19/05/2026
Siyasa ta koma gidan malamai
A yau siyasa ta sauya salo. A da mutane suna kallon malamai tamkar ba ruwansu da harkar shugabanci ko siyasa, amma yanzu al’umma ta fahimci cewa malamai su ne hasken da ke nuna hanya idan al’umma ta rikice.
Shaikh Sani Yahaya Jingir ya kasance cikin manyan malaman da s**a tsaya tsayin daka wajen ƙoƙarin haɗa kan musulmai tare da nuna muhimmancin haɗin kai a cikin al’umma. Yayin da batun Muslim-Muslim ya taso, malam ya yi amfani da hikima da ilimi wajen bayyana cewa manufarsa ita ce zaman lafiya, haɗin kai, da kare muradun addini da al’umma baki ɗaya.
Mutane da dama sun fahimci cewa malamai ba wai neman mulki suke yi ba, a’a suna ƙoƙarin ganin an samu shugabanci nagari wanda zai kawo ci gaba, tsaro, da mutunta addini. A duk lokacin da malamai s**a yi magana akan siyasa, suna yin hakan ne saboda damuwar da suke yi akan rayuwar talakawa da makomar ƙasa.
Shaikh Sani Yahaya Jingir ya nuna jarumta wajen faɗin abin da ya yi imani da shi ba tare da tsoron s**a ko matsin lamba ba. Wannan ya sa mutane da yawa suke ganin siyasa ta koma gidan malamai, domin malamai suna ƙara shiga cikin wayar da kan jama’a akan muhimmancin zaɓar shugabanni na gari masu tausayi da adalci.
Hakika, al’umma tana buƙatar malamai masu faɗin gaskiya, masu kira zuwa zaman lafiya da haɗin kai. Domin idan malamai s**a yi shiru a lokacin da al’umma take cikin ruɗani, to wa zai nuna hanya?
Allah ya ƙara wa malamai hikima da ikon faɗin gaskiya, ya kuma ba ƙasarmu shugabanni na gari masu kishin talaka da addini.