08/11/2025
Shin ya dace mabiyin Sheikh Zakzaky (H) ya aika masa da budaddiyar wasika ta social media?
A cikin tsarin tarbiyyar Musulunci, akwai babbar dokar da take koyar da ladabi da girmamawa ga shugabanni na addini. Sheikh Zakzaky (H) ba kawai jagora bane, amma malami ne wanda ya gada ilimi daga makarantar Ahlul Baiti (AS).
Saboda haka, duk wata mu’amala da ake yi da shi – musamman a bainar jama’a – ya kamata ta kasance cikin ladabi, natsuwa, da hikima.
Dalili daga Alƙur’ani:
> "Ya ayyuhan ladheena aamanu, la tarfa’u aswaatakum fawqa sawti nabiyy..."
“Ya ku waɗanda kuka yi imani, kada ku ɗaga murya a gaban Annabi, kuma kada ku yi magana da shi kamar yadda kuke magana da juna…”
(Suratul Hujurat 49:2)
Wannan aya ta koyar da cewa, magana ko mu’amala da shugaba na addini tana da adabi na musamman.
Sheikh Zakzaky (H) yana cikin jerin malamai masu daraja waɗanda suke bin tafarkin Annabi (S) da Ahlul Baiti (AS).
Saboda haka, aika masa da budaddiyar wasika ta social media — wadda duniya za ta gani — ba hanya ce ta ladabi ba, musamman idan abin yana da nauyin gyara ko shawara.
Hadisin Ahlul Baiti (AS):
Imam Ja’afar al-Sadiq (AS) ya ce:
> “Wanda ya ba shugabansa shawara a bainar jama’a, to ya raina shi. Amma wanda ya ba shi shawara cikin sirri, to ya girmama shi.”
(Al-Kafi, Juz’i na 2)
Wannan yana nuna cewa, duk shawara, tambaya, ko ra’ayi da ke da alaƙa da jagora, ya kamata ta kasance cikin sirri da ladabi, ba a bainar jama’a ko ta social media ba.
Darasi ga mabiyan Sheikh Zakzaky (H):
Kada mu mayar da social media hanyar magana kai tsaye da Jagora.
Idan akwai bukatar isar da saƙo, ayi hakan ta tsarin hukuma na harkar Musulunci (kamar Amiran gari ko Sakataren Media).
Kada mu bari “ra’ayin kai” ya sa mu karya tsarin da Ahlul Baiti s**a kafa na girmama shugaba da kiyaye martabarsa.
Daga karshe:
Wanda ya san darajar Sheikh Zakzaky (H) ba zai rubuta masa budaddiyar wasika ta social media ba.
Ladabi da natsuwa su ne alamar biyayya da gaskiya a cikin tafarkin Jagora.
Girmama Jagora alama ce ta fahimta, kuma yin shiru a gabansa ibada ce.
Shahidanmu TV