16/08/2025
Hotuna: Ziyarar dubiya da Shugaban Izala Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau da tawagarsa s**a kai ga Daraktan agaji na Izala mai helkwata a Jos, Alh Isa Waziri Gombe, domin rashin lafiya da yake fama da shi a gidansa dake birnin Gombe. Cikin Tawagar shugaban akwai shugaban majalisar Malamai na ƙasa, Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, babban sakataren ƙungiyar, Sheikh Dr. Muhammad Kabir Haruna Gombe, daraktan agaji na ƙasa, Sheikh Engr Mustapha Imam Sitti, Alaramma Ahmad Suleiman, Alaramma Nasiru Salihu Gwandu da shugaban JIBWIS na Jahar Gombe Engr Salisu Muhammad Gombe da sauran jama'a s**a raka Shugaban.
Allah ya bashi lafiya da sauran musulmai muminai masu lalura. Amin
Jibwis Nigeria