Mujallar Arewa

  • Home
  • Mujallar Arewa

Mujallar Arewa Mujallar Arewa jarida ce da take kawo muku sahihan labarai da Harshen Hausa akan Abubuwan da suke faruwa a Arewacin Najeriya da ma Duniya baki daya
(2)

A Cikin Motocin Da Aka Turo Min Na Zaba Za A Siya Min Har Da Ta Naira Milyan 150 Amma Sai Na Zabi GLK Saboda Na Fin Sont...
08/08/2025

A Cikin Motocin Da Aka Turo Min Na Zaba Za A Siya Min Har Da Ta Naira Milyan 150 Amma Sai Na Zabi GLK Saboda Na Fin Sonta, Cewar Rahama Sa'idu

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Allah Ya Yiwa Mahaifin Bello Galadanci (Ɗan Bello) Malam Habib Rãșuwa yanzun nan.Alla...
07/08/2025

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Allah Ya Yiwa Mahaifin Bello Galadanci (Ɗan Bello) Malam Habib Rãșuwa yanzun nan.

Allah ya gafarta masa.

YANZU-YANZU: Amnesty International Ta Yi Kira Ga Hukumomin Nijeriya Da Su Saki Dan Gwagwarmaya SoworeKungiyar kare haƙƙi...
07/08/2025

YANZU-YANZU: Amnesty International Ta Yi Kira Ga Hukumomin Nijeriya Da Su Saki Dan Gwagwarmaya Sowore

Kungiyar kare haƙƙin bil’adama ta duniya, Amnesty International, ta yi kira ga hukumomin Nijeriya da su saki ɗan gwagwarmayar kare hakkin ɗan Adam kuma ɗan jarida, Omoyele Sowore, wanda ke fuskantar tsangwama da hana 'yanci daga 'yan sanda.

Ƙungiyar, ta bayyana cewa dole ne a saki Sowore ba tare da wani sharaɗi ba, tare da janye dukkan zarge-zargen siyasa na ɓata-gari da ake yi masa. Ta kuma ce ya kamata gwamnati ta saurari masu s**a, maimakon toshe bakinsu ta hanyar amfani da ƙarfin iko.

Amnesty International ta jaddada cewa ya zama wajibi a bawa Sowore damar yin amfani da 'yancinsa na furta albarkacin baki, da gudanar da taron lumana.

Me zaku ce?

Duk wani jami'in sojin da aka gani sanya da jar hula ko jar ɗauri a gannu kamar yadda waɗannan su ka yi, me hakan ke nuf...
03/08/2025

Duk wani jami'in sojin da aka gani sanya da jar hula ko jar ɗauri a gannu kamar yadda waɗannan su ka yi, me hakan ke nufi?

Muna kira ga jam'iyyar hadaka ta ADC da ta gaggauta bawa wannan budurwar mukami, domin tafiyar ta matasa ce Maza da Mata...
03/08/2025

Muna kira ga jam'iyyar hadaka ta ADC da ta gaggauta bawa wannan budurwar mukami, domin tafiyar ta matasa ce Maza da Mata, inji Ibrahim Umar.

Me za ku ce?

📸 AAR Hausa

Hotunan Jaruma Hadiza Gabon A Daren Jiya A Wajan Bikin Jarumin Film Din Facebook Wato Jamilu Kochila
03/08/2025

Hotunan Jaruma Hadiza Gabon A Daren Jiya A Wajan Bikin Jarumin Film Din Facebook Wato Jamilu Kochila

Tinubu Ga Matasan Najeriya: Ku Yi Amfani da Fasahar Zamani Wajen Gina Ƙasa, Ba Wai Kawai Fad’ar Ra’ayi BaShugaban ƙasa B...
02/08/2025

Tinubu Ga Matasan Najeriya: Ku Yi Amfani da Fasahar Zamani Wajen Gina Ƙasa, Ba Wai Kawai Fad’ar Ra’ayi Ba

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana hakan ne yayin taron Progressives Digital Media Summit da aka gudanar a ranar Juma’a a birnin Abuja. Ya yi kira ga matasa da su yi amfani da kafafen sada zumunta ba kawai don bayyana ra’ayinsu ba, sai dai wajen warware matsalolin ƙasa, samar da mafita, da jagorantar sauyi. Ya ce matasa su zama jagororin ci gaba, su inganta ƙwarewar dijital, su kuma tabbatar da gaskiya da amana a kowanne mataki. Ya jaddada cewa matasa su ne babban jari da Najeriya ke da shi, kuma zaɓin da suke yi shi ne zai tsara makomar ƙasar.

Ɗan Sanda Ya Ƙi Karɓar Cin Hancin Naira 800,000 Don Sako Wanda Ake Zargi da Fashi a Akwa IbomWani jami'in 'yan sanda mai...
02/08/2025

Ɗan Sanda Ya Ƙi Karɓar Cin Hancin Naira 800,000 Don Sako Wanda Ake Zargi da Fashi a Akwa Ibom

Wani jami'in 'yan sanda mai kula da sashen makamai na musamman (SWAT), Ebong Thompson, ya ƙi karɓar cin hancin naira 800,000 da aka ba shi domin ya sako wanda ake zargi da fashi da makami tare da ɓoye laifin.

MINISTAN MATASA....Daga Rabiu Biyora Ganin irin yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsaya tsayin daka wajen jana'izar mar...
22/07/2025

MINISTAN MATASA....

Daga Rabiu Biyora

Ganin irin yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsaya tsayin daka wajen jana'izar marigayi tsohon Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari da kuma kyakkyawar alakar dake tsakanin Buhari da Tinubu sai nake ganin abu ne mai kyau a siyasa Shugaba Tinubu ya bawa Yusuf Buhari mukamin Minista musamman Ministan Matasa...

Yin hakan zai kara dankon zumunci sosai...

A yanzu Yusuf Buhari yana da shekara 33 a duniya shekarun da zasu bashi damar tsayawa kowacce irin takara a Nigeria...

A bangaren siyasar Arewa kasancewar Yusuf Buhari minista a gwamnatin Tinubu hakan zai iya zama dalilin da Tinubu zai samu karin magoya baya daga yankin Arewa Maso Yamma.....

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Omo Ovie Agege da tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Hon. ...
22/07/2025

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Omo Ovie Agege da tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Hon. Ahmad Idris Wase da sauran ƴan tawagarsu sun ziyarci gidan marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ke Daura domin yi wa iyalinsa ta'aziyyar rasuwarsa.

Shin Kuna goyon bayan Hawa'u Halliru gwangwazo ta cigaba da fitowa a shirye shiryen gidan talabijin na RFI - Hausa ?
20/07/2025

Shin Kuna goyon bayan Hawa'u Halliru gwangwazo ta cigaba da fitowa a shirye shiryen gidan talabijin na RFI - Hausa ?

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mujallar Arewa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Mujallar Arewa:

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share