02/08/2025
Labari Da Ɗumi Ɗumi:
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya dakatar da kwamishinan sufurin jihar Hon Namadi, dakatarwar ta fara aiki nan take.
Biyo bayan Hukumar DSS ta Gano Dala dubu Talatin $30,000 aka bawa Kwamishinan Sufurin jihar Kano domin Belin dilan muggan kwayoyi.
A wani rahoto da Jaridar Daily Nigerian ta wallafa na cewa Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Namadi, ya karɓi cin hancin dala 30,000 daga hannun dilan muggan kwayoyi -Sulaiman Danwawu domin ya tsaya masa, a cewar wani rahoto da hukumar tsaro ta farin kaya, SSS ta gabatar.
Mista Namadi, wanda ‘yan sanda s**a taba shelanta nemansa da laifin zamba, sannan kuma aka tuhume shi da aikata laifuka a shekarar 2013, Gwamna Abba Yusuf ya nada shi a matsayin kwamishina kuma mamba a majalisar zartarwa ta jihar Kano.
Majiyoyi a hedikwatar SSS da ke Abuja sun shaida wa wannan jarida cewa hukumar ta yi bincike a asirce kan badakalar karbar belin sannan ta kuma ba da shawarar korar kwamishinan ga gwamnan.
Rahoton ya ce an biya kwamishinan dala 30,000 kafin ya amince ya tsaya a matsayin wanda ya yi kaurin suna wajen safarar miyagun kwayoyi.
Bayan da jama’a s**a yi Allah-wadai da lamarin, gwamnan ya kafa kwamitin bincike don binciki badakalar badakalar da za ta tsaya masa tare da mika rahoto cikin mako guda.