Siyasa da Rayuwa

  • Home
  • Siyasa da Rayuwa

Siyasa da Rayuwa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Siyasa da Rayuwa, Magazine, .

Wannan shafi ne na siyasa da rayuwa, wanda yake aiki tukuru, wajen fayyace al'amuran dake gudana a yau-da-gobe, domin wayar da kai, ilmantarwa, fadakarwa da ciyar da al,umma gaba, bisa hasken ilimi.

Littafin "War" na mashahurin dan jarida Ba'amurke, Bob Woodward, wanda ya fito ranar 15 ga watan Oktoba, 2024, ya tona a...
01/11/2024

Littafin "War" na mashahurin dan jarida Ba'amurke, Bob Woodward, wanda ya fito ranar 15 ga watan Oktoba, 2024, ya tona asirin shugabannin Larabawa, musamman shugaban Masar, Janar Sisi, cewa sun taimakawa Israila a yakinta na kare-dangi a kan Falasdinawa.

27/10/2024

"ولا تهنوا في ابتغاء القوم ان تكونوا تالمون فانهم يالمون كما تالمون وترجون من الله ما لا يرجون..."

Babu shakka ana kashe mana farar hula a Gaza, to amma sojojin Israila suna daukar dalma.

25/10/2024

Mu abinda muka sani, azzaluman shugabanni kaddamar da jihadi ake yi a kan su, a kifar da gwamnatocinsu a kafa sababbi, kamar yadda Usman Danfodiyo ya yi da sarakunan kasar Hausa.

19/10/2024

Netanyahu: Kere na yawo, zabo na yawo...

19/10/2024

Amana ce a kanmu yadda muka yaki aqidar Iran mu yaki siyasar Sa'udiyya.

18/10/2024

Yau shekara 50 ke nan cif da Mahaifina ya rasu.
Don Allah ku yi masa addu'a.

18/10/2024

ان مسكم قرح فقد مس القوم قرح مثله وتلك الايام نداولها بين الناس

18/10/2024

ولا تحسبن الذين قتلوا في سبيل الله امواتا بل احياء عند ربهم يرزقون.

17/10/2024

العدو لا يعرف اسمى الاماني.

16/10/2024

Maigida ya ce Yayanta su je su ci Abinci a gidan Kishiyarta, amma ta Hana!!

Wani labari ne da gidan radiyon Freedom Radio ya yada jiya a cikin shirinsa mai farin jini, In Da Ranka.

Maigida ne ya doki matarsa saboda ya ce yayanta (yayansa ke nan) su je gidan kishiyarta su ci abinci, ita kuma ta hana.

Labarin ya yi matukar bakanta mun rai saboda ya nuna yadda muke zaune da ka, babu la'akari da Shari'a, ko al'ada ko sanin ya-kamata.

A Shari'a da al'ada, maigida yana da iko da hurumin ya tura yayansa daya gidan nasa su je su ci abinci da daya matar tasa ta dafa. Amma a wajen matan zamani, wadanda su ba ruwansu da Shari'a ko al'ada, sai bin son zuciya, bai isa ba.

Wai shin ina matanmu s**a dosa ne?! Shi ke nan yanzu yayan kishiyoyi sun dena zumunci ke nan? Shin auren mata biyu, ko uku ko hudu, haramun ne? Yanzu matanmu ba su da hankalin da za su bambance tsakanin kishiya da yayanta (watau yayan mijinsu)?

Dukan da wannan miji (na cikin labarin In Da Ranka) ya yi wa matarsa yana iya zama kuskure ne, amma ita kuma abinda ta yi fa? Na ce yana iya zama, saboda idan ba wannan ne karo na farko ba da matar take hana yayansa zuwa gidan daya matar tasa, to babu laifi idan ya dake ta, duka na Shari'a.

