annabinku (SAWA) da Amirul Muminin (Ali (AS) da Imamai (AS) za su sake dawowa gare ku." (Mu‘ujamu Ahadith al‑Imam al‑Mahdi, j. 5, sh. 327)

Haka kuma Imam Ja’afar Sadiƙ (AS) ya ce:

«أَوَّلُ مَنْ یَرْجِعُ إِلَی اَلدُّنْیَا اَلْحُسَیْنُ بْنُ عَلِیٍّ عَلَیْهِ السَّلاَمُ.»

"Na farkon wanda zai dawo duniya shi ne Hussain ɗan Ali (AS)." (Bihar al‑Anwar, j. 53, sh. 46)

D) Ruwayoyin da s**a ba da labarin raj’ar mutanen kirki daga al’ummomin da s**a gabata da kuma al’ummar Musulunci:

Imam Ja’afar Sadiƙ (AS) ya ce:

«یَخْرُجُ اَلْقَائِمُ مِنْ ظَهْرِ اَلْکَعْبَةِ مَعَ سَبْعَةٍ وَ عِشْرِینَ رَجُلاً خَمْسَةَ عَشَرَ مِنْ قَوْمِ مُوسَی عَلَیْهِ السَّلاَمُ اَلَّذِینَ کَانُوا یَهْدُونَ بِالْحَقِّ وَ بِهِ یَعْدِلُونَ وَ سَبْعَةٌ مِنْ أَهْلِ اَلْکَهْفِ وَ یُوشَعُ بْنُ نُونٍ وَ سَلْمَانُ وَ أَبُو دُجَانَةَ اَلْأَنْصَارِیُّ وَ اَلْمِقْدَادُ وَ مَالِکٌ اَلْأَشْتَرُ فَیَکُونُونَ بَیْنَ یَدَیْهِ أَنْصَاراً أَوْ حُکَّاماً.»

"Qa’im (Imam Mahdi AS) zai bayyana daga bayan Ka’aba tare da mutum ashirin da bakwai, goma sha biyar daga mutanen Musa (AS) waɗanda s**a kasance suna shiryarwa da gaskiya kuma suna yin adalci da ita, da kuma mutum bakwai daga Ashabul Kahf, Yusha’u ɗan Nun, Salman, Abu Dujana al‑Ansari, Miƙdad da kuma Malikul Ashtar; kuma za su kasance a gabansa a matsayin mataimaka ko shugabannin rundunarsa." (Rawdat al‑Wa’izin, j. 2, sh. 266)

Wannan tattaunawa za ta ci gaba...

An ɗauko daga littafin "Negine Afarinesh”, tare da ɗan gyara kaɗan.

https://ha.hawzahnews.com/xfLbs

https://chat.whatsapp.com/LN2jhDhG9a1B2AtmnHlNyV

https://t.me/KamfaninDillancinLabaranHauza

https://www.facebook.com/share/1EETPjNEPk/

Me Ya Sa Allah Ya Halicci Jahilci?Hauza/ Ɗan Adam halitta ce mai hankali, sha’awa da ikon zaɓi; wannan baiwa ce da ta sa...
27/08/2026

Me Ya Sa Allah Ya Halicci Jahilci?

Hauza/ Ɗan Adam halitta ce mai hankali, sha’awa da ikon zaɓi; wannan baiwa ce da ta sanya shi tsakanin faɗuwa da ɗaukaka. Jahilci shi ne rashin kula da hankali da ilimi, kuma wannan damar ta zaɓi ce ke samar da yanayin da mutum zai samu ci gaba har ya kai wani matsayi da ya fi na mala’iku.

https://ha.hawzahnews.com/xg59q

https://chat.whatsapp.com/LN2jhDhG9a1B2AtmnHlNyV

https://t.me/KamfaninDillancinLabaranHauza

https://www.facebook.com/share/1EETPjNEPk/

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a mahangar tauhidi, Allah bai halicci jahilci ba, sai dai Ya halicci hankali da ilimi. Jahilci yana samun ma’ana ne a lokacin da mutum ya yi watsi da hankalinsa da kuma damar da yake da ita ta ilimi. Haka kuma mutum, saboda yana da hankali da sha’awa, halitta ce mai ikon zaɓi; kuma wannan zaɓi shi ne sirrin ci gabansa ko faɗuwarsa.

Allah bai halicci jahilci ba, a’a, abin da Ya halitta shi ne ilimi da hankali. Jahilci yana samun ma’ana ne a inda ba a kula da hankali da ilimi ba. Mutum kuma, saboda yana da hankali da sha’awa, yana da ikon zaɓi, kuma wannan ikon ne yake ba shi damar samun ci gaba ko faɗuwa, tare da ba shi wata dama da za ta iya kai shi zuwa matsayi da ya fi na mala’iku.

Allah bai halicci jahilci ba, sai dai Ya halicci ilimi da hankali. A inda hankali ba ya nan, a nan ne muke magana game da “jahilci”. Saboda haka, Allah Ya halicci abin da yake akwai, ba abin da babu shi ba. Misali, idan babu wata bishiya a gabammu, ba za a iya tambayar wa ya dasa wannan bishiyar ba. Amma game da abin da yake akwai, kamar tebur, ana iya tambayar wa ya ƙera shi. Haka nan hankali yana nan, kuma Allah ne Ya halicce shi.

