19/07/2026
SHIN KO KUN SAN DALILIN DA YA SA ƊUMAMAR YANAYI (GLOBAL WARMING) KE DA HAƊARI?
Shin kun san cewa kusan kashi saba'in da ɗaya cikin ɗari (71%) na doron Duniya ruwa ne, yayin da kashi ashirin da tara cikin ɗari (29%) kawai ne ƙasa?
A cikin hikimar Allah, wani ɓangare na wannan ruwa ya daskare ya zama manyan duwatsun ƙanƙara (Polar Ice Caps) a ɓangarorin Arewa da Kudu na Duniya.
Ɗumamar yanayi (Global Warming) na nufin ƙaruwan matsakaicin zafin Duniya na tsawon lokaci. Wannan ƙarin zafin yana sa wasu sassan waɗannan manyan ƙanƙara su fara narkewa.
Yayin da ƙanƙarar ke narkewa, ruwan da ke shiga tekuna yana ƙaruwa, wanda ke sa ruwan teku ya ƙaru/tashi (Rise in Sea Level). Hakan na iya haddasa ambaliya (Flood) a wasu yankuna dake kusa da teku, tare da lalata gidaje, gonaki, da sauran abubuwan more rayuwa.
Bugu da ƙari, ɗumamar yanayi na haifar da sauyin yanayi (Climate Change), wanda zai iya jawo tsananin zafi (Heat Waves), tsananin sanyi (extreme cold), sauyin yanayin ruwan sama (Changes in Rainfall Patterns), fari (Drought) da ambaliyar ruwa (Flood), waɗanda ake kira (Extreme Weather Conditions).
Kare muhalli, rage gurɓata iska, da amfani da albarkatun ƙasa cikin hikima na daga cikin matakan da za su taimaka wajen rage tasirin ɗumamar yanayi da kare Duniyarmu.
Kimiyya tana taimaka mana mu fahimci yadda Duniyarmu ke aiki, domin mu kare ta daga irin waɗannan haɗurra.