
27/04/2025
JANA'IZA CIKIN HOTUNA:
Miliyoyin Al'umma Musulmai Ne S**a Halarci Sallar Jana'izar Sheikh Mai Nasara Liman, Shugaban Majalisar Malamai Na Kungiyar Fityanul Islam. A Filin Idin Mallawa Dake Tudun Wada Zari'a.
A Yau Lahadi Da Misalin Karfe Biyu Da Rabi Na Rana 2:30pm Aka Gabatar Da Jana'izar Shugaban Majalisar Malamai Na Fityanul Islam Sheikh Mai Nasara Liman Tudun Wadan Zari'a, Wanda Allah Ya Karbi Rayuwar Shi A Jiya Asabar Bayan Fama Da Rashin Lafiya.
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Amb Malam Ahmad Nuhu Bamalli, Yana Daya Daga Cikin Sarakunan Da S**a Halarci Jana'izar, Tare Da Manyan Shehunai, Malamai, Da Shuwagabannin Fityanul Islam Na Kasa. Daga Ko Ina A Fadin Duniya.
SHEIKH SALAHUDDEN IBRAHIM INYASS Shine Ya Jagoranci Sallar Jana'izar A Filin Idin Mallawa Dake Jos Road Tudun Wada Zari'a.
β Abubakar H Sirrinbai