16/06/2025
12 AVANTAGES DU SOURIRE.
… Voir plus
AMFANI 12 NA MURMUSHI.
"Murmushinka ga ɗan'uwanka sadaƙa ne" Hadith
1. Murmushi da fara’a wasu ne daga cikin kyawawan ɗabi’u da ke da tasiri mai kyau a rayuwar dan Adam. Duk da cewa su ne mafi sauƙin aikatawa cikin alheri, su ne kuma ke haifar da manyan sauye-sauye a zamantakewa a lafiya, da kuma zaman lafiya tsakanin al’umma.
A al’ada, addini da kimiyya duk sun tabbatar da muhimmancin murmushi da fara’a a rayuwar yau da kullum.
2. Murmushi yana sanya mutane jin daɗin kasancewa tare. Yana kawo kusanci tsakanin abokai, ‘yan uwa, da maƙwabta.
3 . Mutumin da ke yawan murmushi yana da sauƙin mu’amala. Ana jin daɗin zama tare da shi, hakan kuma yana rage husuma da gaba.
4. Fara’a alama ce ta ladabi da mutunci. Kuma Yana nuni da kyakyawar zuciya da ƙimar da mutum ke ba wasu.
5. Mutane da ke musayar fara’a na gina yanayi mai daɗi a tsakanin su, wanda ke taimakawa wajen kawar da damuwa da kunci.
6. Murmushi Yana Rage damuwa (stress): Bincike na kimiyya ya tabbatar da cewa murmushi yana rage sinadarin cortisol, wanda ke da alaƙa da damuwa.
7. Mutum mai murmushi akai-akai yana samun ƙarfi wajen yaƙar cututtuka, saboda murmushi na ƙara yawan sinadarin endorphins da serotonin, masu kawo farin ciki.
8. Murmushi yana rage hawan jini da bugun zuciya, yana hana cututtukan zuciya.
9. Murmushi alama ce ta natsuwa da yarda. Kuma Yana iya dakile tashin hankali ko sabani kafin ya faru.
10. Al’umma da ke yawan fara’a da musayar murmushi na da ƙaranci wajen samun rikici, saboda akwai jin daɗin zama tare da juna.
11. Musayar murmushi tsakanin mabanbantan al’umma na nuna haɗin kai da zaman lafiya.
12. Murmushi da fara’a ba su da tsada, amma suna da fa’idodi masu yawa ga rayuwar ɗan adam. Su ne mabuɗin zaman lafiya, ƙauna, da lafiya mai ɗorewa. Idan kowane mutum zai riƙa amfani da murmushi da fara’a a cikin hulɗarsa da jama’a, tabbas za a samu rayuwa cike da farin ciki da zaman lafiya.
Bahaushe yace:
"Shinfiɗar fuska tafi ta tabarma."
Allah taa'la Ya gyara zukatanmu da halayanmu.