Dr Rabiou Amadou

Dr Rabiou Amadou Touchez ces messages qui sonnent de l'avenir.
(1)

18/07/2025

Ko mu yi abun kirki ko na banza, duk ba daya daga cikinsu da zai sa mu dade a duniya ko kuma mu bar ta da sauri.

17/07/2025

Duk da soyayya ba ruwanta da kuɗi ko mulki, talakawa sukan shan wahala wajen neman su auru. Ko mi yake sa hakan ?

19/06/2025
28/10/2024

Daga Dan Guntun Gatarinka

« Baya ce tsanin hayewa gaba. » waiwaye ne gyaran tafiya. Su karade duk girman t**i, da hakan ne suke wayayya. Saurayi da budurwa can a da, kowa kunyar kowa yake. Amma yau juyin duniya, kan so se a yi ma caccake.

Tun kafin in kawo haka, na share tafiya mai tsayi. Yau dadi gobe bakin ciki, duk domin neman matsayi. Fata na kasance nai daban, daga masu fadin son zuciya. Allah kare ni da jan kafa, bautarka ta zan min kariya.

Na tashi da dogon bincike, ko mi na gani se na nada. In tara mahangan rayuwa, in sun kai min in yaryada. Ko mi ka yi yau zai zo gaba, tanadi mai kyau, wankan dare. Addu'a sam ba ta faduwa, sheri ne dan banzan kare.

Wane ne banza sakare? Kar dai fa ku ce min jahili. A'a mai tarin ilimi, se dai ba aikin hankali. To, ina anfanin mai sani, in ba ya koyon ji da kai? Duk fadin wannan duniyar, ba mai karfin yantar da kai.

12/12/2023

Wai akwai wani laifi ga wanda zai dauki littafi saboda ya koyi karatu ne? Wani masanin boye ya ce wai ba mai iya koyar da kanshi.

10/11/2022

✍️ In har akwai sauran lokaci to akwai sauran dama. Allah ya sa mu ga Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam. Ameen

18/09/2022

KUKAN KURCIYA 2:

Mai farga a soyayya shi ne abun ki ga yan mata. Kariyar darajar da yi ma kanshi kan sa ya rabu da maisonshi. Dalilin dai guda daya ne, mata ke nuna girman kai. Duk da cewa su ke a kasa, sun ki saukar da kai a kasa.

Ko wa ya zo da zancen auren, sai su daukeshi mai sauri. So suke a ja lokacin dadi, su handame kudin baiko. Sun tatse saurayi tsaftsaf sai su juya ba su ko waige. Mai yiwuwa ne ga yan mata akwai cin lokaci.

Saurayi ya yi ta zama da budurwa ba don za su aure ba. Ga dogon tadi in an zo fira dai ana zikiri. Har sai zance duk ya kare a koma jere sambatu. Maganar gaske ba ta da yawa, karya ita ce ta mai kuri.

Maza irin kujjiya ne sai an bara a san na kwarai. Karshen duniya ya dumfaro, marasa kumya suna zowa. Abun kunci da kokawa, gaskiya ta koma can baya. Manya duk sun yadda girmansu, tarbiyya ba ta amfani.

Masu ilmi da jahillan sun hau dodar a hanya dai. Masu gargadi fa sun kare sai sauran masu bin duniya. Lokacin abu ya zo a yishi don shirme sai a lalata. Iyakar komi duniya, mai hankali ya hankalta.

Aikin da mutum ya yi shi kadai ke binshi har kabari. Mummuna ka yi ko mai kyau Allah ne masanin komi. Ya Allah Hadamu Da Nagari , fatanmu zama a kan tsari. Ameen, don son Nabiyyuna Muhammadu daha son Kowa.

13/09/2022

Ba inda rayuwa ba ta kai mutum har bayan rai. Allah ya jikan magabata da mun ma dukka. “Watarana sai labari.” inji Bahaushe.

10/09/2022

Makiyi shi ke takatsantsan wajen ganin cewa bai yi kuskure ba. Su kuma gwanaye da kuskuren suke amfani wajen karin daukaka.

07/09/2022

Allah ka laɗɗafa mana, Allah ka yassure mana, Allah ka bamu faɗimatu sa'adatu. Ameen

05/09/2022

Buƙata ba ta da kaɗan ✔️

Adresse

Maradi

Téléphone

+22785378557

Site Web

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque Dr Rabiou Amadou publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Contacter L'entreprise

Envoyer un message à Dr Rabiou Amadou:

Partager