25/08/2026
Eid-el-Maulud: CAN ta bukaci ’yan Najeriya da su yi koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammadu
Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta bukaci ’yan Najeriya su mayar da darussan rahama, da adalci da tausayi da Annabi Muhammadu ya koyar zuwa ayyukan da za su taimaka wajen magance matsalar rashin tsaro, da tsadar rayuwa da ƙarfafa haɗin kan Ƙasa.
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh, ya sanya wa hannu a ranar Talata a Abuja, domin taya al’ummar Musulmi murnar bikin Eid-el-Maulud.
Mista Okoh ya taya al’ummar Musulmi a fadin Najeriya murnar bikin, tare da yi musu addu’ar samun zaman lafiya da albarka ga iyalansu da al’ummominsu.
Ya ce bikin Eid-el-Maulud, wanda ake gudanarwa domin tunawa da haihuwar Annabi Muhammadu, wata dama ce ta yin tunani kan darussan rahama, adalci, tausayi ga talakawa da masu rauni, gaskiya da zaman lafiya tsakanin al’umma.
Ya ce wadannan dabi’u suna da muhimmanci musamman a wannan lokaci, domin suna tunatar da mutane muhimmancin kula da juna, kare mutuncin dan Adam da kuma neman zaman lafiya, ko da kuwa ana amfani da bambance-bambancen da ke tsakanin mutane wajen cimma muradun siyasa ko na kashin kai.
Archbishop Okoh ya ce bikin ya zo ne a lokacin da 'yan Najeriya da dama ke fuskantar mawuyacin hali, sakamakon karuwar tsadar rayuwa da matsalar rashin tsaro da ke shafar gidaje da al’ummomi a sassan kasar.
“Mutane sun gaji da alkawura; abin da suke so shi ne su ga rayuwarsu ta inganta,” in ji shi.
Saboda haka, ya bukaci gwamnatin tarayya da shugabanni a dukkan matakai da su daina dogaro da alkawura kawai, su koma ga daukar matakan da za a iya gani a fili.
Ya ce ’yan Najeriya na bukatar ingantaccen tsaro, saukaka matsin tattalin arziki da kuma shugabanci da zai sanya jin dadin al’umma a matsayin babban abin da yake fifita.