05/01/2024
Tsaro: An zargi 'Yan Banga da Karkatar da Shanun fulani a Mazoji, jahar Katsina.
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, @ Katsina Times
Yayin da gwamnatin Katsina ke kokarin bambance fulanin kirki da kuma miyagu domin samar da zaman lafiya ingantacce. Ayyukan wasu yan banga a yankin mazoji karamar hukumar Matazu na kokarin mayar da hannun agogo baya a yankin.
Wasu fulani da jaridun Katsina times ta samu labarin su sunyi zargin wasu yan banga sun kore masu shanu a rafi wajen shan ruwa sun karkatar da wasu.
Fulanin da s**a tabbatar da gaskiyar su, s**a nufi wajen jami an tsaro domin su bayyana kansu ayi bincike na gaskiya a basu shanun su.
Fulanin sun bayyana cewa bayan jami an tsaro sun tabbatar da cewa lallai shanun su na gaskiya ne, sai s**a ce suje cikin shanun da aka tara su dauki nasu.
Daya daga cikin fulanin ya fada mana cewa, shanun shi talatin da uku aka kora amma shanun sa guda Goma sha shidda kawai ya gani a wajen sojoji, kuma an zabe masu koshin da lafiya, ba an gansu ba a wajen sojoji.
Wanda ya shaida ma jaridun Katsina Times yace sojoji sun tabbatar masa iya shanun da aka kawo masu kenan.
Karamar hukumar Matazu na Ćaya daga cikin Ćananan Hukumomi da ke Fama da Matsalar rashin tsaro a jihar Katsina. Sai dai 'wasu fulani na Matazu sun koka akan yanda wasu 'Yan banga suke keta musu haddi ba tare da tabbatar da kuma banbance masu laifi da marasa laifi ba.
Koken da Katsina Times ta samu da wasu gungun fulani a Mazoji a Karamar hukumar ta Matazu, sun zargi, 'Yan Banga da Kore masu shanu babu gaira babu Dalili.
Kamar yanda wani da ya bukaci mu sakaya sunansa ya bayyana mana, cewa 'Yan Banga sun zo har inda yake kiwon shanunsa sun kore masa shanu guda talatin da uku 33, da Tunkiya 27, yace "abin ya faru da yamma, a washe gari na biyo sawu daga mazoji zuwa Matazu, sai na tarar da shanu 16 a maimakon 33, babu guda 17, na iske shanun a wajen sojoji, saboda da s**a kora su daga nan can wajen sojoji s**a isa dasu, kuma ba namu kadai s**a kore ba hadda na 'yan