Al qurra'u Tv

Al qurra'u Tv Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Al qurra'u Tv, TV Channel, A4 B5 MIYANGO Close AMINA COURT ESTATE, Abuja.

*{ إِنَّ ٱلَّذِینَ یَتۡلُونَ كِتَـٰبَ ٱللَّهِ وَأَقَامُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنفَقُوا۟ مِمَّا رَزَقۡنَـٰهُمۡ سِرࣰّا وَعَلَانِیَةࣰ یَرۡجُونَ تِجَـٰرَةࣰ لَّن تَبُورَ }*🩷❤️🧡💛💔💖💘
FOR MORE YOU CAN REACH US THROU THIS NUMBER 08060604143 JAZAKALLAHU KHAIRAN

22/08/2025

Khudubar Juma'a Kai Tsaye daga Masallacin Juma'a na Jami'a Mallakar Jihar Gombe State

Tare da Sheikh Professor Dahiru Inuwa Ibrahim

28/SAFAR/1447HJRY
22/AUGUST /2025MLDY

JAMI'AR USMANU ƊANFODIYO DA KE SOKOTO TA SHIRYA MUSABAQAR MURNAR CIKA SHEKARU 50 DA KAFUWASanarwa!     Sanarwa!!      Sa...
22/08/2025

JAMI'AR USMANU ƊANFODIYO DA KE SOKOTO TA SHIRYA MUSABAQAR MURNAR CIKA SHEKARU 50 DA KAFUWA

Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!!

Jami'ar UDUS wacce ta cika shekaru 50 da kafuwa ta shirya wasu shiraruwa (Programs) domin murnar cikarta shekaru 50 da kafuwa

Wannan Musabaqa na daya daga cikin shirye-shiryen da aka tsara za'a yi domin wannan murna

Ita dai wannan musabaqah ɗaliban UDUS maza da mata da ke karatu halin yanzu ne kawai ke da damar musharaka a ciki a ɗayan wadannan matakai hudu:

1- Qira'o'i bakwai (القراءات السبع) tare da tambayoyin tafsir (Kalimat ko Almuyassar) na Hizifi 2 na karshen Qur'ani

2- Hizifi 60 da tafsir (Kalimat ko Almuyassar) ɗan takara na da zaɓi

3- Hizifi 60

4- Hizifi 10 tare da tambayoyin tajwidi

Za'a fara wannan musabaqah a ranar litinin 25/08/2025 zuwa Alhamis 28/08/2025
إن شاء الله
WURI: Centre for advanced science research and analytical service (CASRAS)
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
Main campus.

LOKACI:
Zaman safe: Daga karfe 10:00 na safe zuwa 1:00 na rana

Zaman yamma: Daga karfe 4:00 zuwa 6:00 na yamma

Ana gayyatar kowa da kowa

Sanarwa daga
Dr. M. K. Sabo
Sakataren kwamitin shirya musabaka

22/08/2025

Light of Guidance Youth Conference 2025

Taken Taro:
"Matasan Mu, Makomar Mu:
Rayuwa Da Manufa mai kyau ta hanyar amfani da Hasken Shiriya daga Allah"
Wurin Taro: National Mosque Conference Hall Abuja Nigeria.
Rana: LAHADI 24 WATAN AUGUST 2025
Lokaci: KARFE 9:00 NA SAFE ZUWA 6:00 NA YAMMA.
(MATA ZASU IYA HALARTA)
Allah ya bada iKon Halarta, Allah ya amfanar damu abunda zamu saurara daga bakin Manyan Malamai da Masana.
Aamin Yaa Rahman
Ahlul Qur'an TV KRYSTAL TV AL QURRA'U TV Prof. Mansur Sokoto, mni Professor Isa Ali Pantami Muhammad Kabir Haruna

📸Alhamdulillah📸Mun Tarbo Gwani Bilal Hamza Wakilin Musabuqar duniya 60+tafsirDaga sokoto zuwa MafaraTawagar Matasa ce Ah...
21/08/2025

📸Alhamdulillah📸

Mun Tarbo Gwani Bilal Hamza
Wakilin Musabuqar duniya 60+tafsir
Daga sokoto zuwa Mafara

