Hazaka TV

Hazaka TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hazaka TV, Media/News Company, Gwarimpa, Abuja.
(1)

WATA SABUWA: Za mu janye goyon bayanmu ga APC idan ba ta cire Ali Modu Sherrif daga cikin kwamitin tallar Tinubu ba Wata...
27/08/2026

WATA SABUWA: Za mu janye goyon bayanmu ga APC idan ba ta cire Ali Modu Sherrif daga cikin kwamitin tallar Tinubu ba

Wata kungiyar magoya bayan APC da ke yakin neman sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 ta yi barazanar janye goyon bayan da take ba shi bisa radin kanta, idan har tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ci gaba da kasancewa cikin tsarin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Kungiyar mai suna Grassroots Movement for Tinubu Continuity Come 2027, ta bayyana wannan gargadi ne cikin wata takardar korafi mai dauke da kwanan watan 25 ga Agusta, 2026, wadda ta aika wa shugaban jam’iyyar APC na kasa, tare da kwafin takardar zuwa fadar shugaban kasa.

Kungiyar ta ce korafinta ya ta’allaka ne musamman kan nada Sheriff a matsayin mai kula da yakin neman zaben APC na shiyyar Arewa maso Gabas, a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar domin zaben 2027.

Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Sani Ahmad Zangina, ya ce kungiyar na nan daram kan kudirinta na ganin an sake zaben Tinubu, amma ba za ta iya ci gaba da gangamin neman masa goyon baya ga talakawa ba muddin wannan tsari bai sauya ba.






DA DUMI-DUMI: Zan bawa Tinubu Kuri'a Miliyan 20 daga Arewa Matawalle, Ya sake jaddada Alkawarinsa Ga Tinubu. Bayan dawow...
26/08/2026

DA DUMI-DUMI: Zan bawa Tinubu Kuri'a Miliyan 20 daga Arewa Matawalle, Ya sake jaddada Alkawarinsa Ga Tinubu. Bayan dawowa gida Najeriya.

‎Dubban magoya baya sun fito domin tarbar Ƙaramin Ministan Tsaro, Dr. Bello Matawalle, bayan dawowarsa gida Najeriya, lamarin da ya sake jawo zazzafar muhawara kan ƙarfin siyasar Matawalle da kuma yiwuwar samun gagarumin goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

‎Hotuna da bidiyoyin taron sun nuna yadda magoya baya s**a fito cikin ɗimbin jama'a domin tarbar tsohon gwamnan jihar Zamfara. Wannan gagarumar tarba ta sa wasu masu sharhi da magoya bayan jam'iyyar APC ke cewa alkawarin tattara kuri'u miliyan 20 daga Arewa domin Tinubu na iya zama abin da za a iya cimmawa, idan aka yi la'akari da irin ƙarfin da manyan jiga-jigan siyasar Arewa ke da shi a matakin ƙasa da ƙasa.

‎A kwanakin baya, wata ƙungiyar magoya bayan Tinubu mai suna Northern Vanguard for Asiwaju ta bayyana aniyarta ta taimaka wajen tattara akalla kuri'u miliyan 20 ga shugaban ƙasar a zaɓen 2027, tana mai bayyana cewa za ta dogara da tsarin siyasa da magoya bayan Matawalle da sauran jiga-jigan APC a fadin Arewa.

‎Amma babbar tambayar da mutane ke yi ita ce: Shin taron dubban mutane domin tarbar Matawalle yana nufin za a iya sauya wannan taro zuwa kuri'u miliyan 20?

‎Amsar ita ce, yana yiwuwa a siyasance, amma ba abu ne mai sauƙi ba.

‎Tarbar jama'a na iya nuna farin jini, tasiri da ƙarfin tsarin siyasa, amma zaɓe yana buƙatar abubuwa da dama. Dole ne a tabbatar da rajistar masu zaɓe, fitowarsu ranar zaɓe, haɗin kai tsakanin manyan jiga-jigan siyasa, da kuma yadda jama'a ke kallon manufofi da ayyukan gwamnati.

‎Matawalle dai ya sha bayyana cewa yana da yakinin Arewa za ta nuna goyon bayanta ga Tinubu a 2027, yana mai cewa ayyukan gwamnati a yankin za su iya ƙara wa shugaban ƙasar farin jini.