Abinda wannan mata ta yi rashin addini ne, da rashin mutunci, da rashin hankali, da rashin tarbiyya, da rashin sanin ya-kamata, da zunzurutun jahilci. Gaba da kiyayya take so ta dasa a tsakanin yan uwa, yayan uba daya, babu gaira, babu dalili.

Irin wannan dabbanci na matan zamani dole a yake shi, kuma dole al'umma duka su yi Allah-wadai da shi.

Kuma na lura mai gabatar da wannan shiri na In Da Ranka da na yi nuni zuwa gare shi (wadda ita ma mace ce) ta nuna rashin hadarin wannan dabbancin a fakaice. (Watakila ba da niyya ta yi ba.) Ta ce wai mijin ya doke ta "don kawai ta hana yayanta zuwa gidan kishiyarta su ci abinci." Don kawai da ta ce, kuskure ne babba saboda yana nuna abin ba wani babban al'amari ba ne da ya isa a yi duka a kansa.

Daga karshe ina kira ga matanmu da su dawo cikin taitayinsu. Kishi ba hauka ba ne! Haka nan auren mace fiye da daya ba haram ba ne. Kuma ko ba kome ya fi zina.

Kamar yadda nake kira ga maza da kada su sassauta wajen ganin ba'a raba kan yan uba, an dasa gaba da kiyayya ba a tsakanin su.

Allah ya shirye mu baki daya.

15/10/2024

Tsakanin Shugabannin Nijeriya da Talakawansu

Alaka tsakanin Shugabannin Nijeriya da Talakawansu alakar bayi ce da iyayen gidansu. Maimakon shugabanni su yi hidima ga Talakawansu, kamar yadda abin yake a ko wane tsarin mulki a duniya, a Nijeriya talakawa ke bauta, su kuwa shuwagabanni su kwashe arzikin kasa don amfanin kawunansu da iyalansu da yan barandansu.

Ana yin gwamnati ne don ta sarrafa arzikin kasa, ta samar da ababen more rayuwa ga yan kasa, amma banda a Nijeriya. A kasata Nijeriya banda ma gwamnati ta kasa samar da kome ga talaka, kullum sai tatsar sa take yi, tana yi masa alkawuran karya da rainin wayo.

Gwamnatin Nijeriya ta kasa samarwa yan kasa tsaron rayukansu da dukiyoyinsu, ta bar su a hannun yan fashi da yan ta'adda da yan daba da yan fashin daji da sauran dukkan nau'i na masu laifi. Yau yan Nijeriya su ke samawa kansu tsaro. Don haka hatta a cikin birane ko ina sai shingaye kake gani suna tashi don ba wa kai tsaro.

Gwamnatin ta gaza ba wa yan kasa abinci, a yau yunwa tana kashe mutane ana ji, ana gani, babu ruwan shugabanni. Su aikin sace dukiyar mutane da kulle-kullen siyasa ne ya dame su. Abinci ya fi karfin talaka saboda rashin abincin da tsadarsa da rashin kudi a hannun mutane.

Gwamnati ta gaza ba mutane ilmi, yau kowa ya koma ga makarantu masu zaman kansu, sai dai wanda ba shi da hali shi ke kai yayansa makarantun hukuma wadanda suna ne kawai na makarantu suke dauke da shi, amma ba hakika ba.

Gwamnati ta kasa samar da tsarin lafiya ga talakawa, don haka mutane sun koma asibitoci masu zaman kansu, saboda asibitocin gwamnati sun zama suna kawai, kuma a hakan ma kome sai talaka ya biya.

Gwamnati ta kasa ba mutane ruwan sha, saboda haka talakawa sun koma shan ruwan jiyoji da kududdufa, nusamman a yankunan karkara, masu hali kuma su haka rijiyoyin burtsatsae.

Gwamnati ta gaza samawa talakawa wutar lantarki, don haka mutane sun hakura da hasken lantarki kuma sana'o'i da s**a dogara da wutar lantarki duka sun tsaya, abinda ya kara jefa mutane cikin talauci. Masu hali sun koma amfani da "Sola", marasa shi kuma ko oho.

