06/08/2023
Kafin Ka Goyi Bayan Ya*kar Kasar 🇳🇪 Nijar, Ya Kamata Ka San Wannan;
Wanda ya rubuta,
Abu Albani Auwal Ahmad
Don Allah, a daure a karanta wannan rubutun, yana da matukar muhimmanci a wannan lokacin.
1. Na farko dai, yawanci mutane ba su san Nijar na da arziki ba, saboda wadanda s**a mallaki Nijar (🇫🇷Fra*nce) ba su barsu sun mori arzikin kasarsu yadda su uwayen gidan nasu ke mora ba.
2. Watakila ka yi mamaki idan na ce maka Nijar itace kasa ta 6 a duniya, ba fa a Afirka ba, a'a, a duniya, wajen arzikin sinadarin Uranium.
3. Da Nijar, da Namibia da South Africa, kasashe 3 a Afirka, su suke fitar da Uranium kashi 18% cikin 100 da ake amfani da shi a duniya.
4. Kashi 50% cikin 100 na Uranium din Nijar, fitar da shi ake yi zuwa kasar Far*ansa.
5. Kusan kashi 24% cikin 100 na Yuraniyom din da kasashen turai (EU) ke amfani da shi daga Nijar ya ke fitowa.
6. A kasar Far*ansa, kusan ko wane 💡 koyin lantarki 1 cikin guda 3, yana bada wuta ne daga Yuraniyom din Nijar da aka sarrafa ya ke bayar da wuta wa kasar, alhali kusan kashi 80 cikin 100 na 'yan kasar Nijar kuma ba su da wuta.
7. Mafi yawan 'yan Nijar Mus*ulmai ne kuma Hau*sawa yan'uwanmu (mu 'yan arewa), domin mun fi k**a da su a komai sama da k**ar da mu ke da ita da 'yan ku*du da muke rayuwa a matsayin 'yan kasa daya.
8. Idan aka shiga Nijar da ya*ki, karshe Arewa za su gudo, kuma kowa ya san yadda 'yan arewa musamman Hausawa Musulmai ke da karbar baki da sakewa da su musamman bakon da ya ke Mus*ulmi kuma ya ke jin Hausa. Me ka ke tsammani idan s**a zo ba bu sana'a, ba bu jari, ba bu muhalli, muka sake karuwa sama da karuwar da muke da ita yanzu, s**a zo s**a hade da namu matasan da su ma ba su da sana'a, mai ka ke tsammanin hakan zai haifar? Karin talauci, karin rashin tsaro, karin rashin zaman lafiya irin wadanda duk su ne yanzu mu ke fama da su.
9. Sannan wa yace maka yakin iya kan sojojin da s**a yi juyin mulkin zai tsaya? Sannan idan aka ka*she Musu*lmai kuma Hau*sawa yan'uwanmu wa ke da asara? Wa