Aisha haruna

Aisha haruna 😭wlh ina son Muhammadu Rasullullahi S A W. ♥️♥️♥️ ya Allah 🤲ka dauka rayuwata a bisa sunna Mazon Rahama S A W ❤❤❤
(4)

insha Allahu sanadiyar rubuta sunan Allah daya tak shizai zama sanadiyar yayewar Damuwarmu baki daya  🙏🥰
17/10/2025

insha Allahu sanadiyar rubuta sunan Allah daya tak shizai zama sanadiyar yayewar Damuwarmu baki daya 🙏🥰

17/10/2025
Nasiha zuwaga amarya da aka aure ta biyu ku ta uku ko ta hudu  1 Ki fara da niyya mai kyau.Ki yi aure ne domin neman yar...
17/10/2025

Nasiha zuwaga amarya da aka aure ta biyu ku ta uku ko ta hudu

1 Ki fara da niyya mai kyau.
Ki yi aure ne domin neman yardar Allah da kwanciyar hankali, ba don takara da wata mace ba. Idan niyyar ki ta gyaru, Allah zai sanya miki albarka.

2 Ki kasance mai tawali’u da nutsuwa.
Ki sani aure na tarayya ne, kuma dukkan matan suna da hakkinsu. Kada ki nuna girman kai ko raini ga wasu matan mijin.

3 Ki karɓi kaddarar Allah da farin ciki.
Allah ne ke rabon aure da ƙaddara. Idan kin samu matsayin mata ta biyu ko ta uku, ki gane wannan wata ni’ima ce da jarrabawa a lokaci guda ki rungumi ta da haƙuri da godiya.

4 Ki kula da mijinki da gaskiya da biyayya.
Ki yi masa biyayya a cikin abin da ya halatta, ki kula da bukatunsa da tsafta da ladabi. Wannan shi ne ginshikin zaman lafiya.

5 Ki guji ƙiyayya da hassada.
Kada ki kalli abokin aurenki da hassada. Kowa da rabonsa ne a wajen Allah. Ki maida hankali kan ƙaunar mijinki da kula da gidanki kawai.

6 Ki yawaita haƙuri.
Aure da yawa yana buƙatar haƙuri sosai. Ki yawaita istighfari da addu’a. Haƙuri yana kawo kwanciyar hankali da nasara.

7 Ki kula da sirrin gidanki.
Kada ki bayyana sirrin mijinki ko maganganun da ke tsakanin ki da shi ga wasu. Sirri amana ce.

8 Ki zama mai ladabi da magana mai taushi.
Harshe yana iya gina aure ko rushe shi. Ki rika magana cikin ladabi, musamman idan an samu saɓani.

9 Ki riƙe ibada sosai.
Ki tsare salla, ki yawaita karatun Qur’ani, addu’a da istighfar. Mata mai ibada tana samun nutsuwa da daraja a wajen mijinta.

10 Ki roƙi Allah albarka da zaman lafiya.
Rikici a cikin aure da yawa yana iya fitowa, amma da addu’a da imani, komai zai daidaita.

Addu’a mai kyau ga irin wannan amarya:

اللهم اجعل بيننا مودة ورحمة، وبارك لنا في زواجنا، واصرف عنا الشيطان والنزاع.

Ya Allah, Ka sanya soyayya da rahama a tsakanina da mijina, Ka albarkaci aurenmu, Ka nesanta shaidan da rikici daga garemu

Abu Ja'afar Assunny ✍️

17/10/2025

Ka mu'amalanci mutane da tarbiyyarka ba da tasu ba.

17/10/2025

Umarni da kyakykyawan Aiki sadaka ne hani da mummuna ma sadaka ne❤️

17/10/2025

Ya Ubangiji ina rokonka rayuwar da babu Nadama a cikinta 🤲

16/10/2025

Idan kanaso kayi mutunci a idon mutane kada kataɓa bada shawara a inda ba'a nemi shawararka ba.

JAN HANKALI GAMEDA SALLAR ASUBAH:```Sallar Asubah🌙 itace mafi Alheri Fiyeda Bacci, mu rage Barci Donmu ribanta da Gobenm...
16/10/2025

JAN HANKALI GAMEDA SALLAR ASUBAH:

```Sallar Asubah🌙 itace mafi Alheri Fiyeda Bacci, mu rage Barci Donmu ribanta da Gobenmu.```

*Barci Amsawar Zuciya ne Itakuwa Sallah Amsawar kiran Ubangiji ne*

```Shi Barci mutuwane Ita Kuwa Sallah Rayuwace```

*Shi Barci Hutune na gangar Jiki Sallah Kuwa hutuce na Ruhi*

```Shi Barci da Mumini da kafiri Duk Suna Yinsa. Ita Kuwa Sallah Muminine Kadai Yake yinta```

*Masu tashi lokacin Hudowar Alfijir sun Rabauta, Fuskarsu kuma ta Haskaka Goshinsu kuma Yayi Haske da Kyalli Lokacinsu kuma yayi Albarka,*

```Idan Kana cikinsu toh Ka godewa ALLAH. Daya Fifitaka, IdanKuwa baka cikinsu toh Ka Roki ALLAH Ya Sakaka a Cikin su```

*Amma menene yafi Alfijir🌙 kyau??*

Farillarsa {Sallar Asuba} zata Sakaka Acikin Kulawar Ubangiji. Sunnarsa (Rak'ataanil fajr) tafi Duniya 🌍 da Abindake Cikinta {Hadeeth}```

*Ita Sallah Asubah, da Mala'iku masu dutyn Dare da Mala'iku masu dutyn safe Duka suna Halartar ta,*

Ya kai Dan'uwa, Yake Yar'uwa kisani fah kaima kasani Duk Wanda Yarayu Akan wani abu, toh akansa zai Mutu, Wanda Ya Mutu akan wani Aiki kuma Akansa za'a tasheshi```

*Idan ka Karanta wannan sako kuma kayi aiki Dashi toh ka samu Ladan Aikin ka, idan kuwa katura ma wasu suma s**ayi Aiki Dashi toh Ladanka zai nunku A Wurin ALLAH inshaa Allah*

Kada ka 6oye ilimi, ka Bayyana shi, Zaka Samu Kyakkawan Sakamako, a wurin Allah Madaukakin sarki.

ALLAH YA KARBA MANA IBADUNMU, YASA MU DACE DUNIYA DA LAHIRA.

Mallam Ahmad tijjani yusuf guruntum

Idan ka ga mutum yana cikin damuwa, ka yi ƙoƙari ka gaya masa magana mai daɗi, mai ƙarfafa zuciya da sanya fata da natsu...
16/10/2025

Idan ka ga mutum yana cikin damuwa, ka yi ƙoƙari ka gaya masa magana mai daɗi, mai ƙarfafa zuciya da sanya fata da natsuwa, koda ƴan kalmomi ne. Bai fi ya ɗauke ka minti biyu ba, amma kalmomin za su iya zama a zuciyarsa har abada. Har yanzu ina tuna kalmomin da wasu s**a gaya min lokacin da nake cikin damuwa, kuma ba zan taɓa mantawa da su ba.


Isa Sadi

16/10/2025

Ina matukar Kaunarku Saboda ALLAH ina fatan nidaku ALLAH ya hada fuskokinmu a Aljannah firdausy Ya Hayyu Ya Qayyum 🤲🤲

16/10/2025

Wanna Gaskiya ne Malam

16/10/2025

Address

Abuja
900001

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Aisha haruna posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Aisha haruna:

Share