Malumfashi Post

Malumfashi Post Malumfashi Post Sabon Shafin Jarida Ne Dake Kokarin Kawo Muku Sabbin Kayatattun Labaran Duniya Aciki

Da Dumi-Dumi : Hukumar zabe a jihar Katsina ta sanar da Dr. Dikko Umar Radda na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe ...
19/03/2023

Da Dumi-Dumi : Hukumar zabe a jihar Katsina ta sanar da Dr. Dikko Umar Radda na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da kuri'u 859,892. Ya doke na PDP Yakubu Lado da ya samu kuri'u 486,620

06/03/2023

YANZU-YANZU:
Hukumar INEC Babbar Munafuka Ce, Ba Zata Yi Zaɓen Gwamnoni Mai Inganci Ba, Cewar Atiku Abubakar

Yanzu-Yanzu- Sabuwar Transfoma ta wuta ta iso har cikin unguwar Mata Mlf  Transfomar wacce wacce al,umma unguwar Mata da...
06/03/2023

Yanzu-Yanzu- Sabuwar Transfoma ta wuta ta iso har cikin unguwar Mata Mlf Transfomar wacce wacce al,umma unguwar Mata da Unguwar Amare s**a dade suna kira da roƙon ganin an sama musu ce gomnatin APC ta sama musu yau.

Haka suma Unguwar Dawo dake a garin an samu kai musu tasu wacce suke nema

Burin shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi Mal: Maharazu Adamu Dayi ya cika Allah ya saka masa da Alkhairi.

Mai girma mataimakin gwamnan jihar yobe Hon Idi Barde Gubana a mazabarshi dake gubana karamar hukumar fune
25/02/2023

Mai girma mataimakin gwamnan jihar yobe Hon Idi Barde Gubana a mazabarshi dake gubana karamar hukumar fune

Sheíkh Muhammad Sani Yahaya Jingir  Jingir Shugaban Majalisar Malamai Na Kasa Da Kasa Na Kungiyar Jamaatu Izalatil Bid a...
25/02/2023

Sheíkh Muhammad Sani Yahaya Jingir Jingir Shugaban Majalisar Malamai Na Kasa Da Kasa Na Kungiyar Jamaatu Izalatil Bid ah Waikamatis Sunnah Ya Kada kuri'ar Shi Ga Bola Tinubu kamar yadda yayi kira ga Jama'ar Musulmaí.

Da Ɗumi-Ɗumi; Kai tsaye yadda shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari da iyalinsa a falonsa dake Daura suke kallon yadd...
25/02/2023

Da Ɗumi-Ɗumi; Kai tsaye yadda shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari da iyalinsa a falonsa dake Daura suke kallon yadda shugaban ƙasar gobe Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yake kaɗa ƙuri'arsa daga Falamo ta jihar Lagos.

Nasara ta Tinubu ce

24/02/2023

DA DUMI'DUMI ASIRIN ATIKU ABUBAKAR YA TONU!

Yadda Dan takarar Neman Shugaban Kasar Najeriya Atiku Abubakar da Gwamna Tambuwal da Gwamna Okowa Suke Shirya Yadda Za suyi Maguɗin Zaɓe Gobe.

Ku saurara a wannan sautin muryar za ku ji har yadda s**a shiryar yadda s**a hada kai da gwamnan babban bankin Najeriya don biyan buƙatar kan su....

Zamu Gurfanar Da Buhari A Kotun Duniya Kan Zargin Kisan Gilla Ga Yan Kungiyar Biyafara, Inji Atiku Abubakar Daga Comr Ha...
18/02/2023

Zamu Gurfanar Da Buhari A Kotun Duniya Kan Zargin Kisan Gilla Ga Yan Kungiyar Biyafara, Inji Atiku Abubakar

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Shugaban Kungiyar Hadin Kan Kudu maso Gabas na Atiku, Kenneth Uzumaki Austin ya bukaci yankin Kudu maso Gabas da su amince da Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP da wasu fitattun shugabannin yankin Arewa kuma amintattu s**a yi.

Ya ba da tabbacin cewa a ganawar sirri ne a wani taro da aka yi a gidan wani Janar na Soja Rtd kuma wanda ya taba ministan tsaro a Abuja, inda aka kammala wani bangare na yarjejeniyar kuma aka amince da shi.