Ku Sabunta Goyon Bayan ku ga Tinubu Sakon Shugaban Kungiyar izala reshen jos ga musulmi..~ Sheikh Yahaya Jingir
26/08/2026

Ku Sabunta Goyon Bayan ku ga Tinubu Sakon Shugaban Kungiyar izala reshen jos ga musulmi..

~ Sheikh Yahaya Jingir

17/08/2026

Da Gwamnatin Nigeria Za Ta Ba Yan Kasuwa Su Gina Hanyoyi A Kasar Sai Su Dinga Amsar Kudi A Kowace Rana Da Matsalar Lalacewar Hanya Ta Kau A Nigeria...

~ Alh Balarabe Shehu Illelah Tsohon Shugaban Hukumar NBC Na Nigeria....

‎Ana Zargin Shugaban Karamar Hukumar Kabo da K**a Wani Matashi Saboda Bayyana Ra’ayinsa na Siyasa‎Ana zargin Shugaban Ka...
11/08/2026

‎Ana Zargin Shugaban Karamar Hukumar Kabo da K**a Wani Matashi Saboda Bayyana Ra’ayinsa na Siyasa

Ana zargin Shugaban Karamar Hukumar Kabo ta Jihar Kano, Hon. Lawan Najume Kabo, da hannu wajen k**a da tsare wani matashi mai suna Aliyu Muhammad Haruna, wanda aka fi sani da Babagana, bisa zargin ya bayyana ra’ayinsa kan wasu batutuwan siyasa.

An bayyana hakan ne cikin wata takardar ƙorafi mai ɗauke da kwanan wata 10 ga Agusta, 2026, wadda aka miƙa wa Sufeto-Janar na Rundunar ’Yan Sandan Najeriya a Hedikwatar ’Yan Sanda da ke Louis Edet House, Abuja.

Takardar ta ƙunshi ƙorafi kan k**awa da tsarewa ba bisa ka’idar doka ba, da kuma zargin amfani da ikon ’yan sanda ba daidai ba wajen k**a matashin.
‎A cikin ƙorafin, lauyoyin Aliyu Muhammad Haruna sun bayyana cewa:

“Mu ne lauyoyin Mr. Aliyu Muhammad Haruna (Babagana), kuma bisa umarninsa, mun rubuto wannan wasiƙa domin sanar da ku halin da ya dabaibaye k**awa da tsare shi da jami’an ’yan sanda da ke aiki a Sashen ’Yan Sandan Kabo.”

A cewar takardar, lauyoyin sun yi zargin cewa k**awa da tsare Babagana ya faru ne bisa umarni ko sa hannun Shugaban Karamar Hukumar Kabo, Hon. Lawan Najume Kabo.

‎LauyoyinLauyoyin sun kuma nemi a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa domin gano halaccin k**awa da tsarewar, yanayin da ya kai ga jami’an ’yan sanda ɗaukar matakin, da kuma rawar da Shugaban Karamar Hukumar ya taka a cikin lamarin.

Takardar ta bayyana Babagana a matsayin ɗan Najeriya, ɗalibi kuma ɗan asalin Jihar Kano, tare da cewa, bisa bayanan lauyoyinsa, ba shi da wani tarihin aikata laifi da ya shafi wannan ƙorafi.


A ranar 3 ga Mayu, 2026, da misalin ƙarfe 1:00 na rana, jami’an ’yan sanda da ke aiki a Sashen ’Yan Sandan Kabo sun je gidan Babagana da ke Gidan Alh. Haruna, Kabo, inda s**a k**a shi tare da kai shi ofishin ’yan sanda.

A cewar Babagana, jami’an sun ɗauki matakin ne bisa umarni ko sa hannun Hon. Lawan Najume Kabo, Shugaban Karamar Hukumar Kabo.

Takardar ta ƙara da cewa Babagana ya taɓa samun rashin jituwa da Shugaban Karamar Hukumar kan wasu batutuwan siyasa da kuma yadda ake gudanar da harkokin ƙaramar hukumar.

Kafin k**a shi, Babagana ya kasance yana bayyana ra’ayoyinsa da rashin amincewarsa da wasu manufofi ko matakan gudanarwa da s**a shafi Shugaban Karamar Hukumar.

‎A halin yanzu, lauyoyin matashin suna neman a gudanar da bincike domin tabbatar da ainihin dalilin k**awa da tsare shi, da kuma gano ko an yi amfani da ikon ’yan sanda ba bisa ka’ida ba.