Tawagar Matasa ce Ahlil Qur'an s**a tarbo Gwani Bilal hamza bayan samun gagarumar nasara da yayi a Musabuqar duniya da ta gudana a saudiyya

Fodio Online TV

ENGR. ABBA KABIR YA KARRAMA BUKHARI SUNUSI IDRIS 🌹📖 Alhamdulillah! ♥️Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Malam Eng...
21/08/2025

ENGR. ABBA KABIR YA KARRAMA BUKHARI SUNUSI IDRIS 🌹📖

Alhamdulillah! ♥️
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Malam Engr Abba kabir yusuf ta karrama ɗan asalin jihar Kano, Bukhari Sunusi Idris, wanda ya samu matsayi na uku a Gasar Alƙur’ani ta Duniya. 🌍📖

A wani gagarumin biki na tarbar gwarzon, gwamnatin jihar ta tura wakilai zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano domin tarar da shi tare da rakashi zuwa Gidan Gwamnati. 🕌🤲

Wannan nasara babbar alfahari ce ga Kano, ga Nigeria, da al’ummar Musulmi baki ɗaya. 🇳🇬✨




21/08/2025

KAI TSAYE KARATUN LITTAFIN SHARHUS SUNNAH

DARASI NA 64

DAGA MASALLACIN MUHAJIRINA WAL-ANSAR KADO FISH MARKET FCT

MAI GABATARWA MALAM USMAN HAMZA ALBAYAN IKARA

21st August 2025CE/ 27th Safar 1446AH

21/08/2025

KARATUN LITTAFIN SHARHIN RIYADUS SALIHEEN NA SHEIKH UTHAIMIN

DARASI NA 299

AYAU ALHAMIS
27 SAFAR 1447
21 AUGUST 2025


DAGA
MASALLACIN FEDERAL TEACHING HOSPITAL GOMBE.

Mutanan Abuja karku Bari a baku labari jibi ne Anan Amina court estate Apo dutse Abuja Akwai wurin Mata
21/08/2025

Mutanan Abuja karku Bari a baku labari jibi ne Anan Amina court estate Apo dutse Abuja

Akwai wurin Mata

20/08/2025

Nasihar Prof. Mansur Sokoto, mni zuwa ga yan takara

Assalamu alaikum Mai bukatar neman scholarship a Saudia sun sake bude karo na biyu ga mai buƙata. Na tsawon kwana biyu n...
20/08/2025

Assalamu alaikum
Mai bukatar neman scholarship a Saudia sun sake bude karo na biyu ga mai buƙata.
Na tsawon kwana biyu ne kacal. Allah yasa mu dace

ادرس في السعودية - وزارة التعليم

GWANI BILAL HAMZA – NASARAR WAKILCI ✨🇸🇦🇳🇬Alhamdulillah!A bana mun samu gagarumin alfahari da ɗan’uwarmu, matashinmu Gwan...
20/08/2025

GWANI BILAL HAMZA – NASARAR WAKILCI ✨🇸🇦🇳🇬

Alhamdulillah!
A bana mun samu gagarumin alfahari da ɗan’uwarmu, matashinmu Gwani Bilal Hamza, wanda ya wakilci ƙasarmu a babban gasar Qur’ani ta duniya a Saudiyya, matakin Izu 60 tare da Tafsiri.

🕌 Tabbas, a zukatanmu ka riga ka zama zakara. Kaunarka da soyayyarka ta ginu cikinmu. Samun damar wakiltar ƙasa a irin wannan gasa babban daraja ne da ba kowa ke iya riskar sa a rayuwarsa.

📖 Ka gabatar da karatu cikin natsuwa, kwarewa, da salo na musamman da kowane mai sauraro zai tabbatar da cewa ka cancanci wannan alfahari. Ga sauti iya sauti, ga haddar Qur’ani iya hadda – lallai ka yi abin koyi.

🤲 Allah ya ƙara maka daraja da albarka.
Ka tuna: Ba lambar yabo kaɗai ce nasara ba – wakiltar ƙasa kanta babbar nasara ce da ba ta gushewa a tarihi.

💚 Muna alfahari da kai, Gwani Bilal Hamza! ♥️🇳🇬

Address

A4 B5 MIYANGO Close AMINA COURT ESTATE
Abuja
90000

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al qurra'u Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category