Ɗan Talla

Ɗan Talla Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ɗan Talla, Abuja.
(2)

ƊAN TALLA Nigeria LTD Company: Shafine dake bawa manya da ƙananun ƴan kasuwa da kamfanunuwa damar tallata hajarsu ga kwastomominsu dake fadin Duniya lungu da sako a online, ta hanyar bamu Tallace -Tallacenku.
09024075618

24/07/2025

Muna Neman Wanda zai siyi wnn page din.
🙋

21/05/2025

Ka da ka tsaya jiran samun sa'a, ka fita ka neme ta!
🙅

Ka nemi kudi, domin su na daga cikin manyan abubuwan da ke saukaka rayuwa da kawo nutsuwa a duniya. Amma kada ka bari so...
15/05/2025

Ka nemi kudi, domin su na daga cikin manyan abubuwan da ke saukaka rayuwa da kawo nutsuwa a duniya. Amma kada ka bari son kudi ya kaika ga sabawa Ubangiji. Ka nemi halal, ka nisanci haram, domin albarka tana cikin abin da aka samo da gaskiya da amana.

Ya Allah, Ka azurta mu da halal mai albarka, Ka bamu isasshen arziki a duniya, Ka kuma azurtar da mu a lahira.

ƊanTalla

13/05/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Khamis Gwani Kibiya, Sageer Ayuba, Abdullahi Dahiru, Ahmad Shehu

Babu laifi...! Don ka iya abu, ko kanada wani talent na abu, ko kai expert ne a wani abu, indai ba abun banza bane, kafi...
12/05/2025

Babu laifi...!

Don ka iya abu, ko kanada wani talent na abu, ko kai expert ne a wani abu, indai ba abun banza bane, kafi to kace ka iya abun.

Kar kaji kome, ba alfahari bane, you are only stating the FACT kawai, idan ka iya abu, ka fito kace ka iya abu, kuma ka nuna wa mutane cewa ka iya, don su san ka iya din.

Akwai da yawa da suke da kwarewa da skills akan abubuwa da yawa, amma saboda rashin fadawa na kusa garesu ma, sai a tsallakesu a tafi wani wuri daban.

Idan 'yan gidan ku ma ba su san potentials naka ba, taya zakayi tunanin na waje su san kana da wani potential, don haka it is very important ka fito fili ka fadawa kowa abun da ka iya kuma ka nunawa mutane.

Idan har baka fadi abunda ka iya ba, babu yadda za'a yi mutane su san kanada wani abu a tare dakai, don haka, feel free, ka fadi abunda ka iya, expertise naka, da skills naka, kuma ka nunawa duniya shi, don asan ka, asan abunda kasani.

ƊanTalla
Aliyu Dahiru Aliyu

Neman Arziki...!Idan ka tashi nema, to ka zage dantse sosai, ka ɗaura himma da nufin yin nasara 100%, kada ka nemi ko 99...
12/05/2025

Neman Arziki...!

Idan ka tashi nema, to ka zage dantse sosai, ka ɗaura himma da nufin yin nasara 100%, kada ka nemi ko 99.9%, ka ɗauki azamar samu duka, a zahiri ka riƙa bayyana cewa ƙarfi da dabaru da himmarka su ne za su ba ka nasara, amma a cikin ranka ka riƙa jin Allah kaɗai mai bayarwa da hanawa, ka alaƙanta zuciya gare Shi. Duk da cewa mutum ba ya samun duka abin da yake so a rayuwa, amma dai kada ka riƙa tunanin faɗuwa ko asara a lokacin da kake tsaka da gwagwarmaya. Abin da ka samu na nasara sai ka gode Allah, wanda ba ka samu ba, ka yi haƙuri, ka ci gaba da fafatawa. Idan kana son samun duka abin da kake so, sai dai ka yi ayyukan da Allah Yake so, ka samu Aljanna, a nan ne kaɗai za ka samu duk abin da kake so.