A cewar Austin wanda ya yi magana a wajen wani taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Abakaliki, wani bangare na yarjejeniyoyin sun hada da cewa Atiku idan ya zama shugaban kasa, zcikin kwanaki 100 na farko a kan karagar mulki, zai tabbatar da sakin jagoran ‘yan awaren Biafra. , IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, za a sake shi ba tare da wani sharadi ba.

Wani tsohon shugaban majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Adolphus Wabara ya tabbatar da hakan a hukumance.Na biyu kuma shi ne Atiku ya yi alkawarin yin aiki don tabbatar da mafarkin shugabancin kabilar Ibo ta hanyar tabbatar da mika mulki ga shi. magajinshi na kabilar Igbo.

Ya yi nuni da irin alkawuran da Atiku Abubakar ya sha na cewa zai zama matattakalar shugabancin kabilar Ibo.” Daya daga cikin furucin Atiku ya fito ne a farkon makon nan a ranar Talata yayin taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar a Enugu. Wannan shi ne karo na uku da dan takarar PDP zai yi takara. yi wa ‘yan kabilar Igbo alkawari a yankin Kudu-maso-gabas.

Atiku ya fara wannan alkawari ne a watan Satumba a wani taron shiyyar PDP da aka gudanar a Enugu.Dan takarar na PDP ya kuma yi irin wannan alkawari a lokacin kaddamar da yakin neman zabensa na yankin Kudu maso Gabas a Awka, jihar Anambra, a watan Disamba. Da yake magana a lokacin gangamin Enugu a ranar Talata, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce har yanzu ya tsaya kan maganarsa.

Na uku, ya ce, shi ne matakin da Atiku ya dauka na bayar da cikakken hadin kai kan binciken da kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ke gudanarwa da kuma tabbatar da a gaggauta gurfanar da shugaba Buhari mai barin gado da manyan jami’an gwamnatinsa kamar babban lauyan gwamnatin tarayya, babban hafsan soji, da GOC 82 Div. na sojojin Najeriya, saboda kisan kare dangi da aka yi tare da aikin sojan Python Dance da aka gudanar a Kudu maso Gabas.

“Tuni kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) da ke birnin Hague na binciken farmakin da sojojin Najeriya s**a kai wa wata al’umma a watan Satumbar 2017 a jihar Abia a lokacin wani atisayen lambar soja mai suna Operation Python Dance 2 (Egwu Eke Abuo) wanda zai samu ne kawai. goyon baya da hadin kan gwamnati da Atiku ya yi alkawari.

“A cikin wasikar da aka samu mai lamba OTP-CR-413/17 mai kwanan wata 20 ga Maris, 2018, wanda jaridar Sun ta buga ita ce amsa ta biyu da kotu ta bayar ga wanda ya shigar da karar, an tabbatar da cewa harin da sojoji s**a yi da kuma kashe-kashen sun riga sun kasance a matakin farko. jarrabawar ofishin mai gabatar da kara.

"Sashe na wasikar da Mark Dillon, shugaban sashen bayanai da shaidu a ofishin mai gabatar da kara, ya sanya wa hannu, ya karanta: "A bisa ga haka, za a yi nazari kan sadarwar ku ta wannan mahallin, tare da taimakon sauran hanyoyin sadarwa da sauran bayanan da ake da su. "in ji Austin.

Domin ya kara tabbatar da wannan batu, Austin ya yi nuni da wani taro da kungiyar dattawan Arewa ta yi da shugabannin yankin kudu maso gabas inda shugaban NEF, Ango Abdullahi, ya gabatar da dukkan sharuddan da aka amince da su.

Abdullahi, a wata hira da jaridar Tribune ta ranar 12 ga Fabrairu, 2023, ya tabbatar da wannan taro da wadannan kalmomi: NEF na ci gaba da tattaunawa da sauran masu ruwa da tsaki daga sassan kasar nan masu sha’awar zaben.

Ko a yau (Alhamis) muna taro da wakilan kungiyar Ohanaeze a Abuja.” NEF da Ohanaeze suna ganawa a yanzu kuma ba mu san sakamakon tattaunawar da s**a yi ba tukuna,” Austin ya nakalto Abdullahi ya musanta ikirarin nasa.