Gwamnatin Nijeriya sam ta daina gina tituna, sai dai t**in kabilanci da ya fi ko wanne t**i a duniya tsada. Tituna duka sun rugurguje, ba bambanci tsakanin birane da dazuka. A sakamakon haka, kullum sai hadurra ake yi wadanda suke lakume rayukan talakawa da haddasa asarar dukiya. Kuma saboda tsabar raina talaka wai harajin t**i za su dawo da shi, kowa ya hau matattun titunansu sai ya biya.

Ya Allah Annabinka Muhammad (SAW) ya yi addu'a, ya ce:

"اللهم من ولي من امر امتي شيءا فشق عليهم فاشقق عليه." (رواه الامام مسلم)

Ma'ana: "Ya Allah wanda ya shugabanci wani abu daga al'amarin al'ummata, kuma ya tsananta musu, ka tsananta masa."

Ya Allah ga Shugabanninmu sun tsananta mana, Allah ka tsananta musu.

06/10/2024

Shekara Guda da Yakin Israila a kan Gaza: Nasarori da Busharori (1)

Yau ake cika shekara guda da mayakan kungiyar Hamas s**a kai gagarumin hari na tarihi a kan haramtacciyar kasar Yahudu ta Allah-ya-isa, watau Israila.

Harin da s**a yi wa lakabi da Dufanul Aqsa (Ambaliyar Masallacin Qudus) ta aike da Yahudawa 1,300 Barzahu a wannan safiya mai albarka da dumbin tarihi.

Biyo bayan wannan hari mai albarka, kasar Bani Yahudu ta shiga halin firgici da alhini kwatankwacin wanda kasar Amurka ta shiga a ranar sha daya ga watan tara (9/11) sakamakon harin da kungiyar Alqaida ta kai kan cibiyar kasuwanci ta duniya a birnin New York, shekaru ishirin da uku da s**a wuce.

Daga wannan rana, Israila ta kaddamar da yakin kare dangi a kan Musulmin Falasdinu, tana kashe maza da mata da kananan yara da tsofaffi, tare da ruguza masallatai da makarantu da asibitici da kasuwanni da gadoji da matatun ruwa da tashoshin lantarki da gidajen burodi da gidajen kwana na yan kasa farar hula. Adadin wadanda s**a rasa rayukansu ya kai sama da dubu arba'in da daya (41,000) izuwa yau, masu rauni kuwa sun haura mutum dubu dari (100,000).

Duka wannan barna duniya tana kallo: Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Turawa masu karyar kare hakkin dan Adam da kungiyoyin kasa-da-kasa masu rajin kare hakkin dan Adam duka sun zuba ido, sun yi shuru a gaban wannan ta'asa wacce take nuna Yahudawa a matsayin bararoji masu halin namun daji.

Haka nan kasashen Musulmi sun yi shuru, sai yan kadan wadanda suke tabuka irin abinda ake cewa "motsi ya fi labewa". Su kuwa shugabannin kasashen Larabawa abinda s**a yi ya fi labewar muni. Yawancinsu suna goyon bayan Yahudawan Israila a boye saboda kare karagunsu da kujerunsu na mulki. A yayin da malaman fada s**a zama shaidanun bebaye, ba cas ba as.

To sai dai duk da wannan, dakarun Musulunci na mayakan Hamas da kungiyar Jihad da masu taimaka musu na kungiyoyin Shi'ar Hizbullah ta Labanan da Hutsawa na Yaman, ba su gushe ba suna dandanawa sojojin Israila bone a filin daga a tsawon wannan shekara.

Kuma wannan shi ne ya kawo mu ga nasarori da s**a tabbata da busharori masu zuwa, insha Allah.

Za mu ci gaba.

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Siyasa da Rayuwa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Siyasa da Rayuwa:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share