
09/09/2025
Faransa ta dauki alkawarin mara wa Qatar baya bayan harin Isra’ila a Doha
Gwamnatin Faransa ta bayyana goyon bayanta ga Qatar, bayan harin da Isra’ila ta kai kan gine-ginen zama a babban birnin Doha, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka da kuma jikkata mutane da dama.
Ministan Harkokin Wajen Faransa ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, “Faransa na tare da Qatar wajen kare mutuncin kasa, tsaron al’umma, da kuma hakkinsa na kasancewa mai ‘yanci ba tare da tsangwama daga waje ba.”
Harin da aka kai a Doha ya haddasa s**a daga kasashen duniya, ciki har da Kungiyar Hadin Kan Larabawa (OIC) da Majalisar Dinkin Duniya, inda s**a bayyana shi a matsayin babban take hakkin bil’adama da kuma saba wa ka’idojin kasa da kasa.
Qatar dai ta yi tir da wannan hari, inda ta ce an kai shi ne da gangan kan gidajen da ke dauke da wasu manyan ‘yan siyasar Hamas.
Mahukuntan Doha sun bayyana harin a matsayin keta doka da kuma wata babbar barazana ga zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.