01/08/2026

Ba'a Tsohon Dan Jarida Ba'a Tsohon Likita Kuma Ba'a Tsohon Lauya...

Takaitaccen Tarihin Alh Balarabe Shehu Illelah Tsohon Shugaban Hukumar Dake Kula Da Ayyukan Gidajen Yada Labarai Da Kafafen Sadarwa Ta Nigeria Wato (NBC).....

Mun Tattauna Kan Muhimman Alamura Da S**a Shafi Kasa Tare Da Alamuran Yau Da Kullum.....

Cikakkar Firar Na Nan Tafe Insha Allah.....

INNALILLAHI 😭Bawan Allah ya Dawo Daga Aiki Sai Yayi Dare, bayan yazo gida chikin dare Yayita Bugawa Kofa a Bude mashi Am...
29/07/2026

INNALILLAHI 😭

Bawan Allah ya Dawo Daga Aiki Sai Yayi Dare, bayan yazo gida chikin dare Yayita Bugawa Kofa a Bude mashi Amma matarshi Taki Budewa Wai Meyasa Zaiyi Dare Haka,

Shine bawan Allah Yakoma Cikin Motarsa Ya Kulle Ya Kwanta, safiya tayi akaga Mutum kwanche a motor Bai fitowa Akai tunanin lafiya har yanzu shiru ya Dade a chikin motor din aka fahimchi Bai motsi bawan Allah

Ashe rabon sai dai a Sare Kofar Motar A Fito Dashi Babu Rài.

Yanzu kuna ganin za'a iya k**a wannan matar da laifin kisan Kai ko ko a dauki mutuwar a matsayin natural death

Yan Jahohin Kano, Jigawa da Katsina kuna ina ga wata damar tazo da fatan Allah ya baiwa masu rabo Sa’ah.       Asiwaju B...
11/07/2026

Yan Jahohin Kano, Jigawa da Katsina kuna ina ga wata damar tazo da fatan Allah ya baiwa masu rabo Sa’ah.







Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Innalillahi wa inna ilaihi rajiuun. 😭😢😥Allah yayiwa Abokin mu Aliyu Magaji  Rasuwa yanzu, Saka makon MATAR sa ta Caka ma...
11/07/2026

Innalillahi wa inna ilaihi rajiuun. 😭😢😥
Allah yayiwa Abokin mu Aliyu Magaji Rasuwa yanzu, Saka makon MATAR sa ta Caka masa Huka a ciki a yanzun nan kuma anan take ya cika. Abin ya faru ne a cikin garin BIRNIN YERO TASHA dake Karamar Hukumar Igabi kaduna state.

Aliyu mutumin kirki ne kuma haziki ne wajen Neman abin kasa, Abin takai ci ma ya sayo shinkafar da zasuci ne da dare, Hasbunallahu wa ni'imal wakeel.

Allah mai iko Ayau jummuat Aliyu ya kasan ce a Online har karfe 4:36 ashe kawai lokacin sa yake jira, Munyi hira dashi k**ar yadda zaku gani da idan ku, Yana man maganar yanasan yayi karin zabe, nashi ya bace , nace masa Abokina zanzo mutation wajen yin Nima nawa ya samu matsala.

Allah sarki, Aliyu a tare mukai Primary School, kuma mukai Secondary school, Munaje gidansu naci tuwo alokutan baya haka Malika shima yakan zo muci nawa. Allah Madau kakin sarki ka gafarta wannan bawa naka. ka yafe masa kura kuran sa.

Ina kira ga Matasa idan zamuyi AURE wallahi kada mu auri kyau kawai, Mu duba Tarbiyya, Asali, da kuma duk qbin da ya dace a Musulunci sai Allah ya taimakeku.

Kuma a karshe ina kira da Hukuma Dan Dallah Dan san Annabi abiwa wannan bawa Hakkinsa, Yanada yara kananu😭😢 matar sa ta maidasu Marayun karfi da yaji, Allah Ubangiji ya saka masu. Allah Ubangijin ya isar masu.

Rabilu Musa Abdullahi Kwarau✍🏻

Address

Gwarimpa
Abuja

Telephone

+2348103599774

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hazaka TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hazaka TV:

Shortcuts

Share