Dandalin Abuzaid Ɗan Nijer

Dandalin Abuzaid Ɗan Nijer Domin Al'ummar Niger
(1)

Gwamnan Yamai jagoran rusau, tun kwanan baya, ya yi gargaɗi za su rushe duk wurin aka gini, da ya kira "ba bisa ƙa'ida b...
17/09/2025

Gwamnan Yamai jagoran rusau, tun kwanan baya, ya yi gargaɗi za su rushe duk wurin aka gini, da ya kira "ba bisa ƙa'ida ba" ( a dokar ƙasa)

A cikin shirye-shiryen rushe masallacin da mu ka yi kira a baya, ga gwamnati ta yi hak'uri kar ta rushe, to Allah bai nu...
17/09/2025

A cikin shirye-shiryen rushe masallacin da mu ka yi kira a baya, ga gwamnati ta yi hak'uri kar ta rushe, to Allah bai nufa za a rushe, ga malamanmu nan suna kwashe kaya kafin gobe a zo a rushe.

Nasan wannan wurin sosai, wuri ne dake nesa ga hanya ma, ga duk wanda ya san 100meter a Yamai. Wallahi Bansan wace riba, ko akasin ta gwamnati za ta samu a rushe wannan katafaren masallacin da makarantar ba. Kasancewar wurin ya jima, amma bai taɓa takurawa kowa ba. Na taɓa zuwa can yin live (kai tsaye) lokacin da su Malam Kabiru su ka zo daga Nijeriya yin wa'azi, a shekarun baya.

Allah ya mai musu da alheri.
Hotuna: daga Mai karantarwa a masallacin wato imam Abass Hamissu Issa

17/09/2025

An ka$he mutane fiyeda 20 a Jahar Tillabery. Ɓangre daya kuma gwamnati ta bawa bokaye, da matsafa, bana na Nijar kaɗai ba, duk na AES suna warshagale-walle a babban birni, Yamai. Da sunan za su taimaki ƙasashen, ko kawo musu agaji, idan suna iya wani abo su su je, Mali, ƴan ta'adda sun can suna tare, hanya suna ƙone motocin dakon mai, sun hana mai isa babban birni. Ko su je Tillabery inda ake kashin bayin Allah ana karɓar kuɗaɗensu da dabbobin su.

Allah ya shirye mu.

14/09/2025

Dalilin k**a Ibrahim Yacouba:
Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un 😭
Wannan rayuwar mutane ina zamu ne?

Hausa dai ta riga, ta zama Harshen ƙasa a Nijar,  kuma ba abinda zai sauya hakan da yardar Allah.  Sai ma ƙara ɗaukaka n...
13/09/2025

Hausa dai ta riga, ta zama Harshen ƙasa a Nijar, kuma ba abinda zai sauya hakan da yardar Allah. Sai ma ƙara ɗaukaka nan gaba, In sha Allah. An ɗauki wasu aiki, ba su da aiki kullum a wannan kafar sai s**ar wannan dokar da kira a soke wannan matakin. Su sani hakan ba zata taɓa faruwa ba, ba za a koma baya ba ta wannan fannin.

Ko su yi Haƙuri, ko kuma su yi duk abinda za su yi.

Idan mu ka yi rashin sojoji wasun mu ko su yi addu'ar "Allah ya jiķansu" a shafukan su, ba za su yi ba, duk da za kaga s...
12/09/2025

Idan mu ka yi rashin sojoji wasun mu ko su yi addu'ar "Allah ya jiķansu" a shafukan su, ba za su yi ba, duk da za kaga suna faɗin abubuwa ko yin addu'a a bayyane, a shafukan su, idan wani abo a duniya, ya faru da sauran. Amma namu musulmi wasun su, suna ganin duk mai fada, ko yi musu addu'a, a wannan kafar ko kawo labarin, ko yaɗawa, da jaridu na cikin gida, ke yi, ko masu wallafowa a ƙashin kansu,(ra'ayi) ana musu kallon matsayin masu zagon ƙasa, ga Ƙasa. A (tunaninsu kenan fa)

Don haka mu sani: yadda mu ke ganin yahudawan, yammacin duniya suna haduwa, musamman haramtacciyar ƙasa israala suna cutawa musulmi, suna musu k!san gilla, to Kusan haka ne nan a yankin sahel Afrika, baƙaƙen yahudawa, "Fulanin Daji " su ka addabemu, za su yiwa sojojinmu, da al'ummar mu, k!san gilla na wulaƙanci na rashin tausayi. Matsalar ma da (Sunan addini) kusan suma yahudawan ga na afrika idan su ka samu dama, da kayan aiki, irin na yahudawan yamma, za su yiwa musulmi illa k**ar yadda yahudawa ke mana.

Kenan idan mun tashi magana, ko addu'a, saboda ƙwatowa, ko don a ji koken al'ummar musulmi, ko tsinuwa ga yahudawan yamma, mu dinga haɗawa da baƙaƙen yahudawa da ke nan cikinmu suna addabarmu, gabaɗaya Allah ya hadasu ya ts!ine musu albarka.

Allah ya kawowa musulmin duniya sauki, game da matsalolin da s**a mamaye mu.

Magana ake ta Nan jiya fa, an kai hallaka mana fiyeda sojoji 20 a Tillabery. Har yanzu banga sanarwar gwamnati kan abin ...
11/09/2025

Magana ake ta Nan jiya fa, an kai hallaka mana fiyeda sojoji 20 a Tillabery. Har yanzu banga sanarwar gwamnati kan abin ba, ko sanarwar jaje ga iyalan waɗannan sojojin ba, sai sanarwar harin da haramtacciyar ƙasa, ta kai ƙasar Qatar. Nake ganin tana yawo a wannan kafar.

To shikenan.
Allah ya jiƙan sojojinmu dake filin daga don kare rayukanmu, ya gafarta musu. Yasa sun huta.

Adresse

Koira-tagui
Niamey

Site Web

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque Dandalin Abuzaid Ɗan Nijer publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Contacter L'entreprise

Envoyer un message à Dandalin Abuzaid Ɗan Nijer:

Partager