19/09/2021
🌹 littafin abokin fira 🌹
📝
Ramin mugunta ka ginashi gajere 🤕
Wani bawan allah ne talaka matar takeyin wani abinci da ake kiransa da chukui, wanda akeyinsa da daskararren nono 😋 shi kuma ya siyarma dawani me shago dayake unguwarsu, takan mulmula ya koma kaman qwallo, saita siyar masa, shi kuma saiya yayyanka shi a gram 10 yasiyarwa da mutane 👐
Watarana me shago yayi shakkan awon chukui da ake yimasa, domin yaga bayacin riba yadda yakamata 😕 saiya dauko skeli ya aunashi, saiya tararda shi gram 90 ne🙁 be chika 100 yadda yakamata 🤦 sai wnn me shagon yaji haushi 😡 sannan yajira zuwan wnn dattijon da safe, zuwansa keda wuya saiya rufeshi da fada yana cema azzalimi macuci 😥
Bayan ya qare fadansa, sai dattijon nan yace kayi haqury wlhy nida matata bamusan kilo ba 😥 amma alokacinda zamu fara sana'ar chukui munzo munsiya skeli awajenka, sannan muka siya sugar loka 1, kuma akullum da wnn skelin muka aunawa 😕 sai me shagon nan yayi muzu muzu yana zare ido yanajin kunya 😒 kuma yagano cewa cutarda yake yiwa mutane ne aka gano shi
Darasin labari 📝
Idan zaka gina ramin mugunta, to ka gina dai dai kai 👌 wataqila kai zaka fada ciki baka sani ba 🤕
Dayawan masu yin laifi sunada uzuri rashin sani, ko kasawar fahimta 👌ko wani abu me kamada wnn 👐
Ka binciki mutum kan laifinsa, wataqila kaima kanada laipi aciki wanda bakasani ba 👐
Ngd sosai da lokutanku 👐🌹