11/08/2025
Gwamnatin Najeriya ta yi maraba da naɗin ƴar Arewa Maryam Bukar Hassan a matsayin jakadiyar zaman lafiya ta duniya.
A yau Litinin ne gwamnatin shugaba Tinubu ta karɓi baƙuncin fitacciyar mai waƙar baka Maryam Hasan wadda ta yi nasarar zama jakadiyar zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya. Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ne ya karbi bakuncin jakadiyar da tawagarta a fadar shugaban ƙasa inda ya bayyana farincikin gwamnati da shirinta na yin aiki da jakadiyar yar asalin Najeriya don ƙarfafa zaman lafiya a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.
Da yake jawabi ga tawagar ta Global Advocate for Peace ta Majalisar Dinkin Duniya, Shettima ya bayyana Maryam a matsayin mace mai tsayuwar daka wajen sadaukar da basirarta ga wanzar da zaman lafiya musamman a wata ƙasidarta mai taken 'Rikici bai da addini' "wannan ita ce Najeriyar da muke fata, ni a wurina ma wannan ƙasidar ce bakandamiyar Maryam" inji Shettima
Kazalika, Kashim Shettima ya jaddada tsayin dakar da Maryam ta yi na ganin abubuwa sun daidaita a mahaifarta wato jahar Borno duk da ƙalubalen da ta fuskanta a matsayin wani abin a yaba.
Mataimaki shugaban kasar ya tabbatarwa da Majalisar Dinkin Duniya goyon bayan gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu inda ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsu za ta yi duk mai yiwuwa wajen bai wa Maryam da ma sauran matasa goyon baya da tallafa musu.
“Ki kwantar da hankalinki Maryam, ba ke kaɗai ba ce, muna tare da ke, kuma duk wani goyon baya da k**e bukata, za mu ba ki shi" inji Shettima.
Tun da farko, shugabar tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya First Global Advocate for Peace, wato Maryam ta ce aikinta na farko shi ne ta isar da sakon zaman lafiya a duniya, tare da bugan ƙirjin wajen yin fiye da bayar da shawara a ɓangaren wanzar da zaman lafiya a ƙasarta Najeriya a fannin da ta fi ƙwarewa