Allah Ya halicci hankali ne domin bayinsa su samu ci gaba, su kai ga kamala, su kuma kusanci Allah. Amma bai halicci jahilci ba. Mutanen da suke yin watsi da hankali kuma suke taka shi, a zahiri suna shiga matsayin rashin hankali, kuma wannan yanayi ake kira jahilci.

A cikin halittar ɗan Adam akwai hankali, wanda ake kira “hankalin halitta” (aql bil-fitra), amma wannan hankali shi kaɗai bai isa ya kai mutum ga manufarsa ba. Hankalin halitta dole ne ya koma hankalin mallaka (aql bil-malaka), sannan ya koma hankali mai aiki (aql bil-fi’l), daga bisani kuma ya kai ga hankalin da aka samu (aql al-mustafad). Wannan tsari ne ke haifar da ci gaban mutum, har ya iya kai shi wani matsayi da ya fi na mala’iku.

Da a ce an halicci hankalin mutum cikakke tun daga farko, da mutum bai bambanta da mala’ika ba, kuma a wannan yanayin da bai yi wani ƙoƙari na musamman ba. A cikin riwaya an bayyana cewa an halicci dabbobi daga sha’awa zalla, mala’iku daga hankali zalla, yayin da aka halicci mutum daga haɗin hankali da sha’awa.

Idan hankalin mutum ya rinjayi sha’awarsa, mutum zai iya wuce mala’iku; domin mala’ika ba shi da sha’awa kuma yana bin hankalinsa ne. Amma mutum, duk da yana da sha’awa, idan ya bi hankalinsa, wannan ne zai sa ya samu ci gaba. A akasin haka, idan mutum ya bi sha’awarsa, zai iya zama ƙasa da dabba; domin ana ɗauka cewa dabba ba ta da hankali kuma tana bin sha’awa, yayin da mutum yake da hankali amma ya zaɓi bin sha’awarsa.

Saboda haka, hankali dole ne ya kasance yana da damar haɓaka, haka nan ilimi ma ya kasance yana iya ƙaruwa. Domin da a ce hankali da ilimi ba sa iya haɓaka, da mutum zai tsaya a matsayinsa na farko, kuma da ba zai samu damar ci gaba ba.

Zaɓi; Muhimmin Sharadin Mutum da Samun Ci gaba

Wani muhimmin batu shi ne jahilcin da yake kasancewa a cikin mutum. Abin da ake nufi da jahilci ba wai zunubi kawai ba ne; domin kowane zunubi ma ana aikata shi ne ta wani nau’i na jahilci da halin jahilci. Wannan jahilci yana da alaƙa da ikon zaɓin mutum. Da a ce ba a ba mutum wannan damar ba, da an cire masa ikon zaɓi.

Idan mutum ba shi da ikon zaɓi, to ba zai ƙara zama mutum ba; ko dai ya zama mala’ika, ko dutse, ko wani abu makamancin haka. Ci gaban mutum da ainihin mutuntakarsa yana cikin samun damar zaɓi; wato ya kasance yana iya aikata zunubi kuma yana iya ƙin aikata shi. Idan wannan damar ba ta wanzu ba, to ci gaba, zaɓi da mutuntaka ba za su ƙara samun ma’ana ba.

Allah Ya bayyana wannan damar da mutum yake da ita ta ɗaukar amanarSa a cikin ayar:

«إِنَّا عَرَضْنَا الْأَمَانَةَ عَلَی السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَالْجِبَالِ فَأَبَیْنَ أَنْ یَحْمِلْنَهَا وَأَشْفَقْنَ مِنْهَا وَحَمَلَهَا الْإِنْسَانُ إِنَّهُ کَانَ ظَلُومًا جَهُولًا»

Lokacin da aka kwatanta damar mutum ta ɗaukar wannan amana da damar sammai, ƙasa da duwatsu, sai aka bayyana cewa sammai ba su iya ɗaukarta ba, ƙasa ba ta da damar ɗaukarta, haka nan duwatsu ba su da ƙarfin ɗaukarta. Amma mutum yana da damar ɗaukar wannan amana.

Duk da haka, wannan mutum ɗin shi ne wanda zai iya zama “zalim” da “jahil”. Mutumin da zai iya yin zalunci kuma ya iya zama jahili, a lokaci guda yana iya kaiwa matsayin ɗaukar wata amana da babu wani mahaluki da ya iya ɗaukarta, yayin da sammai, ƙasa da duwatsu ba su iya ɗaukarta ba.

Furucin “zalim da jahil” ma yana da muhimmanci idan aka duba shi ta mahangar “rashin abu da damar samuwarsa” (adama wa malaka). Idan babu ilimi, jahilci ba ya da ma’ana; haka kuma idan babu adalci, zalunci ba ya samun ma’ana. Misali, ba za mu taɓa cewa dutse makaho ba, domin dutse ba shi da irin matsayin da ake sa ran yana da ido. Amma idan muka ce mutum makaho ne, hakan ya samo asali ne saboda mutum yana da matsayin da ya kamata ya kasance mai gani.

