07/11/2025
GODIYA TA MUSAMMAN GA MAI GIRMA SARKIN KOKO, KUNGIYAR CIGABAN YANKIN KOKO (KODA), DA CIYAMAN NA KOKO/BESSE AKAN DAWOWAR WUTAR LANTARKI (NEPA) A GARIN KOKO
Alhamdulillah! Bayan dogon lokaci da Garin Koko ke fama da matsalar rashin wutar lantarki (NEPA), cikin ikon Allah, wannan matsalar tazo karshe. A halin yanzu wutar lantarki ta dawo a wasu sassa na Garin Koko, yayin da ake ci gaba da gyare-gyare a sauran yankuna.
Wannan ci gaban mai matuƙar muhimmanci ya samu ne sakamakon jajircewa, kulawa, da sadaukarwa daga Mai Girma Sarkin Koko, Alhaji Mohammed Bello Koko II, tare da haɗin gwiwar Kungiyar Cigaban Garin Koko (KODA) da Shugaban Karamar Hukumar Koko/Besse, Hon. Sirajo Usman Koko.
Mai Girma Sarkin Koko, tare da shugabannin KODA da kuma Ciyaman na Karamar Hukumar, sun nuna kishin al’umma ta hanyar ba da goyon baya da tallafi wajen tabbatar da dawowar hasken wuta a Koko. Allah (SWT) Ya saka musu da alkhairi, Ya ƙara musu lafiya, nisan kwana, da nasarori masu albarka – Amin.
Wannan Nasarar ta Samu ne tun a ranar 14/10/2025, Mai Girma Sarkin Koko ya zauna da Kwamitin NEPA na Garin Koko domin tattauna matsalolin da s**a haifar da rashin wutar lantarki a yankin. Kwamitin ya bayyana cewa adadin kudin da ake buƙata domin gyaran wutar ya kai Naira Miliyan 2.5 (₦2,500,000).
Ba tare da ɓata lokaci ba, Mai Girma Sarkin Koko ya amince da bayar da cikakkiyar gudunmawar wannan adadi ta hannun Gidauniyar Sarkin Koko – Malam Musa Foundation. Wannan taimako mai dimbin albarka ya zama ginshiƙi wajen tabbatar da dawowar wutar lantarki ga daukacin al’ummar Masarautar Koko. Alhamdulillah, yanzu an samu dawowar hasken wuta a yankin Koko.
Wannan ba shi ne karo na farko da Mai Girma Sarkin Koko ke bayar da irin wannan gudunmawa ba. Tun a baya yana taka muhimmiyar rawa wajen gyaran da kuma kula da harkokin wutar NEPA a Garin Koko. Wannan ya nuna irin kishin sa, tausayi, da kulawarsa ga ci gaban al’ummar sa baki ɗaya.
Hakika, samun Mai Girma Sarkin Koko, Alhaji Mohammed Bello Koko II, a matsayin jagora babbar ni’ima ce daga Allah ga al’ummar Koko da kewaye. Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya saka masa da alkhairi, Ya ƙara masa lafiya, da kuma nasarori masu ɗorewa a dukkan al’amuransa.
Godiya ga Shuwagabannin KODA
Haka kuma, muna mika godiya ta musamman ga Kungiyar Cigaban Garin Koko (KODA) bisa jajircewa da haɗin kai wajen tabbatar da wannan ci gaba. Allah Ya saka musu da alkhairi, Ya ƙara musu jagoranci, fahimta, da haɗin kai a dukkan ayyukansu na alheri.
Daga:
Ciroman Koko Media Team
07/11/2025