
15/11/2022
YAN KWANA KWANA NA KOKARIN KASHE GOBARA A KASUWAR SUNGA:
Gobarar ta tashi ne yanzun nan a kasuwar kayan masarufi ta Singa da ke Kano.
Kawo yanzu dai ba a san musabbabin tashin wutar ba, to sai dai wani mai shago a kasuwar ya shaida wa wakilin mu cewa wutar lantarki ce ta haddasa tashin gobarar.