03/10/2025
SALATUL FATIHI BA TA FI QUR'ANI BA A WAJEN 'YAN 'DARIQAR TIJJANIYYA
Falalar da ake fada ta Salatul Fatihi, ita ma tana cikin abinda yake sanya wasu hassada da kiyayyar wannan Salati. Falalar kuwa ita ce kamar haka:
A) Wanda ya karanta ta qafa daya, yana da ladan wanda ya yi wa Annabi Salati Dubu Shida (6,000).
B) Wanda ya karanta ta sau daya, yana da ladan wanda ya karanta Qur'ani sau 6, ga wanda ba ya tsayawa ga Umurnin Qur'ani.
C) Qafa 'daya nata ya yi daidai da tasbihin halittu.
D) Shehu Tijjani (R.A) ya ce, "Wanda Ya karanta ta sau daya, Allah Zai haramta jikinsa ga Wuta".
E) Shehu Tijjani (R.A) ya ce, "Wanda ya karanta ta sau daya, zai shiga Aljanna".
اللهم صل على سيدنا محمد الفاتح لما أغلق والخاتم لما سبق ناصر الحق بالحق والهادي إلى صراطك المستقيم وعلى آله حق قدره ومقداره العظيم
Mun sha jin wasu suna cewa, "Wannan Salati ya yi kyau da kuma tsari, amma falalarsa ce ba mu yarda da ita ba!"
Abin lura shi ne, akwai Izini na Musamman wanda sai da shi ne ake samun wannan falala da aka ambata, Allah kuma Mai ninka falala ne ga abinda Ya so! Allah Madaukaki Yana cewa:
مثل الذين ينفقون أموالهم في سبيل الله كمثل حبة أنبتت سبع سنابل في كل سنبلة مائة حبة والله يضاعف لمن يشآء والله واسع عليم
"MISALIN WADANDA SUKE CIYAR DA DUKIYOYINSU SABODA ALLAH, KAMAR MISALIN KWAYAR HATSI CE GUDA DAYA (DA AKA SHUKA) TA FITAR DA ZANGANNIYA BAKWAI, A CIKIN KOWACCE ZANGANNIYA AKWAI 'KWAYA 'DARI! KUMA ALLAH YANA NINNINKAWA GA WANDA YA SO, KUMA ALLAH MAYALWACI NE, MASANI!" (Suratul Baqarah: 261)
Annabi (SAW) Yana cewa:
إن الحسنات بعشر أمثالها إلى سبع مائة ضعف إلى أضعاف كثيرة
"KYAWAWAN AIKI, 'DAYA ALLAH YANA BADA GOMA MISALINTA, IZUWA NINKI 'DARI BAKWAI, ZUWA NINKIN-BA-NINKIN (DA YAWA)"
Kuma Annabi (SAW) Yana cewa:
إن لله عبادا ليسوا بأنبياء ولا شهداء، يغبطهم الأنبياء والشهداء لمكانهم من الله عز وجل
"ALLAH YANA DA WASU BAYI, SU BA ANNABAWA BA, KUMA BA SHAHIDAI BA, AMMA ANNABAWA DA SHAHIDAI SUNA BURIN INA MA SU NE SU, DON DARAJARSU A WAJEN ALLAH MADAUKAKI!"
Ka ga wadannan mutane da ba a fade su ba, ba su fi Annabawa da Shahidai ba, daraja ce kawai da Allah Ya ba su. Wannan shi ne abinda ake kira "Maziyya" da "Afdhaliyya". Watau kamar ruwa da turare, za ka iya sayen gwangwani ko kwalbar turare naira dubu, amma da wuya ka iya sayen gwangwanin ruwa a haka! Amma idan aka ce a yi alwala ba za ka yi da turare ba, da ruwa za ka yi. Ka ga ashe turaren bai fi ruwa daraja ba, watau Maziyya ba ta fi Afdhaliyya ba. Don haka Salatul Fatihi ba ta fi Qur'ani ba, falala ce da Allah Yake bayarwa ga abinda Ya so da wanda Ya so.
Shehu Tijjani (R.A) da muridansa gaba daya ba su da abinda ya fi Qur'ani, Salatul Fatihi kuma ba ta fi Qur'ani a wajensu ba. In dã ta fi shi, dã sai mu daina karatun Fatiha da Sura a cikin Sallah mu rinka karanta ta. Wannan kawai mummunar fahimta ce da aka yi wa 'yan Tijjaniyya.
Shehu Tijjani (R.A) ya haddace Qur'ani kyakkyawar haddacewa tun yana da shekara Bakwai da haihuwa, 'ya'yansa ma sun haddace, haka ma almajiransa. Shehu Ibrahim Inyass (R.A) shi da 'ya'yansa sama da Arba'in babu wanda bai haddace Qur'ani ba. Sannan a yau babu wata Dariqa ko Kungiya ta Musulunci da take da yawan mahaddatan Qur'ani sama da Tijjaniyya. Haba 'dan uwana! Dã 'yan Tijjaniyya suna da abinda ya fi Qur'ani ai dã Allah bai wanzar da haske da budi haka a cikinta ba. Falala ce kawai da Allah Yake bai wa abinda Ya so. Allah Madaukaki Yana cewa:
ذالك فضل الله يؤتيه من يشآء والله ذو الفضل العظيم
"WANNAN FALALAR ALLAH CE, YANA BADA ITA GA WANDA YA SO, KUMA UBANGIJI MAI FALALA NE MAI GIRMA!" (Suratul Jumu'ah: 4)
Malam Muhammadu Kani Gusau, Almajirin Marigayi Shehu Mai Hula, a cikin wani yabo da ya yi wa Shehu Tijjani (R.A) yana cewa:
Kash Munkiri nã Qarya..Kan Shehu Tijjani!
Cewa Salatul Fatihi.....Wai tã wuce Qur'ani
Qaryarku ce kuka shirya.....Ya munkiran Tijjani!
Don Shehu ya wuce wasa.....A cikin sanin Qur'ani
Wallahi duk ya fi ku.....Sirrin sanin Qur'ani!
Kuma sai ku nemi dalili.....A Hadisi ko Qur'ani
Uhhmm! Allah Ka bar mu a tafarkin su Shehu Ahmad Tijjani da Khalifansa Shehu Ibrahim Inyass da Almajiransu.