
28/08/2024
Bienvenue sur Notes
Martani zuwa ga 'yenta'adda.
{Sati d'aya (1) bayan kisan gillar sarkin Sabon Birnin Gobir.}
Assalamu alekum warahamatullah✓
'Yen uwa barkarmu da warahaka.
Zamu yi magana ne akan masu aron bakin 'yen ta'adda ko masu kare 'yen ta'adda da cewar Gobirawa su fito suyi yaqi.
To, ku saurara ku jiya ; ko a qarnukkan da s**a gabata ana yaqi ne domin abubuwa k**ar haka : qwatar inci na bauta , d'aukar fansa don wata gaba da ta jima , ko d'aga darajar qabila ko daula. To 'yen uwa mabiya wannan shafin, ku fad'a mana d'aya daga cikin dalilin da mayaqi zai bar gidanshi in ba wannan ba ? Ko kuma d'aya daga cikin dalillan nan da yasa aka kashe Sarkin Gobir ?
Abin kula ko sani anan shine cewar :'yen ta'adda basu da inci ko ace zuciyar fansa balantana wata gabaa, ko qabila , ko kuma uwa uba masarauta da suke yaqi domin d'aga darajarta saidai wani guri na ra'ayin kansu ko kuma na wasu iyayen gidansu k**ar yanda muka tunanin cewar ana so ne a tarwatsa arewacin Nigeria ta fannin qirqirar fad'an qabilanci tsakanin Hausawa da fulani da zai shafi yankuna da dama tun daga Nigeria har Niger da sauransu domin turawa 'yen jari hujja na qasashen waje su dawo da mulkin mallaka a wannan yankin na Afirika musamman Sahel.
Sannan kuma in ana zancen yaqi ba'a maganar kud'i ko kuma dukiya maganar qarfin zucciya ne , izza , mazakuta, d'aukarwa rai...
'Yen ta'adda sun kashe sarki ne don kud'i koko ince dukiyar da s**a yi gajeren haqurin samu, sannan a qarshe da sanin cewar sune sanadiyar wafatin mai martaba daga Allah.
Da kuma taqular yaqi ne, da cewa zasu yi Gobirawa mun k**a sarkin Gobir kuyi shirrin yaqi ku zo waje kaza mu gwabza in kun ci mu da yaqi sai ku d'auko Sarkin Gobir kuyi tafiyarku.
Amman kash ! Anan 6uya s**a yi cikin daji s**a yi aika-aika " aikin jahilci " domin shi jahilici bai san kumya ba. To, ku sani cewar : mu GOBIRAWA "kumya garemu ba tsoroba". Amman su matsorata ne shi yasa har gawar sarki Tsoro ya hanasu su bayar.
In kuma tunanin 'yen ta'adda yaqi ne suke ba ta'addanci ba to, yak**ata su farka shi mayaqin gaske fili yake fitowa ya gwabza da jaruman mayaqan daula kahin/kafin ya baibaya ya kai ga Sarki. Ko kuma 'yenta'adda su fad'amana miye ribar abunda s**a yi saidai zagi da qara wa al'umma qiyayyarsu cikin zukata.
Kuma ku sani shi yaqi ba'a kashe tsofaffi , mata ko kuma qananan yara sai jarumin da aka yi kiti6is da shi a filin yaqi domin al'ummar ma a qashin kanta ganima ce a yaqi. Kenan anan ne za'a ayi alfaharin an yi yaqi/kisa.
A qarshe kuma, kar ku manta a halin yanzu ba GOBIRAWA ko kuma dukkanin Hausawa da kuke garkuwa da su da kuma hana su noma kuke zubdama mutunci ba harma da sauren 'yen uwanku fulani wad'anda basu ji basu gani ba.
>