23/04/2022
BAKU DA HUJJAR ALAKAN TA FULANI DA KALMAR TA ADDAN CI,
kalmar Fulani Kalma ce dake wakiltar Miliyoyin Alumma a sassa daban daban na duniya, Wannan jinsin na Fulani Na wakiltar Bayin Allah Daban daban, Shahidai,Malamai,Shugabanni da sauran Bayin Allah A duk kan sassan Duniya,
Haba Dan uwa wace hujja gareka daza ka Jingina Wa wainnan bayin Allah wannan Mummunar kalma(Ta addanci) Don meyasa Zaka tozarta Bayin Allah da s**a gabata kuma katozarta wainda Zasu Zo,
shin kasan kuwa irin Zafi da Radadin da duk wani jinsin fulani keji a duk lokacinda aka jingina Shi da wannan bakar kalmar'
Kayi tunani dan uwa Ya zakaji a duk lokacinda wani ya jingina Alummar ka ko addinin ka da wannan sunan'
Mecece hujjar ku najingina Alummar Fulani da Ta addanci'
Ta addanci Aikine wanda a kowace kabila ko Addini Akwai Gurbattun ciki da Suke Aikata shi, A duk inda Za asamu nagari to tabbas Za a samu na banza,
Kar kabilanci ko Kiyayya ta Kai ku ga halaka,
Alummar Fulani su s**afi kowace kabila Fuskantar Matsaloli akasar nan ,, karku Zama masu sankai da rashin Adalci , ku kira Yan tadda da sunan su,
Kubar mu ji da matsalolin da s**a da baibaye mu, Kubar mu mu ceto Alummar mu , Kubar mu mu ceto Addinin mu Da wanzuwar kasar Mai Albarka, karku bi wannan hanyar don yimana zagon kasa,
©IBN IBRAHIM