25/09/2025
GAME DA KARATUN MALAM LAWAN
Na saurari cikakken bayanin Mal. Lawan Triumph yau a shafin yanar gizo na gidan rediyon Premier (Mal. Anas ne ya yi sharing). Zancen gaskiya, babu wata s**a ga Annabi ﷺ ciki. Na lura babban dalilin da ya sa WASU mutane s**a yi masa wancan fahimtar shind inda aka fara saka karatun, da yadda taken da aka masa da yadda aka haɗa videon don a cimma abunda ake so na jingina masa cin mutuncin manzon Allah. Shekaran jiya bayan na ga wani bawan Allah (ban san wace ɗarika zan saka shi ba, amma dai ba ɗan Izala bane) ya yi magana yana neman a k**a Mal. Lawan, sai na tambaye shi dalili. Sai ya ce ga abunda ya ce. Na ce ina son in ji da kunne na. Jiya dai ya yi mentioning dina a shafin wani zindiƙi (Bege TV), nan na fara ganin videon, kuma da alama shi ya fara wasa da hankulan mutane.
A takaice, sakonsa shine:
"Manzon Allah yana da mu'jizozi ingantattu da ba ya bukatar waɗanda s**a samo asali daga tatsuniyoyi, wanda wasu cikin tatsuniyoyin ma ba za'a lissafa su a layin karama ba saboda abubuwa da ake zamu ga wadanda ba shi ba, har wasu dabbobi ma ana sami irin haka gare su."
Abunda na lura da su ga masu adawa da mabiya Sunnah su ne k**ar haka:
1. Suna kokarin kare tatsuniyoyi da s**a gada daga iyaye da kakanni ne ta hanyar yiwa duk wanda ya soke su sharri. Sun taɓa yin haka lokacin da s**a dinga yaɗa videon wani malami da ya ce cikin Ash-shifaa akwai hadisai ƙarya da labarai mara tushe. To, da yawansu, da irin labaran nan suke cikin abinci.
2. Akwai masu kokarin yiwa duk wani malamin Sunnah da ya shahara da karantar da Tauhidi sharri saboda abunda ya faru da malaminsu. Su ne ƴan kogo. Su wadannan (da kaso mai yawa cikin sauran ƴan ɗarika) sun fi son Masuss**a kan malaman Sunnah. Ba don komai bai sai saboda shi Annabi ﷺ yake rusawa, su kuma shehunnai suke rusawa. Su kuma waɗannan ƴan bidi'a sun fi jin haushin mai rusa shehu kan mai tozarta Annabi ﷺ da sahabbansa. Su ne fa malaminsu ya ce Annabi hankaka ne, amma muka ji su shuru. Ya ce duwatsu kasusuwan Annabi ne. Amma s**a yi shuru, tare da cewa dawatsun nan ne dai muke takawa, ake gini da su, har tsarki ana yi dasu. Amma shuru kake ji, a haka kuma su ke cewa idan an taɓa Annabi ﷺ, hankalinsu gushewa yake!
Don haka, a cikin bayanan Mal. Lawan gaba ɗaya, a wuri guda zan ce ya k**ata ya gyara lafazi nan gaba. Shine kuma inda yake lissafa sauran Annabawa. Kuma Alhamdulillahi, ba wannan ne mahallin sharri da rikicinsu da shi ba, saboda sun san idan s**a dauko wannan ba zai yi tasiri wajen ɓata wa malamin suna da tunzura masa mutane ba.
Da wannan kuma nike faɗar cewa, idan ana yayata magana kan wani mutum, to ya k**ata idan ka tashi bincike, kar ka yi gaggawa, kuma kar ka dogara da abunda mai adawa da shi yake yaɗawa, ka koma asalin zancen. Kuma ka yi kowa haka, ba iya malamin ƙungiyarka ko ɗarikar ba. Na tuna lokacin da aka dinga yaɗa cewa wani malamin Faira ya ce ya kai matsayin da yake jin sautin alƙalamin ƙudra. Ashe a complete din yana magana ne kan manzon Allah. Amma an ga yadda ƴan media s**a yi wasa da hankulan mutane, kuma har yau an cigaba da yaɗa wancan guntun videon.
Daga karshe, dole a cigaba da rusa ƙarya, amma a dinga taka-tsantsan, kar a bari ƴan bidi'a da masharranta su samu abun riƙo. Duk abunda zai iya jawo cece-kuce kuma saƙo zai iya kaiwa inda ake so ko ba'a kawo shi cikin bayani ba, to barinsa shi ya fi dacewa. Saboda manufa itace a shiryar da mutane, kuma an fi samun haka galiban idan an rufe wa ɗan bidi'a baki ya rasa abun faɗa sai zagi. Amma matukar ka bari ya samu wani ɗan abu ya yi riƙo da shi, to lallai zai ruɗar da wasu mutane, kuma sai an sha wahala kafin a iya fahimtar da su gaskiya. Idan ma basu tada rigima ba kenan.
Daga Dr Ibrahim Usman