10/08/2026
ZAKAT DA WAQF: MANYAN MAKAMAI WAJEN YAKI DA TALAUCI DA YUNWA
Masana Sun Jaddada Muhimmancin Inganta Tsarin Gudanar da Zakat da Waqf a Sokoto
An bayyana Zakat da Waqf a matsayin muhimman hanyoyin magance talauci da yunwa tare da inganta rayuwar al’umma da bunkasa tattalin arziki.
Wannan bayani ya fito ne daga Farfesa Irfan Syauqi Beik, Shugaban Faculty of Economics a IPB University, Bogor, Indonesia, a yayin bikin bude taron horas da ma’aikata na tsawon kwanaki hudu kan Gudanar da Zakat da Waqf, wanda IsDB/SOZECOM ta shirya.
A cikin gabatarwarsa mai taken “International Experiences and Success Stories in Islamic Social Finance,” Farfesa Irfan ya bayyana irin muhimmiyar rawar da Zakat da Waqf ke takawa wajen bunkasa tattalin arziki, ci gaban al’umma, kyautata dabi’u da kuma inganta harkokin ilimi.
Ya ce idan aka samu ingantaccen tsarin tattara da rarraba Zakat, tare da bunkasa ayyukan Waqf, za a iya samar da gagarumar gudunmawa wajen rage talauci da yunwa tare da taimaka wa masu karamin karfi.
HORASWA DON KARA KWAREWAR MA’AIKATA
A nasa jawabin maraba, Shugaban Kwamitin Shirya Taron kuma Executive Chairman na SOZEA, Malam Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato, ya ce taron ya samar da muhimmiyar dama wajen inganta tsarin gudanar da Zakat da Waqf.
Ya bayyana cewa horaswar za ta kara wa jami’an Zakat da Waqf kwarin gwiwa da kwarewa, tare da karfafa musu damar taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arziki da rage talauci a matakin kasa da kasa.
GWAMNATIN SOKOTO TA SHA ALWASHIN GOYON BAYA
A nasa bangaren, Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Sokoto, Dr. Jabir Sani Maihulla, wanda Sakataren Dindindin na ma’aikatar, Dr. Muhammad Sani Labaran, ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da jajircewa wajen bunkasa harkokin addinin Musulunci a jihar.
Ya yabawa wadanda s**a shirya taron bisa kawo irin wannan muhimmin shiri zuwa Sokoto, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin jihar a shirye take ta tallafa wa shirye-shiryen da ke inganta zaman lafiya, jin dadin al’umma da ci gaban tattalin arziki.
SULTAN YA TUNATAR DA MUHIMMANCIN ZAKAT
Shi ma Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda Dagacin Kilgori, Alhaji Muhammad Jabbi Kilgori, ya wakilta, ya tunatar da al’ummar Musulmi cewa Zakat na daga cikin ginshikan Musulunci guda biyar.
Sarkin ya yi kira ga Musulmi da su ci gaba da tsarkake dukiyoyinsu ta hanyar bayar da Zakat k**ar yadda koyarwar Musulunci ta tanada.
Ya kuma karfafa gwiwar Musulmi da su kafa tare da tallafa wa ayyukan Waqf, domin taimakawa wajen bunkasa tattalin arziki da rage talauci a cikin al’umma.
MANYAN BAƘI SUN HALARTA
An gudanar da taron ne a Dan Kanni Guest Inn, Sokoto, inda manyan baki da wakilan hukumomi daban-daban s**a halarta, ciki har da wakilan Ma’aikatun Harkokin Mata da Yara, Jin Dadin Al’umma, da Humanitarian Affairs, baya ga sauran manyan baki daga cikin gida da wajen Najeriya.
Taron na daga cikin kokarin karfafa kwarewar jami’an Zakat da Waqf, tare da samar da ingantaccen tsarin da zai taimaka wajen rage talauci, yunwa da matsalolin tattalin arziki a cikin al’umma.