Haka nan idan muka ce wani mutum jahili ne, hakan yana faruwa ne saboda matsayinsa da ƙarfinsa shi ne ya kasance mai hankali da ilimi. Wanda ba shi da wannan matsayi da wannan dama, ba za a iya cewa shi “zalim” ko “jahil” ba.

Daga wannan batu ma za a iya fahimtar girman mutum, damar da yake da ita da kuma ainihin kasancewarsa na ɗan Adam. Mutum halitta ce mai ikon zaɓi; yana iya zama azzalumi, jahili kuma mai zunubi, amma a lokaci guda yana iya zama adali, masani, mai taƙawa kuma mai ibada.

Da a ce babu ikon zaɓin da aka ba mutum wanda ta hanyarsa zai iya yin zalunci, jahilci da zunubi, da adalci, ilimi, taƙawa da ibada su ma ba za su samu ma’ana ba. A wannan yanayin, mutum ma ba zai ƙara zama mutum ba.

Hauza/ Ɗan Adam halitta ce mai hankali, sha’awa da ikon zaɓi; wannan baiwa ce da ta sanya shi tsakanin faɗuwa da ɗaukaka. Jahilci shi ne rashin kula da hankali da ilimi, kuma wannan damar ta zaɓi ce ke samar da yanayin da mutum zai samu ci gaba har ya kai wani matsayi da ya fi na mala’iku.

An Gano Tare da Tattara Taken Bincike 60,000 Kan Annabi Muhammad (SAWA), Za a Kaddamar da Kundin Juzu’i 12 a Taron Haɗin...
26/08/2026

An Gano Tare da Tattara Taken Bincike 60,000 Kan Annabi Muhammad (SAWA), Za a Kaddamar da Kundin Juzu’i 12 a Taron Haɗin Kan Musulmi

Hauza/ A wani taron manema labarai da aka gudanar domin gabatar da “Kundin Batutuwan Bincike na Ilimomi da Ma’arifar Annabi Muhammad (SAWA)”, an bayyana cewa bayan kimanin shekaru 10 na bincike, tantancewa da tace bayanai, an gano tare da tsara batutuwa da maƙalolin bincike 60,000 da s**a shafi halayya, rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad (SAWA), waɗanda aka rarraba su zuwa fannoni 28 na ilimi.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an shirya wannan aiki cikin juzu’i 12, kuma ana shirin kaddamar da shi a birnin Qum yayin Taron Haɗin Kan Musulmi karo na 40.

Jami’an Makarantun Ilimin Addinin Musulunci (Hauza) sun jaddada cewa bincike kan Annabi Muhammad (SAWA) bai kamata ya takaita ga karatun littattafai kawai ba, a maimakon haka ya kamata ya dace da buƙatu da tambayoyin ɗan Adam a wannan zamani, musamman a fannoni kamar ɗabi’a (akhlaƙ), iyali, adalci, hankali, ilimin ɗan Adam da wayewar kai.

Bisa bayanan da aka gabatar, a matakin farko an tattara kusan batutuwa 70,000 na bincike, sannan bayan an gudanar da bincike, aka cire batutuwa masu maimaituwa tare da rarraba su bisa fannoni daban-daban na ilimi, sai aka samu batutuwa 60,000 da s**a zama na ƙarshe a cikin wannan kundi.

Mai gudanar da wannan shiri ya kuma bayyana cewa kundin yana da tsari na wayewar kai da na ƙasa da ƙasa, inda ya ce batutuwan da aka tattara za su iya zama wata hanya ta bunƙasa binciken ilimi kan Annabi Muhammad (SAWA) a ƙasashen Musulmi daban-daban, tare da ƙarfafa haɗin kan masana a duniyar Musulmi.

Daga cikin batutuwan da aka tanada akwai nazarin dangantakar fahimtar ɗan Adam ta tsarin zamani na duniya da kuma fahimtar ɗan Adam da ɗabi’u bisa koyarwar Annabi (SAWA), da kuma nazarin tasirin ma’arifar Annabi Muhammad kan ginshiƙan iyali a zamanin Daular Usmaniyya da kuma al’ummar Turkiyya ta yau.

Jami’an makarantun Hauza sun bayyana fatan cewa wannan aiki zai taimaka wajen faɗaɗa binciken ilimi da aikace-aikace kan Annabi Muhammad (SAWA), samar da sabbin ra’ayoyin ilimi, da kuma gabatar da fa’idodin koyarwar Annabi ga al’ummar duniya.

https://ha.hawzahnews.com/xg59g

https://chat.whatsapp.com/LN2jhDhG9a1B2AtmnHlNyV

https://t.me/KamfaninDillancinLabaranHauza

https://www.facebook.com/share/1EETPjNEPk/

Ayatullah A’arafi:Al’ummar Likitoci Taska ce Mai Daraja ta Ilimi, Ƙwarewa da Ɗabi’ar AikiHauza/ Shugaban Makarantun Ilim...
26/08/2026

Ayatullah A’arafi:

Al’ummar Likitoci Taska ce Mai Daraja ta Ilimi, Ƙwarewa da Ɗabi’ar Aiki

Hauza/ Shugaban Makarantun Ilimin Addinin Musulunci (Hauza) na ƙasar Iran, Ayatullah Alireza A’arafi, ya bayyana cewa ƙwararrun likitoci da ma’aikatan kiwon lafiya taska ce mai matuƙar daraja ta ilimi, ƙwarewa da ɗabi’ar aiki, waɗanda ke da alhakin kare rayuwa da lafiyar ɗan Adam.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah Alireza A’arafi, Shugaban Makarantun Ilimin Addinin Musulunci (Hauza), ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya fitar domin girmama ƙoƙarin likitoci, inda ya ce:

