
20/09/2025
SHEIKH SANI YAHAYA JINGIR ALHERI NE WA DUNIYAR MUSULUNCI BA SHARRI BA
Jiya ina hanyar Abuja na tsaya nayi sallah, bayan na idar ina hutawa sai na kunna data, sai naga anyi mentioned sunana a karkashin wani jawabi da Adam Ashaka yayi akan Sheikh Sani Yahaya Jingir
Adam Ashaka yace: "Ba'a taba jarabar Musulmin Nigeria da musifa kamar Sheikh Sani Yahaya Jingir ba, domin kasancewarsa cikin al'umma musifa ne, ya mayar da munbarinsa gurin tallata 'yan siyasa.." inji Adam Ashaka
Hakika wadannan kalamai da Adam Ashaka ya jingina su ga Dattijo Malami irin Sani Yahaya Jingir sun munana matuka, kuma ban taba zaton zai furta kalamai masu muni irin haka a kansa ba
Sheikh Sani Yahaya Jingir Malamin addini ne wanda ya tsayu tsayuwan daka akan karantar da tauhidi da Sunnah, amma saboda kuskuren fahimtarsa akan siyasa sai ace ba'a taba yin musifa kamarsa ba, haba Adam Ashaka ina hankalinka ya tafi?
Ko ka san shekarun da Malam Sani Yahaya Jingiri yayi yana karantar da addinin Allah kafin Demokaradiyya tayi tasiri a Nigeria?, nima bana tare da ra'ayi da fahimtarsa akan siyasar Demokaradiyya, amma hakan ba zai sa na manta alherinsa na kirashi da musifa ba, Malam Sani babban alheri ne da garkuwa wa Musulunci
Allah bai taba jarabar Musulmin Nigeria da musifa wacce ta kai na Maitatsine da B0k0 Har@m da masu da'awar komai Allah ne ba, Adam Ashaka ya akayi ka manta da wadannan? a matsayinka na dalibin ilimi baka san cewa shirka shine laifi mafi muni a gurin Allah ba, shin Sani Yahaya Jingir yana karantar da shirka ne da zakace ba'a taba yin musifa irinsa ba?
Shekaru 15 da s**a wuce duk wani mai hankali ya ga abinda B0k0 Har@m s**ayi, anyi amfani da B0k0 Har@m domin a yaki Musulunci da Musulmai a hana yaduwar addinin Musulunci, manyan Malaman Kasarnan masu fada aji sai da s**a dena magana akan makircin B0k0 Har@m saboda tsoron za'a kashe su, amma Sheikh Sani Yahaya Jingir bai yi shiru ba
S**a kai masa harin B0mb a Masallacinsa na 'Yan Taya Jos da nufin ha|akashi, mutum sama da dari aka ka$he a lokacin harin, hakan bai sa ya tsorata ba, ya rubuta Littafi mai taken BOKO HALAL NE KARANTA DA SUNAN ALLAH, anya anyi adalci idan akace wannan Malami masifa ne da ba'a taba yin irinsa ba?
Sai masifar yaki da Musulunci da ta biyo bayan B0k0 Har@m shine annobar Korona, kusan Malaman Kasarnan sai da aka rufe bakinsu, aka hana Sallar Juma'a da khamsu salawat, aka rufe Masallatai, amma Sheikh Sani Yahaya Jingir ya dinga magana yana yakarsu yana cewa makirci ne, shin ya cancanta a kwatantashi da masifa?
Akwai abinda baka fahimta ba game da Malam akan ra'ayinsa na siyasar Demokaradiyya, Wallahi da ka ga ya nace akan Muslim Muslim ticket tsananin kishin Musulunci ne ya sa shi yin haka, kuma iya fahimtarsa kenan cewa Muslim ticket addini ne, duk da su kansu 'yan siyasar sunce ba addini bane, strategies ne don su ci zabe kawai
Malam Adam Ashaka maganarka akan Malam kuskure ne kuma tayi tasiri sosai, ina baka shawara ka janye kalamanka akan Malam sannan ka nemi yafiyarsa
Muna fatan Allah Ya bamu ikon gyara kuskuren mu gaba daya