07/10/2023
MURYAR MUTANEN AREWACIN NIGERIA MAZAUNA JAMHURIYAR NIGER
SHIMFIDA:
An samar da wannan 'page' ne domin kara samun hadin kai tsakanin Hausawa, mutanen arewacin Nigeria mazauna jamhuriyar Niger.
DALILIN BUDE WANNAN 'PAGE'
Duk da cewa mun san akwai hadaddiyar kungiyar 'yan Nigeria mazauna jamhuriyar Niger wato 'Association of Nigerian Citizen In Niger' (ANCN) da kuma wasu kungiyoyin na jihohi kamar kungiyar 'yan jihar Sokoto ko Kebbi ko Katsina ko kuma Zamfara da Kaduna da da Kano da sauran su. Duk da hakan sai muka ga dacewar samar da wannan shafi na facebook, wanda ta hanyar sa ne muke sa ran za a rika samun labaran halin da 'yan uwan mu ('yan arewacin Nigeria mazauna jamhuriyar Niger suke ciki). Saboda haka, muna iya cewa samar da wannan 'page' ba yana nufin mun kirkiri wata sabuwar kungiya bace. Sai dai muna fata wannan shafin ya habaka ya zama dalilin kara kawo cigaba a tsakanin al'ummar mu ta yadda ba a yi tsammani ba.
MANUFAR WANNAN AIKI:
Matsalar komabayan tallalin arziki da Nigeria ta samu kanta a ciki, ya sanya musamman mutanen arewacin Nigeria masu sana'o'in hannu daban-daban da kasuwanci iri-iri suke kwararowa zuwa birane da kauyakun jamhuriyar Niger. Bisa wadannan dalilan muka yi tunanin cewa wasu abubuwa na iya faruwa na farin ciki ko akasin haka da mutanen mu, wanda ya kamata a ce ana da wata kafa wacce za a rika jin labarin juna, musamman a wannan yanayi na dambarwar juyin mulki da ake ciki a jamhuriyar ta Niger. Sannan muna da hanyar jin duk wani abu da ya kamata a sanar da mutanenmu daga 'Nigerian Embassy' da ke Niamey, Niger da kuma daga hadaddiyar kungiyar 'yan Nigeria wato (ANCN).
Muna sa ran wannan 'page' zai taimaka sosai wajen karban sakonni da kuma isar da sakonnin kan halin da 'yan uwan namu 'yan arewacin Nigeria mazauna jamhuriyar din Niger suke ciki a wuraren da suke, idan bukatar hakan ta taso.
AYYUKAN DA WANNAN 'PAGES' ZAI RIKA YI:
(1) Kira zuwa ga sanin dokoki da kuma bin dokokin zama a jamhuriyar Niger.
(2) Kira zuwa ga muhimmancin Kyakkyawar mu'amala da abokan hulda.
(3) Kira zuwa ga muhimmancin gaskiya da rukon amana.
(4) Kira zuwa ga muhimmancin hadin kai tsakanin 'yan arewacin Nigeria mazauna jamhuriyar Niger.
(5) Kira zuwa ga magana da murya daya akan abinda ya shafe mu.
(6) Kira zuwa ga muhimmancin zumunci da hadin kai tsakanin 'yan arewacin Nigeria mazauna jamhuriyar Niger.
(7) Za mu rika yin sanarwoyin na aure, suna da kuma mutuwa da sanarwoyin tarukan da 'yan arewacin Nigeria mazauna jamhuriyar Niger din suke shiryawa, idan bukatar hakan ta taso.
(8) Wannan 'page' zai bukaci akalla mutum dai-dai 'yan arewacin Nigeria mazauna jamhuriyar Niger daga kowace jiha cikin jihohi takwas (8) na jamhuriyar Niger din, wadanda za su zama wakilan wannan 'page' kuma wakilai a cikin 'yan arewacin Nigeria da suke zaune tare da su a jihohin da suke, domin su rika samar mana da bayanan da muke bukata lokaci zuwa lokaci.
(9) Cikin 'yan arewacin Nigeria mazauna jamhuriyar Niger din, mai bukata na iya aiko mana hotunan aikin da yike yi ko kayan da yike siyarwa tare da lambar waya da kuma adireshin wajen da yike domin mu tallata masa a wannan 'page', domin ya samu abokan hulda a cikin mutanen arewacin Nigeria mazauna jamhuriyar Niger din da ma wadanda ba 'yan Nigeria din ba.
KA'IDOJIN MU A HALIN YANZU:
(1) A yanzu, ba mu da shirin tambayan kowa ko dala don yin wani aiki.
(2) Ba za mu wallafa wani abu ko wani labarin da ya fita wajen abubuwan da muka tsara tunda farko ba.
(3) Ba za mu yarda wani ya canza mana tsari ba.
Muna fata Allah ya sa mu fara wannan aiki a sa'a kuma da fatan wadanda muka tsara wannan abin domin su, za su bamu cikakkiyar hadin kai.
Mun gode!
Domin Karin Bayani:
Appél±22795862336/±22789134440
WhatsApp: ±2348033718219.
ASABAR/07/102023
https://www.facebook.com/profile.php?id=61552361421165