بسم الله الرحمن الرحیم

«وَمَنْ أَحْیَاهَا فَکَأَنَّمَا أَحْیَا النَّاسَ جَمِیعًا»

“Duk wanda ya ceci ran mutum, kamar ya ceci rayuwar dukkan mutane ne.” (Suratul Ma’ida, aya ta 32)

Al’ummar ƙwararrun likitoci da ma’aikatan kiwon lafiya taska ce mai matuƙar daraja ta ilimi, ƙwarewa da ɗabi’ar aiki, waɗanda suke gudanar da aikinsu wajen kare mafi darajar baiwar Allah, wato rayuwa da lafiyar ɗan Adam.

A mahangar tauhidi, aikin likita ba wai kawai tarin ilimomi da dabarun gano cututtuka da magance su ba ne; a’a, ilimi ne na ɗan Adam kuma nauyi ne na ɗabi’a, inda bincike da ƙwarewa suke haɗuwa da mutunta ɗan Adam, tausayawa masu fama da wahala da kuma riƙon amanar rayuwar ɗan Adam. Likita, tare da amfani da sabbin nasarorin kimiyya da fasahohin zamani, ya kamata a kodayaushe ya kiyaye mutuncin ɗan Adam, bege na mara lafiya da kuma amincewar al’umma.

Imam Ali (AS) ya ce:

«العِلمُ سُلطانٌ؛ مَن وَجَدَهُ صالَ بِهِ، ومَن لَم یَجِدْهُ صیلَ عَلَیهِ»

“Ilimi iko ne; wanda ya same shi yana samun ƙarfi da shi, wanda kuma ya rasa shi, za a rinjaye shi.”

Saboda haka, ɗaukaka fannin likitanci na ƙasar na buƙatar ci gaba da samar da ilimi, bunƙasa bincike na asali da na aikace-aikace, ƙarfafa koyarwa, yin amfani da fasahohin zamani cikin hikima, tare da kiyaye ɗabi’a da adalci a fannin kiwon lafiya.

Ranar Likitoci dama ce ta girmama ƙoƙarin ilimi da sadaukarwar likitocin da ke aiki a asibitoci, cibiyoyin kiwon lafiya, jami’o’i da fannonin bincike da koyarwa, waɗanda ke yi wa al’umma hidima cikin ɗaukar nauyi da sadaukarwa.

Tare da girmama ƙwaƙwalwar shahidan fannin kiwon lafiya da nuna girmamawa ga dukkan masu hidima a fannin magani, ina taya al’ummar likitoci, malamai, masu bincike, likitocin da ke da ƙwarewa da ɗaliban likitanci, musamman likitoci masu jajircewa da aiki tuƙuru na lardin Qum da Jami’ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Qum, murnar wannan rana.

Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba dukkan likitoci da masu aiki a fannin kiwon lafiya ƙarin nasara a tafarkin ilimi da hidima, ɗaukaka da mutunci, lafiya da walwala; sannan Ya ba marasa lafiya da masu fama da wahala waraka cikin gaggawa da cikakkiya.

Alireza A’arafi

Shugaban Makarantun Ilimin Addinin Musulunci (Hauza) na ƙasar Iran

https://ha.hawzahnews.com/xg59k

https://chat.whatsapp.com/LN2jhDhG9a1B2AtmnHlNyV

https://t.me/KamfaninDillancinLabaranHauza

https://www.facebook.com/share/1EETPjNEPk/

Miliyoyin Mutane Sun Halarci Zagayen 12 ga Rabi’ul Awwal a Garuruwa Daban-daban na NajeriyaHauza/ A daidai lokacin da ak...
26/08/2026

Miliyoyin Mutane Sun Halarci Zagayen 12 ga Rabi’ul Awwal a Garuruwa Daban-daban na Najeriya

Hauza/ A daidai lokacin da aka shiga ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal, ranar zagayowar haihuwar Manzon Allah (S.A.W.A) bisa shahararriyar riwayar Ahlus-Sunna, an gudanar da zagayen murnar Mauludin Annabi (S.A.W.A) a garuruwa daban-daban na Najeriya, tare da halartar miliyoyin mutane.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a ranar Talata, 25 ga watan Agusta 2026, wanda ya yi daidai da 12 ga Rabi’ul Awwal 1448 bayan Hijira, an gudanar da zagayen murnar Mauludin Manzon Allah (S.A.W.A) a wurare daban-daban na ƙasar Najeriya.

Wannan biki da ake gudanarwa duk shekara a garuruwa daban-daban na Najeriya, ya samu halartar dimbin al’umma daga sassa daban-daban, ciki har da maza da mata, yara da matasa, da kuma tsofaffi. Mahalarta sun fito sanye da sababbin fararen kaya, tare da sanya turare, yayin da suke tafiya cikin jerin gwanon cikin tsari.