A karshe ya bukaci ‘yan kabilar Igbo da kada su bari hasashe ko rashin jin dadi ya hana su fitowa kada kuri’a mai yawa don tabbatar da makomarsu bisa alkawuran da Atiku da shugabannin Arewa s**a dauka.

“Akalla Atiku da kansa ya jajirce wajen bayyana matsayinsa na goyon bayan Mazi Nnamdi Kanu, alhali ko dan uwanmu, Obi bai iya yin hakan a fili ba. “Ya kamata mu ‘yan kabilar Igbo su shiga cikin wannan yarjejeniya da Arewa da shugabanninta s**a kulla kuma s**a rufe ta ta hanyar yin amfani da wannan tagomashin fata ta hanyar kada kuri’a ga Atiku da kuma tabbatar da kirga kuri’unsu,” inji shi.

INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHIR RAJI'UNWannan bahun da kuke gani ba kaya bane mutane ne guda biyu da s**a rasu a ciki.Mummu...
04/12/2022

INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHIR RAJI'UN

Wannan bahun da kuke gani ba kaya bane mutane ne guda biyu da s**a rasu a ciki.

Mummunan hadarin Mota ne yayi sanadiyar rasuwarsu da wasu mata da kananan yara a kan hanyar babban titin garin Malam dake jihar Kano.

Karamar motar Taxi da babbar motar Tanki ce s**a yi taho mu gamu a wurin, hakika wannan hatsarin yayi matukar taba mun zuciya duk da bansan su ba😭😭

Muna musu Addu'ar Allah ya jikansu da Rahma, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani.

Comr Abba Sani Pantami

Yadda Shugaba Buhari Ya Sabunta Wa Jami'an Tsaron Mu Makaman Yakin Su.Ya Allah Ka Baiwa Jami'an Mu Nasara akan Yan Ta'ad...
18/11/2022

Yadda Shugaba Buhari Ya Sabunta Wa Jami'an Tsaron Mu Makaman Yakin Su.
Ya Allah Ka Baiwa Jami'an Mu Nasara akan Yan Ta'addan Kasar Nan.

Daga: Usman Rabi'u Kwankwaso

Nasha Wahala a darena na farko, Angon mata takwas reras a rana ɗaya.Daga Hajiya Mariya Azare.“Wani matashi dan kasan tha...
14/10/2022

Nasha Wahala a darena na farko,
Angon mata takwas reras a rana ɗaya.

Daga Hajiya Mariya Azare.

“Wani matashi dan kasan thailanda ya bayyana yadda yasha wahala a daren shi na farko inda ya auri mata 8 rana ɗaya reras.”

“Angon mai suna Ong Dam Sorot, dan ƙasan thailand mabiyin addinin hindu mai sana'an zanen tattoo, ya bayyana yadda daren shi na farko ya bashi wahala inda kowacce tace itace ta farko a gidan.

Ong yace da taimakon abokinsa aka shawo kan wadannan matan inda yabi kowace ɗaki a rana ɗaya yayi kwanciyar aure dasu.”

Yace a yanzu haka yana zaune da matansa lafiya cikin kwanciyan hankalali kuma sun ɗauki junan su 'yan uwan juna kuma abokan shawara.”

Yau Shugaban kasar Nigeria Muhammadu Buhari ya yadda ya furta dakansa cewa tabbas matsalar Tsaron da Nigeria ke fama da ...
15/08/2022

Yau Shugaban kasar Nigeria Muhammadu Buhari ya yadda ya furta dakansa cewa tabbas matsalar Tsaron da Nigeria ke fama da ta wuce gona da iri.

SUBHANALLAHI: Ina Mamakin Yadda Ƴan Najeriya Suke Godewa Allah Kaɗai Basa Haɗawa Da Shugaba Buhari Kan Nasarorin Gwamnat...
05/08/2022

SUBHANALLAHI: Ina Mamakin Yadda Ƴan Najeriya Suke Godewa Allah Kaɗai Basa Haɗawa Da Shugaba Buhari Kan Nasarorin Gwamnatinsa, Cewar Garba Shehu

Mai magana da yawun shugaban ƙasa Malam Garba Shehu ya caccaki ƴan Najeriya kan godewa Allah kaɗai ba tare da haɗawa da shugaba Buhari ba kan nasarar da gwamnatin shugaban ta samu kan yaƙar cutar Korona.

