28/05/2024
Click https://youtu.be/ButvT00Y8V0
Tauraro Na Da Moofy Live on Alheri Channel
✅ Barka, Nazo muku da albishir daga Alheri channel, wannan albishirin babba ne, me kyau, me ratsa zuciya kuma ina farin ciki da wannan batu.tashar alheri zata baku dama domin ku mika sakon godiya ga masoyanku,Wato alheri channel world appreciation day.Mai suna@Taurarona Live season 1 zango na 1 da zaa fara ranan laraba 29 zuwa 31 na watan mayu 2024 karfe Tara na dare live a Alheri channel akan YouTube.
🏆 Shin ko kun Sani cewa akwai Wani bangera na rayuwar biladama da ba a fadarsa yadda ya kamata?
Mutane basu magana a kansa a shafukar sada zumunta ko ince a fili kamar yadda ake yada munanan laifuka da mutane ke aikatawa?
Wannan sashen mun kawo shine domin wallafa mutanen da suke kyautatamana, taimakamana da s**a zame mana madogara ko sila na cimma nasara a rayuwarmu. Mutanen Nan zasu iya kasancewa iyaye, Yan uwa, abokai, miji ko mata, shugaba ko abokin aiki. Zamu karrama su da nuna godiya garesu ta salo me burgewa kan Alheri channel duk wata so daya kuma zamu fara da wannan watar me gabatowa. Ga yadda zaku kasance tare da ni a wannan shiri
1. Zaku rubuto sako na Mika gaisuwa da jinjinawa tare da takaitaccen labari akan tauraron da kuke so mu wallafa da Kuma dalilin dayasa ya zama abin alfahari gareku tare da hotonsa. ko Kuma kuyi gajeren bayani cikin bidio Wanda tsayinsa be Fi minti 3 ba.
2. Bayan Kun rubuta labarinku ko Kuma kunyi bidion na nuna godiya ga jaruminku/tauraronku sai ku turo mana a kowane shafukar sada zumuntanmu kamarsu TikTok, Facebook da Kuma Instagram. Zamu dauka mu wallafa a shirin mu na live season 1 phase 1 a Alheri channel da ke kan YouTube.
✅ Zamu gabatar dasu, mu kuma haska tauraronku a ranar nuna godiya na Duniya ta Alheri channel a shirin TauraroNa akan YouTube da Kuma shafukarmu na sada zumunta.
Mu taru mu nuna godiya tare da jinjinawa mutanen da s**a haskaka rayuwarmu Duniya ta sansu
A cikin shirin TauraroNa live zango na 1.... Jinjinawa mutanen kirki cikin biladama
Godiya muke.😎🥰😍
Tip
✅ Barka, Nazo muku da albishir daga Alheri channel, wannan albishirin babba ne, me kyau, me ratsa zuciya kuma ina farin ciki da wannan batu.tashar alheri zat...