Daga cikin masoya Manzon Allah (S.A.W.A) da s**a halarci wannan zagaye akwai mabiyan Harkar Musulunci ta Najeriya ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H). Mabiyan Harkar sun halarci taron cikin tsari da haɗin kai, ɗauke da tutoci da hotunan wasu daga cikin jagororin gwagwarmaya, ciki har da Imam Khumaini (Q), Shahidin Jagora (Q), Shahid Sayyid Hassan Nasrullah, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene’i, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) da sauran fitattun jagororin gwagwarmaya.

A yayin zagayen, mahalarta sun ci gaba da bayyana ƙauna da girmamawa ga Manzon Allah (S.A.W.A) da iyalansa tsarkaka, inda s**a rera waƙoƙi da yabon Manzon Allah (S.A.W.A) da Ahlul Baiti (A.S).

Haka kuma, a yayin gudanar da wannan biki, an raba alawoyi, biskit da dafaffen abinci ga jama’a da masu kallo, lamarin da ya ƙara sanya yanayin garuruwan ya kasance cikin farin ciki da murnar zagayowar haihuwar Manzon Allah (S.A.W.A).

Ya kamata a lura cewa wannan shi ne zagayen farko na bukukuwan Mauludin Manzon Allah (S.A.W.A) da aka gudanar a Najeriya, yayin da ake sa ran sake gudanar da wani zagaye a ranar 17 ga watan Rabi’ul Awwal a sassa daban-daban na ƙasar.

https://ha.hawzahnews.com/xg54J

https://chat.whatsapp.com/LN2jhDhG9a1B2AtmnHlNyV

https://t.me/KamfaninDillancinLabaranHauza

https://www.facebook.com/share/1EETPjNEPk/

Harkar Musulunci Ta Fara Taron Makon Haɗin Kan Al'ummar Musulmi a AbujaAbuja – Hauza: Harkar Musulunci a Najeriya ƙarƙas...
26/08/2026

Harkar Musulunci Ta Fara Taron Makon Haɗin Kan Al'ummar Musulmi a Abuja

Abuja – Hauza: Harkar Musulunci a Najeriya ƙarƙashin jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ta fara gudanar da Taron Makon Haɗin Kan Al'ummar Musulmi a Abuja, da nufin ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al'ummar Musulmi daga mazhabobi daban-daban.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an fara taron ne a ranar Talata, 12 ga Rabi'ul Awwal 1448H, wanda ya yi daidai da 25 ga Agusta 2026, a Abuja. Ana gudanar da taron na tsawon kwanaki biyar a cikin watan Rabi'ul Awwal na kowace shekara, inda malamai da sauran al'ummar Musulmi ke taruwa domin tattauna rayuwar Manzon Allah (SAWW), koyarwarsa da darussan da za a iya amfani da su wajen ƙarfafa haɗin kan al'ummar Musulmi.

An buɗe taron da addu'ar buɗewa daga Sheikh Rabi'u Funtuwa. Daga bisani, Abban Sayyida ya gabatar da karatun Alƙur'ani Mai Girma tare da karanta ziyarar Manzon Allah (SAWW) domin neman tabarruki. Haka kuma, tawagar Ittihadu Shu'ara ta gabatar da waƙoƙin yabon Manzon Allah (SAWW).

Babban baƙon mai jawabi a taron, Sheikh Shareef Ahmad Suleja, ya gabatar da muƙala mai taken: “Nazarin Rayuwar Annabi Muhammad (SAWW) a Makka: Hulɗar Musulmi da Waɗanda Ba Musulmi Ba — Darussa ga Al'ummar Najeriya.”

A cikin jawabinsa, Sheikh Shareef Ahmad Suleja ya yi bayani kan matsayin ɗan Adam da kuma muhimmancin sanin darajar Manzon Allah (SAWW), yana mai bayyana rayuwar Annabi a matsayin babban darasi ga dukkan al'umma.

Ya ce Manzon Allah (SAWW) shi ne hasken da ke bayyana gaskiya, sannan ya jaddada cewa tun kafin aiko shi da saƙon Allah, mutanen Makka sun riga sun amince da gaskiyarsa, amana da adalcinsa, har s**a laƙaba masa suna Al-Amin saboda kyawawan ɗabi'unsa.

Da yake magana kan mu'amalar Manzon Allah (SAWW) da waɗanda ba Musulmi ba, Sheikh Shareef ya bayyana cewa rayuwarsa tana ƙunshe da muhimman darussa kan yadda za a gudanar da hulɗa cikin adalci, mutunci da kyawawan ɗabi'u.

Ya kuma bayyana cewa irin ƙauna da kulawar da Annabi (SAWW) yake nunawa sahabbansa ta sa kowannensu yake jin cewa shi ne mafi kusanci da Manzon Allah.

A wani ɓangare na jawabinsa, Sheikh Shareef Ahmad Suleja ya yabawa Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) bisa ci gaba da wannan da'awa, yana mai cewa mafitar Najeriya ita ce komawa ga tarbiyyar Manzon Allah Muhammad (SAWW) da Ahlul Baiti (AS), tare da tsayawa kan gaskiya da adalci wajen tunkarar zalunci.