Shehu ya bayyana cewar, zuwan Korona yasa duniya ta zuba ido dan ganin yadda cutar zata wargaza Afirika musamman Najeriya, sai dai haka bai faru ba.

"Zuwan cutar Korona ya kawowa gwamnatin shugaba Buhari babban cikas, amma ƴan Najeriya idan s**a tashi sai s**e sun gode Allah su yi shiru, tabbas komene ya faru dole a godewa Allah saboda idan ba tare da ikonsa ba babu abinda zai faru."

"Amma kuma Allah na amfani da sanadi wajen tabbatuwa da faruwar abubuwa." Inji Garba Shehu

Siyasa Bada Gaba Ba: Wakilan Dan Takarar Kujerar Majalisar Wakilai Mai Neman Wakiltar Kananan Hukumomin Funtua Da Dandum...
16/07/2022

Siyasa Bada Gaba Ba: Wakilan Dan Takarar Kujerar Majalisar Wakilai Mai Neman Wakiltar Kananan Hukumomin Funtua Da Dandume Karkashin Inuwar Jam'iyyar Apc Hon. Abubakar Ahmad Muhammad (Gardi) Sun Wakilcheshi Domin Ta'aziyya Ga Abokin Karawarsa, Hon. Abubakar Salisu Asas Na Jam'iyyar PDP

Daga: Shamsu Wapa Dandume

Ranar Asabar 16-07-2022 Wakilan Dan Takarar Kujerar Majalisar Wakilai Mai Neman Wakiltar Kananan Hukumomin Funtua Da Dandume Jihar Katsina Karkashin Inuwar Jam'iyyar Apc, Hon. Barista Abubakar Ahmad Mohammad (Gardi)

Sun Wakilche Shi Domin Yima Abokin Karawarsa Na Jam'iyyar PDP, Hon. Abubakar Salisu (Asas) Ta'aziyya, Bisaga Rasuwar Mahaifinshi A Gidansa Dake Birinin Zaria, Wanda Allah Yayi Ma Rasuwa Satin da Ya Gabata, Tareda Jajanta Ma Shi, Da Addu'ar Neman Allah Ubangiji Ya Jikanshi da Rahama, Yasa Aljannace Makomarshi Ameen

Shugaban Kwamitin Tuntuba Na Hon. Barrista Abubakar Ahmed Muhammad, Malam Bala Anwarudeen Shine Ya Jagoranchi Tawagar, Wanda Yasamu Rakiyar, Samaila Nababa, Da Shamsudden Adam (Ofisa), da Malam Ibrahim Sani Bawa, Da Mai Kulada Bangaren Kafar Sadarwar Zamani ( Social Media) Hamza Lawal

Macen Da Ta Fara Tuka Mota A Najeriya, Funmilayo Ransome-Kuti, Mahaifiyar Fela Kuti
16/07/2022

Macen Da Ta Fara Tuka Mota A Najeriya, Funmilayo Ransome-Kuti, Mahaifiyar Fela Kuti

ZABEN OSUN: Wankin Hula Na Neman Kai Jam'iyyar APC Dare, Yayin Da Jam'iyyar Adawa Ta PDP Ke Ci-gaba Da Jiƙa Mata Wanki.
16/07/2022

ZABEN OSUN: Wankin Hula Na Neman Kai Jam'iyyar APC Dare, Yayin Da Jam'iyyar Adawa Ta PDP Ke Ci-gaba Da Jiƙa Mata Wanki.

DA ƊUMI-ƊUMINSA: An Yi Wa Mataimakin Shugaban Ƙasa TiyataAn yi wa mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo tiy...
16/07/2022

DA ƊUMI-ƊUMINSA: An Yi Wa Mataimakin Shugaban Ƙasa Tiyata

An yi wa mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo tiyata a kafarsa a yau, bayan kwantar da shi a asibiti

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar Laole Akande ne ya bayyana haka a shafinsa na Tuwita, kamar yadda BBC ta rawaito.

Sanarwa ta ci gaba da cewa mataimakin shugaban kasar ya ji raunin ne yayin wasan sukwas (squash).

Nan gaba kadan ne a yau likitocinsa za su yi bayanin halin da yake ciki.

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Malumfashi Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share