06/06/2025
Sakon Barka da Sallah Daga Kungiyar Arewa Online Journalists Forum (AOJF)
A madadin Shugabanni da daukacin mambobin Kungiyar Arewa Online Journalists Forum (AOJF), muna mika sakon Barka da Sallah ga daukacin 'yan Najeriya, musamman al’ummar Musulmi a fadin duniya baki daya.
Muna taya ku murnar kammala azumin watan Zulhijja da kuma gudanar da ibadar Eid-el-Kabir cikin Albarka da aminci. Wannan lokaci ne na nuna biyayya, tawali’u, da hadin kai kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya nuna mana kyakkyawan misali na sadaukarwa.
A wannan rana mai albarka, muna rokon Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya ba mu zaman lafiya, albarka da cigaba a Najeriya da duniya baki daya. Hakanan muna kira da a ci gaba da yi wa kasa addu’a da kuma kokarin wanzar da gaskiya, adalci da zaman lafiya a dukkan fannonin rayuwa.
Muna kuma kara jaddada kudirin AOJF na ci gaba da yaki da labaran ƙarya (fake news), da kare martabar aikin jarida a Arewa da Najeriya baki daya.
Barka da Sallah!
Eid Mubarak!
Taqabbalallahu minna wa minkum.
Malam Barrah Almadany
Shugaban AOJF
06/06/2025