Ya kuma bayyana juriyar da Sayyid Zakzaky ya nuna a cikin wahalhalu da tsanantawar da ya fuskanta a matsayin babban darasi ga al'umma, yana mai kira ga Musulmi da su yi koyi da haƙuri da jajircewarsa wajen bin tafarkin Allah.

A ƙarshe, babban mai jawabin ya yi kira ga mahalarta taron da su ƙara himma wajen nazarin rayuwar fiyayyen halitta, Manzon Allah (SAWW), tare da ƙoƙarin aiwatar da darussan rayuwarsa a cikin al'umma.

Bayan kammala jawabin, Sheikh Rabi'u Funtuwa ya gabatar da ta'aliki, inda ya ƙara haskaka muhimman darussa da abubuwan da s**a fito daga jawabin Sheikh Shareef Ahmad Suleja.

Daga bisani, Dr. Aminu Yabo ya rufe taron da addu'a.

Wannan taro dai zai ci gaba har tsawon kwanaki biyar inda malamai daban-daban daga fahimtoci daban-daban za su gabatar da jawabai.

https://ha.hawzahnews.com/xg59c

https://chat.whatsapp.com/LN2jhDhG9a1B2AtmnHlNyV

https://t.me/KamfaninDillancinLabaranHauza

https://www.facebook.com/share/1EETPjNEPk/

Sharhin Hadisin Akhlaƙ; Tasirin Tunawa da MutuwaHauza/ Shahid Imam Ayatullah Khamene'i ya bayyana ma’anar hadisin «أَکثِ...
26/08/2026

Sharhin Hadisin Akhlaƙ; Tasirin Tunawa da Mutuwa

Hauza/ Shahid Imam Ayatullah Khamene'i ya bayyana ma’anar hadisin «أَکثِرْ ذِکْرَ الْمَوْتِ» (Ka yawaita tuna mutuwa), inda ya jaddada cewa mallakar dukiya, ’ya’ya da sauran abubuwan kawata rayuwar duniya ba abin zargi ba ne. Abin da ke cutar da mutum shi ne tsananin son waɗannan abubuwa da rashin iya kame wannan so, har ya hana shi sadaukarwa, bayar da sadaka da kuma sauke nauyin da ke kansa.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Shahid Imam Ayatullah Khamene'i (Allah Ya tsarkake ruhinsa) ya kasance yana yin sharhin hadisan Akhlaƙ a farkon zaman karatun bahasin fikihu na manyan malamai (Bahsul Kharij).

Taken wannan darasin shi ne “Tasirin yawaita tuna mutuwa”, inda ya yi sharhin wani hadisi daga Imam Muhammad Baƙir (AS):

بسم‌الله‌الرّحمن‌الرّحیم

الحمدلله ربّ العالمین

«أَکثِر ذِکرَ الموت»

“Ka yawaita tuna mutuwa; ka riƙa yawan tunanin mutuwa.”

Sannan hadisin ya ci gaba da cewa:

«فَإِنَّهُ لَم یُکثِر ذِکرَهُ إِنسانٌ إِلَّا زَهِدَ فِی الدُّنیا»

“Domin babu wani mutum da yake yawaita tuna mutuwa face ya zama mai rage sha’awar duniya.”

Shahid Imam Ayatullah Khamene'i ya bayyana cewa manyan matsalolin mutane suna faruwa ne saboda tsananin sha’awar duniya. Dukiyoyi, dukiya mai yawa, kayan more rayuwa, kyau, iko, ƙarfi, matsayi da makamantansu duk abubuwan duniya ne, kuma tsananin sha’awarsu ne ke sa mutum ya yi tuntuɓe.

Ya jaddada cewa ba wai waɗannan abubuwan na duniya kansu ne marasa kyau ba. Allah Maɗaukaki Ya ce:

«أَلْمَالُ وَالْبَنُونَ زِینَةُ الْحَیَاةِ الدُّنْیَا»

“Dukiya da ’ya’ya kayan ado ne na rayuwar duniya.”

Saboda haka, ba a zargi mutum saboda yana da dukiya, ’ya’ya ko iyali ba. Abin da ke cutar da mutum shi ne tsananin son waɗannan abubuwa, wanda kan kai shi ga zaɓar hanya mara kyau a lokacin da ya kamata ya yi sadaukarwa ko ya bayar da abin da yake da shi wajen taimakon wasu.

Ya ce babban matsalar mutane masu rauni a rayuwar duniya ita ce yawan son duniya, ƙaunarta da kuma ruɗuwa da ita. Tambayar ita ce: Mene ne maganin wannan ruɗuwar?

Ya amsa da cewa:

“Tuna mutuwa; yawaita tuna mutuwa.”

