31/12/2025
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya sanar da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Obi ya bayyana hakan ne yayin wani taro da magoya bayansa a birnin Enugu, inda ya ce sabon matakin na daga cikin dabarun da za su ƙarfafa fafutukar samar da sahihin zaɓe a ƙasar.
A cewarsa, shi da magoya bayansa za su yi duk mai yiwuwa wajen hana maguɗi da murɗiyar zaɓe a babban zaɓen shekarar 2027, tare da jaddada aniyarsu ta kare ƙuri’ar jama’a.
Sauya sheƙar ta Peter Obi na zuwa ne a daidai lokacin da siyasar ƙasar ke ƙara ɗaukar zafi, yayin da jam’iyyu ke fara shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.