
02/08/2025
A yayin da fafatawar siyasa ke ƙara zafi gabanin babban zaɓen 2027, ɗaya daga cikin fitattun matasan ‘yan siyasa a jihar Bauchi, Malam Nasiru Cigari, ya bayyana cewa tsaida Honarabul Farouk Mustapha a matsayin ɗan takarar gwamna karkashin jam’iyyar PDP zai zama babban tubali ga nasarar jam’iyyar a matakin jiha.
Nasiru Cigari, wanda ya fito fili yana nuna goyon bayansa ga Kwamishinan Ayyuka na Musamman da Raya Karkara, ya ce Farouk Mustapha ya gina kyakkyawar dangantaka da jama’a, yana da sanayya da goyon baya a sassa daban-daban na jihar, tare da kwarewa da sanin makamar shugabanci.
Ya ƙara da cewa Hon. Farouk mutum ne mai mutunta kowa da kowa, wanda ba ya nuna bambanci ko fifita wani yanki bisa wani, kuma hakan ne ya sanya ya samu karɓuwa da girmamawa a tsakanin yawancin al’ummar jihar Bauchi.
Cigari ya ce al’ummar Bauchi na bukatar sabon salo na shugabanci wanda zai mayar da hankali kan haɗin kai, ci gaba da wakilci nagari. A cewarsa, Hon. Farouk ya nuna kwarewa da sadaukarwa a matsayinsa na kwamishina, kuma hakan ne ya ƙara tabbatar da cancantarsa a matsayin wanda zai iya jagorantar jihar cikin gaskiya da adalci.
A ƙarshe, Malam Nasiru Cigari ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar PDP a matakai daban-daban da su dauki matakin da zai tabbatar da nasarar jam’iyyar, ta hanyar tsaida ɗan takarar da ke da tarin kwarewa da kuma goyon bayan jama’a – wanda a cewarsa, babu wanda ya fi Hon. Farouk Mustapha wannan cancanta a halin yanzu.