Wato mutum ya riƙa yawan tuna mutuwa, domin hakan zai taimaka masa wajen rage jingina zuciyarsa ga abubuwan duniya da kuma fahimtar cewa dukiyar duniya da sauran abubuwan more rayuwa ba su dawwama.

https://ha.hawzahnews.com/xg59s

https://chat.whatsapp.com/LN2jhDhG9a1B2AtmnHlNyV

https://t.me/KamfaninDillancinLabaranHauza

https://www.facebook.com/share/1EETPjNEPk/

Bambancin Mahangar Kiristanci da Musulunci Game da Dangantakar Imani da HankaliHauza/ Imani a matsayin ginshiƙi shi ne ɗ...
25/08/2026

Bambancin Mahangar Kiristanci da Musulunci Game da Dangantakar Imani da Hankali

Hauza/ Imani a matsayin ginshiƙi shi ne ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin fahimtar ilimin tauhidin Kiristanci. A wasu fahimtoci, ana ɗaukar imani a matsayin wanda ya fi hankali muhimmanci, ko ma a sanya su a matsayin abubuwa biyu masu karo da juna. Wannan ra’ayi kuwa ba a karɓe shi a al’adar Musulunci ba, saboda matsayin da hankali yake da shi wajen gane tushen addini.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza | Dangantakar da ke tsakanin hankali da imani na daga cikin muhimman batutuwan da ake tattaunawa a falsafar addini da ilimin tauhidi. Wasu ra’ayoyi suna ɗaukar imani a matsayin wanda ya fi hankali, har ma suna fassara su a matsayin abubuwa biyu masu saɓani da juna. A al’adar Kiristanci, ana kiran wannan ra’ayi da “Imaniyya” (Fideism), kuma ya bayyana ta hanyoyi daban-daban.

Tambaya: Menene Imaniyya, kuma me ya sa ta yaɗu a Kiristanci amma Musulmi ba sa karɓarta?

Imaniyya ta yaɗu a cikin al’adar Kiristanci, kuma ta bayyana da siffofi daban-daban; tun daga Imaniyya mai tsanani, wadda take kallon hankali a matsayin wanda yake karo da imani, zuwa Imaniyya matsakaiciya ta Augustine, wadda take ɗaukar imani a matsayin sharadin fara fahimta.

Ana iya danganta tushen wannan tunani da tsarin ilimin tauhidin Kiristanci da wasu koyarwarsa, kamar “Trinity” (Uku-cikin-ɗaya), “Incarnation” (Allah ya ɗauki siffar mutum), da “Original Sin” (asalin zunubi), waɗanda ba su yi daidai da fahimtar hankali ba.

A gefe guda kuma, a al’adar Musulunci, hankali yana daga cikin ingantattun hanyoyin samun ilimin addini, kuma ba a karɓar imani a kan tushen addini ba tare da yin hukunci da hankali ba.

Saboda haka, bisa fahimtar Musulmi, Imaniyya a wannan ma’anar ba abin karɓa ba ce ko kaɗan.

Madogara: Cibiyar Amsa Tambayoyin Addini ta Ƙasar Iran

https://ha.hawzahnews.com/xg4Xn

https://chat.whatsapp.com/LN2jhDhG9a1B2AtmnHlNyV

https://t.me/KamfaninDillancinLabaranHauza

https://www.facebook.com/share/1EETPjNEPk/

Al-Bayhaqi, mashahurin malamin hadisi na Ahlus-Sunna a ƙarni na huɗu, ya ambaci bayanai guda biyu game da Sayyida Khadij...
25/08/2026

Al-Bayhaqi, mashahurin malamin hadisi na Ahlus-Sunna a ƙarni na huɗu, ya ambaci bayanai guda biyu game da Sayyida Khadija (S.A) waɗanda idan aka haɗa su za a iya fahimtar cewa tana da shekara 25 a lokacin da ta auri Annabi Muhammad (S.A.W.A).

Domin karanta cikakken rubutun a shiga link 🔗

https://ha.hawzahnews.com/xg4Xj

https://chat.whatsapp.com/LN2jhDhG9a1B2AtmnHlNyV

https://t.me/KamfaninDillancinLabaranHauza

https://www.facebook.com/share/1EETPjNEPk/

Hauza/ Auren Annabi Muhammad (S.A.W.A) da Sayyida Khadija (S.A) yana daga cikin auratayyar da s**a bar tarihi mai ɗorewa a Musulunci. Sai dai wasu shahararrun bayanai game da shekarun Nana Khadija (S.A) da kuma zargin cewa ta taɓa yin aure kafin aurenta da Annabi (S.A.W.A), bisa binciken majiyoyin...

Masaniyar al’adu:Mace Musulma a Yau Ita ce Mai Daidaita Ƙwarewar Zamantakewa da Kiyaye Iyakokin Ɗabi’aHauza/ Malamar Hau...
25/08/2026

Masaniyar al’adu:

Mace Musulma a Yau Ita ce Mai Daidaita Ƙwarewar Zamantakewa da Kiyaye Iyakokin Ɗabi’a

Hauza/ Malamar Hauza da jami’a ta bayyana wasu muhimman siffofin da ake buƙata ga mace Musulma a duniyar yau, inda ta jaddada cewa samun sani, sanin ainihin kai da kuma ɗaukar nauyi su ne ginshiƙan halayen mace Musulma.

https://ha.hawzahnews.com/xg4Yn

https://chat.whatsapp.com/LN2jhDhG9a1B2AtmnHlNyV

https://t.me/KamfaninDillancinLabaranHauza

https://www.facebook.com/share/1EETPjNEPk/

Nida Hikmat-Nia ta bayyana hakan ne a wata hira da wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, yayin da take magana kan siffofin mace Musulma a duniyar yau.

Ta ce: “Mace Musulma a yau ya kamata ta kasance mace mai sani, mai sanin ainihin tarihinta da asalinta, mai kunya, mai ƙwarewa da kuma mai ɗaukar nauyi.”

