17/08/2025
LABARI MAI CIKE DA DARUSSA A RAYUWA!
Tsakanin Ibn Hajar Da Malaminsa Al-Haisami.
Alhafiz Nuruddin Al-Haisami Babban Malamin Hadisi ne, kuma Malami ne ga Alhafiz Ibnu Hajar Al-asƙalani, sannan Aboki ne na kusa ga Babban Malamin da Ibnu Hajar ya ke matuƙar tutiya da alfahari da shi a duniya, wato Alhafiz Abdurrahim Al-iraƙi. Allah Ya yi musu Rahama.
Ibn Hajar a cikin littafinsa (Inba'ul Gumr) Ya bayyana irin yadda wannan Malami na sa Alhafiz Nuruddin Alhaisami yake ƙaunarsa ya ke girmama shi, ya ke nuna fifikon Ibnu Hajar da tumbatsarsa a ilimin Hadisi, Ibnu Hajar ya ke cewa:
كان يودني كثيرا ويشهد لي بالتقدم في هذا الفن
Alhaisami ya rubuta bakandamen littafinsa sananne wanda ba shi da kamarsa, wato littafin (Majma'uzzawa'id Wa Manba'ul Fawa'id) sai Ibnu Hajar ya ci karo da wasu kura-kurai da matsaloli a cikin wannan Littafi na Malaminsa Alhaisami. Nan ta ke sai Ibn Hajar ya fara tattara kura-kurai da matsalolin da ya samu a littafin Malamin na sa, ai kuwa sai labari ya isarwa Malaminsa Alhaisami cewa Ibn Hajar ya samu kura-kurai da yawa a littafin nan naka da ka ke ji da shi kuma ka sha matuƙar wahala wajen rubuta shi, kuma Ibn Hajar ya fara aiki a kan haka domin fito da kura-kuran nan da bayyana su ga mutane domin yin gyara a gare ka.
A lokacin da Alhaisami ya samu wannan labari, sai ya nuna rashin jin daɗi dangane da haka, ya nuna bai so haka ba, hankalinsa ya tashi har ya fito ya bayyana haka a fili! Shi kuwa shi Ibn Hajar da ya ga haka, ba tare da jan lokaci ba sai ya ajiye wannan aiki, ya tsaya chak! Ya kame hannayensa daga cigaba da tattara waɗannan kura-kurai. Ga abin da Ibnu Hajar yake cewa a littafinsa (Inba'ul Gumr Bi Abna'il Umur)
وكنتُ قد تتبعتُ أوهامه في كتابه مجمع الزوائد فبلغني أن ذلك شقَّ عليه فتركتُه رعاية له.
Ya ce: Na kasance na bibiyi kura-kuransa a littafinsa (Majma'uzzawa'id) sai labari ya same ni cewa hakan ya ƙona masa rai, sai na bari na daina saboda kula da hakkinsa da girmama shi.
Daga Darasin da za mu dauka a