04/07/2025
Na tabayin MUNAFURCI asiri na ya tonu... Daman bantaba yiba sai awannan lokacin na fara ashe ba riba... 🤔 "ina dawowa daga islamiyya aka aike ni tasha siyan kayan miyar taushe, aka lissafi mini komai, kabewa, kayan miya, alayyahu, gyadar miya irinta kuli, aka bani kudaden na tafi.. 🚶♂️🚶♂️
Da naje saina rarrage kudin komai tunda ai alokacin kayan miya araha yake, nabi kowanne na rage naira 10, 10, 👌
Bayan an bani chanjin na zagaya wajen masu kayan wasa na siya 'dan DOKI, naje wajen masu LAKA da GIREBA na siya 😋
Na kashe kudin duka anan, na tafi gida..
Ina zuwa na tarar babanmu ya kawo kayan miya kwando ukku, ashe Dama jinkirin dawowa yayi shiyasa aka bani inje in siyo 🤔
Ina shiga gida yace "Kashhh! Ina ka siyo kayan nan? Nace" tasha naje" sai yace "toga kudin mashin ka mayar ka amso kabewa kadai"
Naji cikina yace " 'kuuuuu😳🙆♂️... Nace" baba bazasu amsa ba" sai yace "OK bari yanzu in daukeka a mota sai mu koma Dan kada magriba yayi"
' kirjina ya fara duka ukku ukku🙆♂️... Da aka gama safke kayan miyan cikin kwando, sai naji ya cewa mama "nawa ne kika bashi" sai mama tace "1500 ce"
Sai yace "to muje idan aka mayar sai a amsa gyada da kabewa kadai saimu dawo" 😳
Yace "muje koh"
Na bishi simi simi kamar kazar da kwai ya fashewa aciki... 😳
Gashi nan babanmu ba wasa wallahi, idan ya gano nayi munafurci wallahi saina daku kamar kalangu.. 🙆♂️
Ya Bude mota ya shiga, nima na Bude zan shiga kofar baya... Yace "a'a ina zaka shiga haka, dawo ka shiga na gaba"
Na dawo.. Ya Bude mini daga ciki.. Na shiga na zamna na rufous kofa da kyar "😳😥
Na rugume kayan miya aka tafi... 🤣🤣
🚶