ƊanTalla
Aliyu Dahiru Aliyu

12/05/2025

Sana'ar da kuke rainawa wani da ita yayi arziƙi.
ƊanTalla✍️

Albarkacin Kasuwa...!In dai kana da tsayayyar sana'ar da kake iya riƙe kanka, to in sha Allahu za ka iya riƙe aure.ƊanTa...
12/05/2025

Albarkacin Kasuwa...!

In dai kana da tsayayyar sana'ar da kake iya riƙe kanka, to in sha Allahu za ka iya riƙe aure.

ƊanTalla
Aliyu Dahiru Aliyu

Ku gwada....!Ka ɗauki wani yaro mai kwazo, yana karanta littattafai kullum ko da shafi biyu ne, yana koyo, yana amfani d...
12/05/2025

Ku gwada....!

Ka ɗauki wani yaro mai kwazo, yana karanta littattafai kullum ko da shafi biyu ne, yana koyo, yana amfani da lokacinsa yadda ya kamata. Bayan shekaru, sai ka gan shi ya zama wani babban mutum. Shi ma dai ka ɗauki wani wanda kullum yana sheƙa shayi da kosai da safe, sai ya kwanta har zuwa la’asar, daga nan ya ɗauki waya yana whatsapp har dare. Bayan shekaru, za ka same shi ya zama cikakken Mara Makoma tantirin talaka faƙiri, kuma da wancan na farkon Mai hazaƙa da mayar da hankali da wannan Sarkin chatting da ziyartar ƴan mata dukkansu ba rana ɗaya s**a zama abinda s**a zama ba , ƴan ƙananun abubuwan da suke yi Kullum sune s**a mayar da su haka, don haka ka lura sosai Babana da ƙananun ayyukan da kake yi kullum wallahi su ne za su gina ka ko su rusa ka.

ƊanTalla
Aliyu Dahiru Aliyu

Soyayyar Zamani Ko Kashe Kai ?Duba misalin saurayi mai budurwa. Yana kashe N1000 a kullum wajen kira da chatting, da Kud...
12/05/2025

Soyayyar Zamani Ko Kashe Kai ?

Duba misalin saurayi mai budurwa. Yana kashe N1000 a kullum wajen kira da chatting, da Kudin Mota wajen kai mata ziyara (Zance) sai ya yi wata shida yana tafiya zance—kai! Shi da kansa bai lura ba, amma idan ka tara hakan, N180,000 dubu ɗari da Tamanin sun tafi a wata shida kawai. Shin me wannan kuɗi da ya kashe s**a amfana masa? Meyasa bai ƙara kuɗin a karin kasuwanci sa ba ? Wata shida kawai 180k shekara kuma fa ya kai 360k Bai Mori Komai ba ,A'a! Na tuna ya Mora tunda tace Masa , "I love you too, baby."

Wai kuma ita budurwar me ta rasa tunda shi ya rasa 360k a shekara kuma ya rasa loƙacinsa ? To ita kuwa babu abinda ta rasa. Bayan shekara biyu, sai ka ga yarinyar nan ta ce masa, "Wallahi ba kai bane mutumin da rayuwata ke buƙata" Kaga kuwa An samu asara biyu: Kuɗi sun tafi, zuciya ta karye, kuma time wasted!

ƊanTalla
Aliyu Dahiru Aliyu

Halayyarka.Kada ka ɗauki ƙananan halaye da wasa, domin ba su da ƙarancin illa kamar yadda kake tunani. A kullum, idan ka...
12/05/2025

Halayyarka.

Kada ka ɗauki ƙananan halaye da wasa, domin ba su da ƙarancin illa kamar yadda kake tunani. A kullum, idan kana ƙara 1% Percent na Abu mara kyau a rayuwarka, bayan shekara goma, za ka samu 100% na matsaloli sun dabaibaye rayuwarka kamar yadda ake yiwa ragon Layya dabaibayi kada ya tsere. Haka nan, idan kana ƙara 1% na ci gaba kullum, bayan shekaru goma, za ka zama wani babban mutum kuma abun kwatance.

ƊanTalla

12/05/2025

Sauya ƙaramar halayyarka yau, sai ka ga yadda rayuwarka zata canza gobe.
ƊanTalla✍️

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ɗan Talla posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Ɗan Talla:

Share