Ta ci gaba da cewa abin koyi shi ne mace wadda ta san kanta, ta gano baiwar da Allah Ya ba ta, sannan ta tsara yadda za ta bunƙasa waɗannan ƙwarewa.

Ta ce mace Musulma ya kamata ta san yadda kafafen yaɗa labarai suke aiki, amma kada ta zama baiwar kafafen yaɗa labarai. Ta kasance cikin al’umma, amma kada ta nemi a gan ta ko a san ta ta kowace hanya. Ta kasance mai son tattaunawa, amma a lokaci guda ta kiyaye iyakokinta na ɗabi’a da akida.

A cewarta, mace tana da nauyi ga iyalinta, amma hakan bai kamata ya sa ta zama ba ruwanta da makomar al’umma ba.

Matsayin kunya da hijabi a asalin mace Musulma

Malamar Hauza da jami’ar ta yi nuni da muhimmancin kunya da hijabi a cikin tsarin asalin mace Musulma, inda ta ce hijabi ba suturar zahiri kawai ba ce, a’a, wani ɓangare ne na asalin mace.

Ta bayyana cewa a wannan fahimta, kunya ba tana nufin tsoro, rashin aiki ko rashin ƙarfi ba ce. Mace Musulma za ta iya kiyaye mutuncinta da iyakokinta, tare da kasancewa mutum mai ƙarfi, mai bayyana ra’ayinta, mai neman haƙƙinta da kuma mai tasiri a cikin al’umma.

Ra’ayoyin Yamma kan matsayin mace

Hikmat-Nia ta ce duk da cewa akwai ra’ayoyi daban-daban game da mata a ƙasashen Yamma, amma babban tsarin al’adu da tattalin arziki a Yamma a lokuta da dama yana kallon darajar mace ne bisa yawan abin da take samarwa ta fuskar tattalin arziki, yawan abin da take amfani da shi, kamanninta da kuma ƙarfin sayayyarta.

Ta ce a irin wannan fahimta, mace na iya samun ƙarin kulawa ne idan ta kasance ma’aikaciya, tana samun kuɗin shiga ko kuma ana amfani da ita wajen talla da kafafen yaɗa labarai.

Ta ƙara da cewa a wasu lokuta ana ɗaga taken ‘yancin mace, amma a aikace mace tana iya fuskantar nauyin yin aiki, ɗaukar alhakin gida, kula da yara, sannan kuma a lokaci guda ana sa ran ta dace da tsauraran ƙa’idojin kyau.

Musulunci ba ya auna darajar mace da kuɗi ko kamanni

Malama Hikmat-Nia ta bayyana cewa Musulunci ba ya danganta darajar ɗan Adam da kuɗin shiga, aiki, kamanni ko yawan ganin ta a cikin al’umma.

Ta ce: “A Musulunci, kafin mace ta kasance ma’aikaciya ko mai wani matsayi na zamantakewa, ita mutum ce mai mutunci kuma baiwar Allah.”

A cewarta, kasancewar mace a cikin al’umma ya kamata ya kasance wata dama ce ta bunƙasa kanta da yi wa al’umma hidima, ba wata hanya ta cin moriyarta ko amfani da ita ba.

Iyali ginshiƙin lafiyar al’umma ne

Malamar ta yi nuni da muhimmancin iyali a cikin al’adun Musulunci, inda ta bayyana cewa iyali ba cikas ba ne ga ci gaba, a’a, shi ne ginshiƙin lafiyar al’umma.

Ta ce idan aiki ko kasancewar mace a cikin al’umma ya jawo lalacewar kwanciyar hankali da tsaron iyali, to ya kamata a sake duba tsarin da ake bi.

Sai dai ta jaddada cewa hakan ba yana nufin a ɗora wa mace laifi ba. A maimakon haka, maza, masu ɗaukar ma’aikata da masu tsara manufofi suma dole ne su ɗauki nauyinsu wajen samar da daidaito tsakanin aiki, rayuwar iyali da kasancewar mace a cikin al’umma.

Mace Musulma ba ta keɓe kanta daga al’umma

Malama Hikmat-Nia ta ce mace Musulma ba ita ce wadda za ta kasance a gida kawai ba tare da sanin abubuwan da suke faruwa a cikin al’umma ba. Haka kuma ba ita ce wadda za ta yi watsi da asalin addininta da tsarin rayuwarta domin kawai ta samu damar shiga cikin al’umma ba.

Ta bayyana cewa mace za ta iya kiyaye asalin kasancewarta mace da siffofinta na tausayi, ba tare da bukatar kwaikwayon maza ba, kuma a lokaci guda ta kasance mai tasiri a fannoni daban-daban na rayuwa.

A cewarta, manufar ba ita ce kawar da bambance-bambancen da ke tsakanin jinsi ba, sai dai hana wariya da kuma hana mace samun damar bunƙasa kanta.

Hauza/ Malamar Hauza da jami’a ta bayyana wasu muhimman siffofin da ake buƙata ga mace Musulma a duniyar yau, inda ta jaddada cewa samun sani, sanin ainihin kai da kuma ɗaukar nauyi su ne ginshiƙan halayen mace Musulma.

Address

Qom

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kamfanin Dillancin Labaran Hauza posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share