
15/07/2025
Na karɓi addinin Musulunci a wani Masallaci amma ana gama bani kalmar shahada na ɗauka wani zai ce in zo muje, kawai sai naga kowa ya watse ya bar ni ni kaɗai, sai na tashi na tafi gurin ƙawaye na musulmai sune s**a riƙa nuna min yadda ake bauta a addinin Musulunci suma sai na tambaye su suke faɗa min.
A unguwar da nake zama nike zuwa inyi aiki in samu abinda zan ci kuma duk wanda ya fito zai aureni sai ƴan unguwar su faɗa masa ni banda uwa kuma ban da uba sannan musulunta nayi koda baƙo ne bai sanni ba daga ranar baya ƙara zuwa abun yana damu na sosai kuma na koma gidan iyaye na da niyyar zan koma addini na na kirista s**a sake koro ni s**a ce ba zasu yarda dani ba na rasa inda zan sa kaina.
Yanzu haka duk wanda na samu koda ba zai iya aurena ba matuƙar zai riƙe ni ya koya min addinin Musulunci to ba zan fita ba, akwai ƙawayena 5 da s**a ga na musulunta nayi nasarar jawo su zuwa addinin Musulunci suma sun karɓa amma saboda babu wanda ya iya riƙe su ya koyar dasu duk sun fita ni kaɗai ce har yanzu ban fita ba nima sabo da mahaifana sunƙi yarda dani—In ji ta
Da wannan muke kira ga musulman Nijeriya masu arziƙi, na tabbatar muna da masu kuɗi, me zai hana a samu wani katafaren wuri a buɗe cibiyar karɓar irin waɗannan bayin Allah dake musulunta a gina masauki ingantacce a riƙa basu abinci koda sau 2 ne safe da dare a ɗauki nauyin malamai su riƙa koyar da su addinin musulunci.
Ƴan'uwa kada fa mu manta gaba ɗaya dukkan Annabawan da ALLAH SWT ya aiko ba wani abu s**a zo yi duniya ba illa kira zuwa ga hanyar Allah, ANNABI MUHAMMAD SAW har haƙori an cire masa an kashe Sahabbansa duk a kan ɗaukaka kalmar Allah amma mu a halin yanzu gasu suna zuwa su musulunta amma sai a watsar da su, wallahi da MANZON ALLAH SAW zai dawo duniya yaga irin wannan abubuwan da sai yayi Allah wadai da mu.
Na tabba a cikin musulman Nijeriya akwai mutum ɗaya mai kuɗin da zai iya kafa wannan cibiyar.
Akwai ire irensu da Dama Yanzu haka wadanda ke Bukatar taimako, Wanda Allah yasa Yake da haki sai Yayi kokari Ya Taimaka masu Don Girman Allah.